Hage Geingob: Shugaban Namibia ya rasu yana dan shekara 82

.

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Shugaban kasar Namibiya, Hage Gein-gob, ya rasu a yayin da ake masa maganin cutar kansa a wani asibiti da ke Windhoek babban birnin kasar.

Mataimakin shugaban kasar, Nangolo Mbumba ya sanar da mutuwar Mr Geingob da sanyin safiyar Lahadi.

Wata sanarwa da Mr Mbumba ya fitar ta ce "Matarsa, Madame Monica Geingos da yayansa suna tare da shi a lokacin da ya rasu,"

A watan da ya gabata ne Mr Geingob, dan shekarar 82 ya sanar da cewa likitoci sun ce yana dauke da cutar kansa.

Ofishinsa ya sanar da cewa zai je Amurka don a yi masa magani, amma zai koma Namibia a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Mr Geingob ya zama shugaban kasa ne a 2015, kuma ya rasu ne yana cikin wa’adin mulkinsa na biyu.

An yi masa aiki kan cutar ta kansa a 2014, kuma daga bisani ya sanar da cewa ya warke daga cutar.

Na dai tsara gudanar da zaben shugaban kasan Namibia da na majalisar dokoki, a watan Nuwamban bana.

Jam’iyyarsa ta Swapo mai rike da mulki tun bayan samun yancin kasar a 1990, ta zabi Mrs Nandi-Ndaitwah domin yi mata takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Yanzu haka dai, Mrs Nandi-Ndaitwah ce mataimakiyar firaiministan kasar, kuma idan ta lashe zaben mai zuwa za ta zamo mace ta farko a tarihi da ta rike wannan mukami.