Arsenal ta cimma matsaya kan Jesus, Bayern ta karyata batun sayen Ronaldo

Arsenal ta cimma matsaya da Manchester City domin sayen dan wasan gaba na Brazil Gabriel Jesus, inda Gunners din za ta biya kudi fan miliyan 45 domin daukan dan wasan mai shekara 25. (Fabrizio Romano)

Paris St-Germain za ta kyale dan wasan tsakiya na Netherlands Georginio Wijnaldum ya bar kungiyar a cikin wannan kaka. Leicester City ne dai ke kokarin sayen dan wasan yayin da Everton da Wolves duk su ma suke nuna sha'awarsu. (90min) 

Sabbin wadanda suka mallaki kungiyar Chelsea sun yi wa mai horas da 'yan wasan kungiyar Thomas Tuchel alkawarin cewa za a sayo masa sabbin 'yan wasa har guda shida. (Telegraph - subscription required) 

Daraktan kungiyar Bayern Munich Hasan Salihamidzic ya ce babu kamshin gaskiya kan rade-radin da ake yi cewar kungiyar za ta sayi dan wasan gaba na Manchester United da Portugal Cristiano Ronaldo. (Sky Germany - in German)

Dan wasan gaba na kungiyar Leeds dan asalin Brazil winger Raphinha, mai shekara 25, ya ki amincewa da tayi daga wasu kungiyoyin kwallon kafa na Ingila saboda yana son tafiya kungiyar Barcelona(Sport - in Spanish)

Chelsea za ta saurari masu taya mai tsaron gida na Spain Kepa Arrizabalaga bayan da dan wasan ya ce babban manufarsa ita ce ya buga wasa. (Mirror) 

Har yanzu Tottenham da Middlesbrough ba su cimma matsaya ba kan sayar da dan wasan 'yan kasa da shekara 21 na Ingila Djed Spence, kasancewar Middlesbrough din na bukatar kudi kimanin fan miliyan 15 da wasu doriya kan dan wasan.(Sun) 

Yayin da Ajax ta fara wasannin share fagen shiga kakar wasanni a ranar Juma'a ba a ga dan wasan gefe na kasar Brazil ba Anthony a cikin tawagar kungiyar ba, kasancewar yana kokarin ganin ya bi tsohon mai horaswa Erik ten Hag wanda ya tafi Manchester United(Mirror)