Fitattun mutanen da suka rasu a 2024

Wasu daga cikin fitattun mutanen da suka rasu a 2024

Asalin hoton, Agencies/Social Media

Lokacin karatu: Minti 6

Shekara ta 2024 kamar sauran shekaru ta zo wa duniya da abubuwa da dama waɗanda tarihi ba zai manta da su ba.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a shekarar, duniya ta yi rashin wasu fitattun mutane, kama daga 'yan siyasa zuwa sarakunan gargajiya da sauransu.

A yayin da muke bankwana da shekarar, BBC ta yi nazarin wasu daga cikin fitattun mutanen da suka rasu a duniya da ma Najeriya a 2024.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi

Ibrahim Raisi

Asalin hoton, Reuters

A cikin watan Mayun shekarar ne kuma shugaban Iran, Ebrahim Raisi ya rasu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ƙasar.

Jirgin saman mai saukar ungulu na ɗauke ne da shugaba Ebrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar Hossein Amir Abdollahian.

Sauran waɗanda suke cikin jirgin sun haɗa da Ayatollah Mohammad Ali Al-e Hashem - limamin masallacin Juma'a na birnin Tabriz da Janar Malek Rahmati watau gwamnan lardin gabashin Azerbaijan.

Kwamandan askarawan kare lafiyar shugaban ƙasa, Sardar Seyed Mehdi Mousavi, da waɗansu jami'an tsaron na cikin waɗanda suka yi hatsari a jirgin mai saukar angulu.

Mutuwar Mista Raisi ta girgiza Iran da ƙawayenta, sannan ta sa an shirya zaɓe a ƙasar domin zaɓen sabon shugaban ƙasar.

Shugaban Namibia Gein-gob

Tsohon shugaban Namibia

Asalin hoton, Getty Images

A farkon watan Fabrairu ne shugaban ƙasar Namibiya, Hage Gein-gob, ya rasu a yayin da ake masa maganin cutar kansa a wani asibiti da ke Windhoek babban birnin ƙasar.

Tun a farkon shekarar ne aka kwantar da Mista Geingob, mai shekarar 82 a asibiti bayan da likitoci suka sanar da cewa yana ɗauke da cutar kansa.

Da fari an yi tunanin cewa zai je Amurka don a yi masa magani.

Shugaban - wanda ya zama shugaban ƙasar a 2015 - na cikin wa'adin mulkinsa na biyu lokacin da ya rasu.

Jagoran adawar Rasha, Alexei Navalny

Alexei Navalny

Asalin hoton, Reuters

Alexei Navalny ya mutu a wani gidan yari da ke wani yanki mai tsananin sanyi kamar yadda kamfanonin dillancin labarai suka ruwaito.

Hukumar kare hakkin ɗan'dam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ɗora alhakin mutuwar tasa kan hukumomin ƙasar.

Ana kallonsa a matsayin ɗan adawar da yake yawan sukar Shugaba Vladimir Putin.

Yana zaman gidan yari na tsawon shekara goma sha tara saboda laifukan da ake ganin bi-ta-da-ƙulli siyasa ne.

A ƙarshen shekarar 2023 ne aka mayar da shi gidan yarin da ke yankin Arctic da ake gani a matsayin mafi azabtarwa.

Tsohon shugaban CAF Issa Hayatou

Tsohon Shugaban CAF

Asalin hoton, Getty Images

A cikin watan Agustan shekarar ne kuma tsohon shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afrika Issa Hayatou ya rasu yana da shekara 77.

Dan ƙasar Kamarun ya kwashe shekara 29 yana shugabancin Hukumar, wanda ya fara a 1988 zuwa 2017.

Yana kuma da babban matsayi a Hukumar kwallon Kafa ta Duniya Fifa.

Ya zama Mamba a kwamitin Fifa mai shalkwata a Switzerland daga 1990 zuwa 2017.

Lokacin da aka dakatar da Sepp Blatter, Hayatou ne ya zama muƙaddashin shugaban Fifa daga 2015 zuwa 2016.

Tsohon firaministan Nijar, Hama Amadou

Tsohon firaministan Nijar

Asalin hoton, Getty Images

A cikin watan Oktoba ne tsohon firaministan Nijar, Hamma Amadou ya rasu yana da shekara 74 a duniya.

Hama Amadou, tsohon madugun adawa ne kuma jagoran jam'iyyar Modern FA Lumana.

Tsohon firaministan ya kasance babban jigo a siyasar Nijar, wanda ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da muƙamin firaminista sau biyu - wata daga 21 ga watan Fabrairun 1995 zuwa 27 ga Janairun 1996 ƙarkashin shugabancin Mahamane Ousmane.

