Yadda za ku gane ko kuna da ciwon zuciya ko ƙoda ta farcenku

Asalin hoton, Getty Images
Farcenku da ke matsayin ado a hannayenku, suna kuma matsayin matattun ƙwayoyin halitta na jiki. Sai dai waɗannan ƙumba za su iya nufin abubuwa da dama game da lafiyarku wanda watakila ba ku sani ba.
Wani bincike da aka gudanar a ya nuna cewa ta hanyar kallon farcen mutum, za a iya gane cutuka da dama da ke da alaƙa da jiki, ciki har da zuciya ko ƙoda.
Har ila yau, an gudanar da wani bincike kan mutum 272 a kwalejin kiwon lafiya a jihar Karnataka na Indiya.
A wannan bincike da aka yi kan lafiyar fata, an kuma yi kan waɗanda ke fama da cutuka da dama da kuma sauyi a faratansu.
Binciken ya nuna cewa kashi 26 na mutanen na fama da matsalolin numfashi, kashi 21 na fama da matsalolin jini, kashi 17 kuma matsalar hanta da tsananin ciwon ciki, sannan kashi 12 na fama da matsalolin zuciya da kuma ƙoda.
Ya kuma gano cewa idan matsalar numfashi ta taɓarɓare, ya fi shafar farcen mutum. Haka kuma, idan akwai cutuka da suka jiɓanci jini a jiki ko kuma ciwon hanta, zuciya ko kuma ƙoda, hakan yana bayyana a farata.
Don haka, idan ka ga sauyi a farcenka, to ka je ka ga likita don karɓar shawarwari.
Bari mu duba irin sauye-sauyen da ake samu a farce, wanda zai nuna ko alama ce ta wata cuta.

Asalin hoton, Getty Images
Shin duk wani sauyi a farce alama ce ta cuta?
Duk da cewa farata a yawan lokuta na alamta yanayin lafiyar jiki, hanyoyi da ake ɗauka na ƙawata farata a wasu lokuta na iya kawo sauyi a cikinsu.
Farata da ke hannu da kuma ƙafa na kare sassan jiki daga samun rauni. Faratan da ke hannun mutum na taimakawa wajen taɓa sassan jiki musamman inda yake yi wa mutum ƙaiƙaiyi.
Bincike da aka gudanar a ɓangaren sanin fannin fata ya nuna cewa sauyi a launin farce da kuma yanaynsa na da alaƙa da cutuka da dama.
Wasu lokuta fiye da alama ɗaya na iya bayyana akan farata a lokaci guda.

Asalin hoton, Getty Images
Ciwon zuciya da sauyi a farata

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon bincike ya nuna cewa faratan waɗanda ke fama da ciwon zuciya suna kasancewa a lankwashe suna kallon ƙasa, kuna ana ganin dogayen layi a kansu.
Dakta Sameer Gupta, likitan zuciya a wani asibiti mai suna Metro Hospital, ya ce, " Da ma faratan ɗan'adam suna kama da ruwan hoda. Idan launinsu ya koma mai ɗan haske-haske, hakan yana nuna cewa akwai rashin jini a jiki."
"Haka kuma, idan launin ya zama shuɗi, alama ce da ke nuna akwai ƙarancin sinadarin oxygen a jiki. Abin da ke haddasa farce ya koma shuɗi zai iya zama alamar cutar zuciya ko kuma huhu. Ya kamata a yi gwaji domin gano abin da ya haddasa cututtukan."
Har ila yau, idan launin farata ya koma shuɗi, wata alama ce da ke nuna cututtukan da suka haɗa da asthma, da rashin sinadarin oxygen da kuma hawan jini a jijiyoyin jini.
Cutar huhu
Haka kuma, yadda yanayin wasu farata ke kasancewa - yana nuna alama ta matsalolin numfashi, musamman idan farce ya lankwashe ko ya yi ƙasa.
An kuma yi duba kan dogayen layuka da ake gani a faratan mutum, yawan ƙaryewar su ko kuma sauyawar launinsa.
Dakta Rashmi Upadhyay, wata likita a cibiyar lafiya a Greater Noida, ta ce matsaloli da ake samu masu alaƙa da huhu na faruwa ne yayin da alamamo a sassan jiki suka fara fitowa.
"Alal misali, launin fata ya koma mai haske-haske. Fata ya yi siriri ko ya riƙa sheƙi. Akwai kuma wasu alamomi da yawa a cikin farata, wadda muke ganin yana nufin cewa akwai matsala a cikin hudu."

Asalin hoton, Getty Images
Launin farata da ke nuna matsala a hanta da ciki
A wani bincike da aka yi kan nazarin fata, mutum 46 da aka samu da matsalar hanta da kuma ciwon ciki na gastrointestinal - faratansu sun kasance masu launin ruwan ɗorawa, dogaye da kuma layuka a cikinsu.
A cewar Dakta Sameer Gupta, lankwashewar farce ko ya ɗan yi ƙasa, na nufin alama ce ta wata matsanancin ciwo.
Yanayin farata da ke nuna matsaloli na ciwon ƙoda
Har ila yau, binciken da aka gudanar ya gano cewa mutanen da ke fama da ciwon ƙoda farcensu zai iya zama mai launin ruwan ɗorawa, dogayen layuka a cikinsu da kuma saurin ƙaryewa.
"Faratan Lindsay misali ne na iri mutanen da ke fama da ciwon ƙoda," a cewar Prajit Majumdar, wani likitan masu fama da ciwon ƙoda a asibitin Yashoda da ke birnin Ghaziabad na ƙasar Indiya.
Sai dai, wasu lokuta saboda raunuka ko ƙawata faratan - hakan yana sa ana samun sauye-sauye da dama.
Don haka, idan ka ga wani bambanci ko kuma sauyi a farcenka, ka tuna cewa yana da muhimmanci ka je ka ga likita.











