Waiwaye: Naɗin manyan hafsoshin tsaro, sanya dokar ta-ɓaci kan satar waya a Kano

Wannan maƙale ce da duba muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron Najeriya

.

Asalin hoton, Facebook/Tinubu

A farkon makon da ya gabatan ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da kwamandojin fadar shugaban ƙasa.

Matakin na zuwa ne bayan sabon shugaban ya sanar da sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ƙasar daga aiki nan take.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ta bayyana Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkar tsaro wato 'National Security Adviser'.

Shugaban Najeriyar dai ya naɗa Manjo Janar C.G Musa a matsayin babban hafsan tsaro, bayan sallamar Laftanal Janar Lucky Irabor.

Tafiyar Tinubu taron harkokin kuɗi na duniya a Faransa

a

Asalin hoton, Daddy Olusegun

Bayan naɗin sabbin jagororin tsaron ne kuma, shugaban na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kama hanyar faransa domin halartar taron nazari tare da rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudi ta duniya da aka gudanar a birnin Paris.

Yarjejeniyar za ta kasance ta fifita ƙasashe masu rauni wajen bayar da tallafi da saka hannun jari sakamakon mummunar tasirin sauyin yanayi, da kuma sakamakon cutar korona.

An dai tsara shugaba Tinubu zai koma Najeriya ranar Asabar, to sai da maraicen ranar ta Asabar fadar shugaban ƙasar ta fitar da wata sanarwa da maraicen ranar Asabar cewa shugaban zai zarce Birtaniya domin wata ziyara ta radin kansa.

An ƙaddamar da dokar ta-ɓaci kan satar waya a Kano

.

Asalin hoton, AFP

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ƙaddamar da dokar ta-ɓaci game da satar waya da kuma wasu laifukan da ake aikatawa a birnin.

Kafofin yaɗa labarai sun ce majalisar dokokin jihar ta nuna damuwa kan matsalolin satar waya da sane da shan miyagun kwayoyi da ma waɗansu laifukan da ke barazana ga zaman lafiyar jihar.

A wata mahawara da shugaban masu rinjaye na majalisar ya gabatar, 'yan majalisar sun amince kan cewa akwai buƙatar a gaggauta magance matsalar kafin ta yi ƙamari.

Majalisar dokokin ta kuma amince da wani ƙuduri da ya buƙaci gwamnatin jihar ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin hukunta waɗanda aka kama da laifi.

Emefiele ya maka gwamnatin Najeriya a kotu

d

Asalin hoton, CBN

A dai cikin makon da muke bankwan da shi din ne tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Mista Godwin Emefiele ya shigar da ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya, yana ƙalubalantar tsare shi da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke yi.

A cikin ƙudurin da ya gabatar, Emefiele ya nemi kotu ta tilasta wa hukumomi tabbatar masa da 'yancinsa na walwala da 'yancin zirga-zirga, don kuwa a cewarsa, babu hujjar ci gaba da tsare shi.

Sai dai, Ofishin Atoni Janar na Tarayya da kuma hukumar DSS sun ce tsare dakataccen gwamnan bankin yana kan doka.

Sun kuma ce tsare jami'in ya dogara ne kan wani umarnin kotun majistare don haka suka nemi babbar kotun ta kori buƙatar da Emefiele ya gabatar.

ASUU ta soki Shirin bayar da bashin karatu ga ɗalibai da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi

z

Asalin hoton, FESTUS KEYAMO/TWITTER

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.

A wata hira da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwuwa ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu "ba zai dore ba".

Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa".