Tsohon shugaban CAF Issa Hayatou ya rasu

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afrika Issa Hayatou ya rasu yana da shekara 77.

Dan ƙasar Kamarun ya kwashe shekara 29 yana shugabancin Hukumar, wanda ya fara shugabancinsa daga 1988 ya kuma gama a 2017.

Yana kuma da babban matsayi a Hukumar kwallon Kafa ta Duniya Fifa.

Ya zama Mamba a kwamitin Fifa wanda ke zaune a Switzerland daga 1990 zuwa 2017.

Lokacin da aka dakatar da Sepp Blatter, Hayatou ne ya zama muƙaddashin shugaban Fifa daga 2015 zuwa 2016.

Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya Gianni Infantino ya mika saƙon ta'aziyyarsa da iyalan Hayatou a Instagram.

"Mummunan labari jin mutuwar tsohon shugaban Caf, tsohon shugaban Fifa na riƙon kwarya, mataimakin shugaban Fifa, kuma mamba a kwamitin Fifa, Issa Hayatou," kamar yadda Infantino ya rubuta.

"Masoyin wasanni, ya bayar da duka rayuwarsa ne wajen gudanar da harkokin wasanni.

"A madadin Fifa muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalansa da 'yan uwansa da tsofaffin abokan aikinsa da duk wani da ya san shi. Ka Huta Lafiya."

A 2021 Fifa ta dakatar da Hayatou saboda karya wasu dokokinta na wasannin tsalle tsalle, lokacin da aka sanya hannu kan wata yarjejeniya mafi girma a harkokin kwallon ƙafar Afrika da wasu kafafen yaɗa labaran Faransa da kamfanin Lagardere a 2016.

Sai dai kotun sauraren kararrakin wasanni ta soke hukuncin a watan Fabrairun 2022.