Mece ce HMPV, sabuwar cuta nau'in korona da ta kunno kai?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara yin kulle ga fasinjojin da suka shiga ƙasar daga ƙasashen da ke fama da cutar numfashi ta HMPV.
Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Najeriya, NCDC ta ce fasinjojin za su rinƙa yin gwaji tun a filin jirgi domin tabbatar da cewa ba sa ɗauke da cutar.
Darekta a hukumar ta NCDC, John Oladepo ya ce Najeriya za ta fara gudanar da kullen ne ga fasinjojin har na tsawon kwana uku kafin a ƙyale su su shiga gari ko kuma wuraren da suka nufa a cikin ƙasar.
"Muna aiki tare da ma'aikatan kan iyaka da ke aiwatar da kullen, muna tabbatar da cewa dukkannin fasinjoji sai sun cike fam na gwaji. Za su saka musu idanu har na tsawon kwana biyu zuwa uku kafin a kyale su su tafi wurin da suka nufi zuwa," in ji darektan.
Ya ƙara da cewa cutar na shafar tsarin numfashin ɗan'adam inda ya ce za su tabbatar da jama'a na cikin ƙoshin lafiya domin tabbatar da cewa annobar ba ta kutsa cikin jama'a ba.
"Ita wannan ƙwayar cutar na shafar numfashi saboda haka ba cuta ba ce da za a yi burus da ita ba.,"in ji shi.
"Ku tabbatar da wuraren da kuke na cikin tsafta, idan kuma wani yayi atishawa to ka tabbatar ta ba shi ratar mita biyu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Ku saka takunkumin fuskan domin tabbatar da tsafta da gujewa kamuwa daga cutar. "
Tuni dai jama'a ke ta yaɗa bayanai na gaskiya da na ƙanzon kurege dangane da cutar a kafafen sada zumunta, kuma kasashe na ta ɗaukar mataki wajen kare al'ummarsu daga kamuwa da cutar.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da kuma cibiyar hana yaɗuwar cutuka ta Afirka ba su fitar da gargaɗi kan cutar ba.
To sai dai mutanen da suka fara nuna damuwa dangane da wannan cuta ta numfashi na ta neman bayanai bisa tsoron cewa ko za ta yi illa irin wadda annobar korona virus ta yi wa duniya.
Bincike dai ya nuba cewa cutar ta numfashi ta HMPV ka iya shafar mutane a kowane shekaru musamman yara da tsofaffi da ma mutanen da ba su da ƙoashin lafiya waɗanda garkuwarsu ta yi ƙasa.
Cibiyar da ke daƙile yaɗuwar cutuka ta Amurka ta ce cutar ta HMPV ka iya haddasa matsananciyar mura ko lumoniya
Cibiyar ta ƙara da cewa cutar dangi ce daga ƙwayoyin cutuka masu nasaba da numfashi kuma ta kasance a duniya tun 2001 lokacin da aka fara gano ta a ƙasar Neitherlands.
HMPV ta fi saurin yaɗuwa a lokutan sanyi da hunturu kuma jama'a na kamuwa da ita ne sakamakon mu'amila da masu ɗauke da cutar ko kuma wurin da ke ɗauke da ƙwayar cuta.
Cutar ta numfashi ba ta da allurar rigakafi to amma ana yin amfani da maganin da ake warkwar da sauran cutukan numfashi a kanta sannan tana buƙatar tsafta da lura sosai musamman idan aka alamun cutar.
Me ya sa HMPV ta karaɗe kafafen watsa labarai?
Rahotannin da BBC ba ta iya tabbatar da su ba sun nuna cewa an samu mutanen da ke ɗauke da cutar ta HMPV a arewacin ƙasar China musamman a tsakanin ƙananan yara.
Wannan labarin dai na zuwa ne shekaru biyar bayan ɓarkewar annobar korona a Wuhan da ke China.
Hotunan da bidiyo na mutanen da ke sanye takunkumi a asibitoci a China sun warwatsu cikin gaggawa a kafafen sada zumunta sannan kafafen watsa labarai na cikin gidan China sun kwatanta al'amarin da irin abin da ya faru a zamanin annobar korona.
Kafafen watsa labarai na China sun ce hukumomin lafiya na ƙaddamar da wasu matakan kariya wajen daƙile bazuwar cutar lumoniya d ke alaƙa da cutar ta HMPV.
Alamu da hanyoyin kariya daga cutar HMPV
Alamun cutar HMPV na kama da sauran cutukan numfashi
- Zazzaɓi
- Tari
- Yoyon hanci
- Mura
- Saurin gajiya
- Harsawa
- Gudawa
- Tashin zuciya
- Zafi a maƙogwaro
Wasu dag acikin manyan alamun sun haɗa da:
- Numfashi da ƙyar
- Asthma
- Kakari
- Ɗaukewar numfashi
- Saurin gajiya
- Mashaƙo
- Lumoniya
Yadda cutar HMPV ke yaɗuwa
Ƙwayar cutar ta fi yaɗuwa ne a lokacin da ka yi hulɗa da mutumin da ya kamu da mai ɗauke da cutar. Saboda haka mutum ka iya kamuwa da cutar idan ya yi waɗannan abubuwa:
- Taɓa wurin da ke ɗauke da ƙwayar cutar
- Taɓa bakinka ko hancinka ko kuma idanunka bayan taɓa ko gaisawa da mai ɗauke da cutar.
- Idan mai ɗauke da cutar ya fesa maka furkakin yawu ta hanyar tofar da yawu ko ataishawa ko kuma tari.
- Yin mu'amala da mai ɗauke da cutar kamar gaisawa hannu da hannu ko kuma taɓa jikinsa.
Cutar ka iya ka iya ɗaukar kwana uku zuwa shida kafin ta bayyana.
Shin HMPV na kama da korona?
Dukka cutukan biyu na da alaƙa da numfashi kuma ana ɗaukar su ne sannan kuma suna da alamu masu kama da juna kamar yoyon hanci da tari da zazzaɓi da toshewar hanci da ciwon maƙogwaro da kuma katsewar numfashi.
Cutukan kan yaɗu ta hanyoyi iri ɗaya kuma dukkanninsu ka iya kai wa ga kwantar da mai ɗauke da su a asibiti.
Sai dai kuma ita cutar HMPV ba ta da mahani ko kuma rigakafi nata na kanta kawo yanzu saɓanin annobar korona.
HMPV cutar numfashi ce ta lokaci zuwa lokaci kamar lokacin hunturu da damina, inda ita kuma cutar korona lokaci zuwa lokaci kan yaɗu a tsawon shekara.
Bincike ya nuna cewa masu ɗauke da HMPV sun ninka masu ɗauke da korona sau uku a kasashen da suka yi fama da korona.






