Faransa ta gayyaci Mateta domin buga mata Olympics a Paris

Asalin hoton, Getty Images
Thierry Henry ya sanar da ƴan wasa 18 da za su buga wa Faransa Olympic, ciki har da ɗan ƙwallon Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta ɗaya tilo da ke buga Premier League.
A gasar ƙwallon kafa ta Olympic ta matasa ƴan kasa da shekara 23, an amince tawaga ta gayyaci manya uku da suka haura ka'ida.
Mateta, mai shekara 27, ya ci ƙwallo 16 a Premier League da ta wuce, amma babbar tawagar Faransa ba ta taɓa gayyatarsa ba.
Ƙungiyoyi ba sa barin ƴan ƙwallo su halarci Olympics, inda Real Madrid ta hana Kylian Mbappe zuwa ya wakilci kasarsa a wasannin da za a yi a Faransa.
To sai dai Michael Olise, wanda ya koma Bayern Munich kan £50m daga Crystal Palace, yana cikin waɗan da Faransa ta gayyata.
Amma dai mai tsaron bayan Chelsea, Lesley Ugochukwu, mai shekara 20, yana jiran ko-ta-kwana.
Henry, tsohon ɗan wasan Arsenal, shi ne kociyan matasan Faransa ƴan kasa da shekara 21, shi ne kuma zai kai tawagar zuwa gasar tamaula ta Olympic.
Tun cikin watan Yuni ya bayyana ƴan wasan kwarya-kwarya, inda Mateta ya ci ƙwallo biyu a wasan sada zumunta da Faransa ta ci Paraguay 4-1.
Ƴan wasan Faransa da aka gayyata buga Olympic:
Masu tsare raga: Obed Nkambadio (Paris FC), Guillaume Restes (Toulouse)
Masu tsare baya: Loic Bade (Sevilla), Bradley Locko (Brest), Castello Lukeba (Leipzig), Soungoutou Magassa (Monaco), Kiliann Sildillia (Freiburg), Adrien Truffert (Rennes)
Masu buga tsakiya: Maghnes Akliouche (Monaco), Joris Chotard (Montpellier), Desire Doue (Rennes), Manu Kone (Borussia Monchengladbach), Enzo Millot (Stuttgart)
Masu cin ƙwallaye: Arnaud Kalimuendo (Rennes), Alexandre Lacazette (Lyon), Jean-Philippe Mateta (Crystal Palace), Michael Olise (Bayern Munich), Rayan Cherki (Lyon)










