Kotu ta aika da dan China da ake zargi da kisan Ummita kurkuku

Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta aike da dan kasar China din nan da ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita kurkuku.

Ana zargin Mista Geng Quanrong da kisan matashiyar, lamarin da ya ci karo da sashe na 221 na kundin laifuka na jihar Kano, a cewar kotun.

Alkalin kotun Mai shari’a Hanif Sanusi Chiroma ne ya tura dan Chinan kurkuku.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a da dare, inda Geng Quanrong, mai shekara 47, ya kutsa kai gidansu Ummita a unguwar Kabuga cikin karamar hukumar Gwale.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da shi a gaban kotun.

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta tabbatar da ganin shari'a ta yi aikinta a batun kashe Ummita.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayin wani jawabi a fadar gwamnatin jihar, ya ce " Kisan zub da jini ne, don haka dole maganar shari'ah ta shigo" kuma sai doka ta yi aikinta.

Kungiyar Sinawa 'yan kasuwa a Najeriya ta yi alla-wadai da kisan da ake zargin Mr Quanrong ya yi wa Ummita.

Da take mika sakon ta'aziyya ga iyayenta, kungiyar ta ce tana ba da cikakken goyon baya ga doka ta yi aikin ta.

A cikin sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce abin da ake zargin Mr Quanrong ya aikata, abin alla-wadai ne kuma babban laifi ne da ya kamata a bar hukumomin tsaro su yi aiki don tabbatar da abin da ya faru.

Mahaifiyar Ummita, Hajiya Lami Sani Buhari ta ce mutumin da ake zargi da kashe 'yarta ya sha zuwa gidansu yana neman ganin Ummita, amma ba ta son fitowa.

Ta ce a ranar da lamarin ya faru, ɗan Chinan da ake zargi ya sake zuwa gidan da daddare inda ya yi ta buga musu kofa, abin da ya tilasta wa mahaifiyar bude masa kofa, don jin abin da ke tafe da shi.

Uwar ta ce Mista Geng ya bangaje ta, ya kutsa kai cikin dakin Ummita, kuma da ganin ta sai ya zare wuka ya yi ta caka mata.