Brittney Griner: Amurka ta yi wa Rasha tayin yarjejeniya

Asalin hoton, Reuters
Amurka ta yi wa Moscow tayin wata yarjejeniya da za ta bayar da damar sako wato ƴar wasan kwando ta Amurka Brittney Griner wadda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na shekara tara.
Griner wadda ta lashe lambar zinari sau biyu a gasar Olympics, an same ta da laifin mallaka da fasa kwabrin wani nau'in mai da ake samu daga wiwi.
Sakataren watsa labarai na ma'aikatar tsaron Amurka John Kirby ya bayyana cewa tayin da Amurka ta yi wa Rasha tayi ne mai gwaɓi, sai dai bai fito ɓaro-ɓaro ba ya yi ƙarin bayani kan tayin .
Sai dai kafofin watsa labarai na Amurka na ta yamaɗiɗi inda suke cewa akwai yiwuwar za a yi musayar fursuna ne inda Amurka za ta miƙa wani mai safarar makamai na ƙasar Rasha domin karɓo gwarzuwar yar wasan kwandon.
Viktor Bout - wanda shi ne fursunan da ake ganin Amurka za ta miƙa, na zaman gidan yari na shekara 25 a Amurka.
Haka ita ma mai magana da yawun Fadar White House Karine Jean Pierre ta tabbatar da cewa Amurka na iya bakin ƙoƙarinta wurin mayar da Griner da wani fursunan Amurka gida inda ta ce tun da farko bai ma kamata Rasha ta kama ƴar wasan ba.
"Hukuncin da aka yanke wata tunatarwa ce kan abin da duniya dama ta riga ta sani. Rasha na riƙe da Brittney ba bisa ƙa'ida ba. Bai kamata ba tun da farko ma a ce ta yi mata shari'a, mun ta kiraye-kiraye ga Rasha ta sake ta domin komawa ga iyalanta da ƴan uwa da abokan arziki da abokan wasanta," in ji Karine Jean.
Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya ce Rasha da duk wata ƙasa da ke riƙe da wani mutum ba bisa ƙa'ida ba alama ce ta barazana ga tsaron duk wani matafiyi ko kuma ma'aikaci da ke zaune a ƙasar waje.











