Wane ne tsohon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya marigayi Taoreed Lagbaja?

Asalin hoton, Nigeria Defense Headquaters
Gwamnatin Najeriya ta sanar da mutuwar babban hafsan sojin ƙasar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, bayan ya sha fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.
An kwashe tsawon lokaci ba a ga marigayi Lagbaja a cikin al'umma ba, lamarin da ya sanya aka riƙa nuna shakku kan lafiyarsa.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba, ya ce Lagbaja ya rasu ne a cikin daren ranar Talata a Lagos.
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai matuƙar baƙin cikin snaar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojin ƙasa, mai shekaru 56," Cewar sanarwar.
Kodayake sanarwar ba ta bayyana cutar da ta yi silar mutuwarsa ba, sai dai shugaban ƙasar ya bayyana marigayin da "wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron ƙasar".
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa marigayi Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ƙasar a watan Yuni na 2023,inda ya maye gurbin Laftanar Janar Faruk Yahaya, wanda tsahon shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya naɗa a 2021.
An haifi Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairun 1968 a Ilobu na jihar Osun da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Ya halarci makarantun St Charles Grammar da kuma Kwalejin horas da malamai ta ATC da ke Osogbo, kafin daga bisani ya shiga makarantar horas da sojoji ta NDA a shekarar 1987, inda ya kammala a ranar 19 ga watan Satumba kuma ya fito da muƙamin second lieutenant.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsohon babban hafsan sojin ya taka rawa a cikin shirin Majalisar dinkin Duniya na samar da zamna lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, MONUC, daga shekarar 2004 zuwa 2005.
Ya kuma shiga cikin rundunar ko-ta-kwana ta ƙungiyar Ecowas, wadda cibiyarta ke ƙasar Mali, daga watan Yuni zuwa Agustan 2010.
Haka kuma Laftanar Janar Lagbaja ya taka rawa a wajen yaƙar ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Boko Haram.
A lokacin mulkin Shugaba Muhammdu Buhari, Lagbaja ya kasance mamba cikin rundunar LAFIYA DOLE tsawon shekara uku, daga watan Disamban 2015 zuwa watan Janairun 2018.
Ya jagoranci rundunar a Monguno kusa da Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriyar.
Laftanar Janar Lagbaja ya karanci fannin nazarin ƙasa, (Geography) a NDA. Ya kuma samu digiri na biyu a fannin dubaru (Strategic Studies) a 2014 a kwalejin kwas ɗin zama babban hafsan soji a Amurka.
Rahotanni sun ce tun bayan ba shi muƙamin, ya riƙa fama da rashin lafiyar da take kawo masa tsaiko wajen gudanar da aikinsa, lamarin da ke sanyawa yana yawan fita ƙasashen ƙetare neman magani.
A ƙarƙashin mulkinsa, an samu ƙaruwar hare-haren Boko Haram da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa, musamman a arewa da kuma tsakiyar Najeriya.
Babban al’amarin da ya faru a ƙarƙashin mulkinsa shi ne satar ɗalibai sama da 200 a wata makaranta a Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ranar 7 ga watan Maris ɗin 2024.
An kuma samu hare-haren ƴanbindiga a cikin babban birnin Najeriya, Abuja, inda aka riƙa sace mutune domin karɓar kudin fansa.











