Real za ta kara da Girona ba tare da Bellingham ba

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fafata da Girona a wasan mako na 25 a La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
To sai dai za ta yi wasan ba tare da Jude Bellingham ba, wanda aka dakatar wasa biyu.
Hakan ya biyo bayan jan katin da aka yi masa a karawa da Osasuna a La Liga.
Alkalin wasan ne ya rubuta a rahotonsa, bayan tashi daga karawar cewar Bellingham ya fada masa kalaman da ba su dace ba.
Shi ne hukumar kwallon kafar Sifaniya ta hukunta shi da dakatarwa wasa biyu.
Real ta je ta doke Girona 3-0 cikin Disambar 2024 a gasar ta La liga a wasan farko tsakaninsu.
Wadan da suka ci nata kwallayen sun hada da Jude Bellingham da Ader Guler da kuma Kylian Mbappe.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 54, sai Atletico ta biyu da 53 da kuma Real Madrid mai maki 51.
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana yan wasan Real Madrid da za su fuskanci Girona ranar Lahadi.
Yan wasan Real Madrid:
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.
Masu buga tsakiya: Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuna Ceballos.
Masu cin kwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.