Sai kuma a karo na biyu daga 31 ga watan Disamban 1999 zuwa 7 ga Yunin 2007 a ƙarƙashin Mamadou Tandja.

A shekarar 2011 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dokokin ƙasar, muƙamin da ya riƙe har zuwa shekarar 2013.

Fitattun mutanen da suka mutu a yaƙin Gaza

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan kwashe fiye da shekara guda Isra'ila na kai hare-harer ramuwar gayya kan ƙungiyar Hamas da ta kai mata hari ranar 7 ga watan Oktoban 2023 inda ta kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Isra'ila ta kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar manyan jagororin ƙungiyar Hamas da ƙawayenta.

Cikin waɗanda aka kashe akwai shugabannin Hamas Biyu, Isma'ila Haniyeh da aka kashe ranar 31 ga watan Yuli a wani hari da aka kai gidan da ya sauka a birnin Tehran lokacin da ya je ƙasar domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar.

Sannan a tsakiyar watan Oktoba rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kisan jagoran ƙungiyar da ya maye gurbin Haniyeh, wato Yahya Sinwar.

Kafin nan a ranar 28 ga watan Satumba, rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe shugahan ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah.

Kisan nasa na zuwa ne bayan jerin hare-hare cikin dare da Isra'ila ta riƙa kai wa birnin Beirut, da ta ce tana kai wa Nasrallah da sauran kwamandojin ƙungiyar Hezbolla.

Fitattun 'yan Najeriya da suka rasu a 2024

Laftanar Janar Lagbaja

Janar Lagbaja

Asalin hoton, Nigerian Amry

A farkon watan Nuwamban shekarar ne kuma gwamnatin Najeriya ta sanar da mutuwar babban hafsan sojin ƙasa na na ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Gwamnatin Najeriya ta ce ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

An kwashe tsawon lokaci ba a ga marigayi Lagbaja a cikin al'umma ba, lamarin da ya sanya aka riƙa nuna shakku kan lafiyarsa.

Kodayake a cikin sanarwar mutuwar tasa ba a bayyana cutar da ta yi ajalisa ba, sai dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana marigayin da "wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron ƙasar".

Mahaifiyar Yar'Adua, Hajiya Dada

Hajiya Dada

Asalin hoton, Sagil Royal Photograpy

A farkon watan Satumbar wannan shekarar ne, mahaifiyar tsohon Shugaban Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ta rasu.

Hajiya Fatima - wadda aka fi sani da Dada - ta rasu tana da shekara 100 a duniya.

Hajiya Dada ta kasance dattijuwar da ake ganin kimarta a ƙasar, lamarin da ya sa 'yansiyasa a ƙasar a lokuta daban-daban ke tururuwar gaishe ta duk lokacin da suka shiga garin Katsina.

Ɗanta Umaru Musa ya rasu yana kan gadon mulkin Najeriya a watan Mayun 2010 bayan shafe watanni yana jinya.

Kafin haka, yayansa Shehu Musa Yar A'dua wanda tsohon mataimakin shugaban mulkin soja ne ya rasu a watan Disamban 1992.

Sarkin Gobir, Isa Bawa

Isa Bawa

Asalin hoton, Zazzau Emirate Photograper

A ranar 21 ga watan Agusta ne kuma aka samu rahotonnin mutuwar sarkin na Gatawa, Alhaji Isa Bawa, inda 'yanbindiga suka kashe shi bayan garkuwa da shi.

Mutuwar sarkin ta girgiza 'yan ƙasar da dama, kasancewa mako guda kafin kisan nasa, an ga sarkin a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya 'yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa'adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.

Marigayin ya shafe tsawo mako uku a hannun 'yanbindigar da suka yi garkuwa da shi a yankin Kwanar Maharba lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.

Sarkin Ningi

Sarkin Ningi

Asalin hoton, NINGI EMIRATE/FACEBOOK

Haka a ranar 25 ga watan Agusta Allah ya yi wa Sarkin Ningi da ke jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya, rasuwa.

Cikin sanarwar rasuwar tasa da masarautar ta fitar ta ce sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birinin Kano, yana da shekara 88 a duniya.

Bayanai sun ce sarkin ya rasu ne bayan ya dawo Najeriya daga Saudiyya inda ya je domin duba lafiyarsa.

An haifi marigayi Alhaji Yunusa Danyaya a shekarar 1936, a garin Ningi kuma ya zama sarki a shekarar 1978, sannan ya kwashe shekara 46 a gadon sarauta.