Ana zargin China da kafa haramtattun ofisoshin 'yan sanda a ƙasashen waje

    • Marubuci, Anna Holligan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Rporter
    • Aiko rahoto daga, BBC News, The Hague

Ana zargin gwamnatin China da kafa "ofishin 'yan sanda" biyu a ƙasar Netherlands a ɓoye.

A makon da ya gabata ma an yi irin wannan zargi cewa China ta buɗe ofishin a Najeriya da wasu ƙasashe.

Wata kafar yaɗa labarai ta Netherlands ɗin ta gano cewa "ofisoshin ƙasar wajen", wadda ta ce za su yi aikin difilomasiyya, ana amfani da su ne wajen toshe bakin 'yan adawar China.

Wata mai magan da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Netherlands ta ce kafa ofisoshin ba a hukumance ba sun saɓa wa ƙa'ida.

Ma'aikatar harkokin wajen China ta musanta zargin.

Binciken ya faru ne sakamakon wani rahoto da aka yi wa laƙabi da Chinese Transnational Policing Gone Wild wanda ƙungiyar Sifaniya ta bankaɗo mai suna Safeguard Defenders.

A cewar ƙungiyar, ofisoshin na tsaro daga yankunan China biyu sun kafa ofishin 'yan sanda 54 a nahiya biyar da kuma ƙasa 21. Akasarinsu suna Turai, ciki har da tara a Sifaniya da huɗu a Italiya. A Birtaniya, ta gano akwai ɗaya a Landan da kuma ɗaya a Glasgow na Scotland.

An kafa su ne don su daƙile aikata laifuka tsakanin nahiyoyin duniya da kuma harkokin mulki, kamar sabunta lasisin tuƙi na China. Amma a cewar Safeguard Defenders, a haƙiƙa suna "aikin kama jan ra'ayi ne", inda suke tilasta wa waɗanda ake zargi da sukar China su koma gida.

Kafar labarai ta RTL News da sashen binciken ƙwaƙwaf na Fllow the Money sun ba da labarin Wang Jingyu, wani mai sukar China da ya ce 'yan sandan ƙasar na bin diddiginsa a Netherlands.

Da yake magan ciin Ingilishi, Wang ya faɗa wa 'yan jarida a Netherlands cewa wani mutum ya kira shi yana iƙirarin cewa daga ɗaya daga cikin irin wannan ofisoshin ne. An ba shi shawarar ya koma China "don na magance matsalolina. Kuma na yi tunani game da iyayena".

Tun daga wannan lokacin, ya bayyana aka dinga hantara da tilasta masa, abin da ya ce ya yi imanin wakilan gwamnatin China ne ke aikatawa. Da yake mayar da martani kan lamarin, ofishin jakadancin China ya faɗa wa RTL News cewa bai san da zaman ofisoshin 'yan sandan ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Netherlands, Maxime Hovenkamp ta faɗa wa BBC: "Gwamnatin China ba ta sanar da Netherlands ba ta hanyoyin difilomasiyya. Wannan ya saɓa wa doka."

Ta ce za su bincika don sanin matakin da za su ɗauka. "Abin damuwa ne a ce an saka ɗan China cikin taskun tilasta wa da tsangwama a Netherlands. 'Yan sanda na duba yadda za su ba shi kariya," in ji ta.

Ayyukan sabunta biza ko fasfo ana yin su ne a ofishin jakadanci ko kuma ƙaramin ofishi. Ƙa'idoji a bayyana suke a wannan ɓangare kamar yadda Yarjejeniyar Vienna ta tanada, wadda duka China da Netherlands suka saka hannu kan ta.

Caji ofis na 'yan sanda irin wanda ake zargin China na buɗewa za su iya saɓa wa doka da kuma karya ƙai'dojin ƙasar da aka buɗe su da dokokin da suke ba da kariya a ƙarƙashin harkokin difilomasiyya.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen China Wang Wenbin ya faɗa ranar Laraba cewa abin da aka siffanta da ofishin 'yan sanda a ƙasashen waje "ofisoshin hidima ne ga 'yan China", kuma China na mutunta 'yancin sashen shari'a na ƙasashe.

'Yan China da yawa sun gaza komawa gida saboda annobar korona, kamar yadda ya faɗa wa 'yan jarida: "Don a taimaka musu, hukumomi sun buɗe hanyoyin gudanar da ayyuka ta intanet. Ana yin irin waɗannan ayyuka ne ga mutane kamar duba su a fili da kuma sabunta lasisin tuƙi."

Yanzu aiki na kan gwamnatin Netherlands don tabbatar da cewa ta kare masu sukar China da ke neman mafaka a ƙasar.