Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙananan yara suna mutuwa saboda yunwa a Sudan
Wata ƙungiyar bayar da agaji ta duniya ta yi gargaɗin cewa munin yunwar da za a shiga a Sudan ya zarce yadda aka yi hasashe a baya.
Ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ta ce ta duba lafiyar dubban ƙananan yara da mata a sansanin ƴan gudun hijira da ke Arewacin Dafur, kuma ta gano cewa ɗaya cikin uku na jimillar su na fama da tsananin yunwa.
A cikin shekara ɗaya, yaƙi tsakanin sojin Sudan da ƴan tayar da ƙayar baya ya tsananta buƙatar ayyukan jin ƙai a sassan ƙasar, musamman a yankin Dafur.
Ƙungiyar ta ce aƙalla ƙaramin yaro ɗaya ke mutuwa cikin kowacce sa’a biyu a sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam.
Ta ce ta kammala wani aikin gwaji ga iyaye mata da ƴaƴan su ƴan ƙasa da shekara biyar, kuma sakamako ya nuna cewa kashi ɗaya cikin uku suna fama da ƙarancin abinci mai gina jiki da kuma tsananin yunwa.
Wannan na nuni da mawuyacin halin da ake ciki, duk da cewa an gudanar da gwajin ne a sansanin ƴan gudun hijira ɗaya kacal kawo yanzu.
Wani jami’in agajin gaggawa da ke aiki a yankin ya tura wa BBC hotunan yanayin da ƙananan yara suke ciki a sauran sassa, kuma hotunan suna da munin gaske don kuwa sun zarce waɗanda aka gani a baya.
Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin jama’a da muhallin su, ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasar, kuma ya hana a samu hanyar kai ɗauki ga ɗimbin masu buƙata.
Masu aikin agaji dai suna ci gaba da kiran a samar da yanayi mai kyau domin shigar da kayan abinci da sauran abubuwan buƙata ga jama’a, idan har ana fatan samun sauƙin yanayin da ake ciki.