Me ya sa Tinubu ke yawan tafiye-tafiye?

Lokacin karatu: Minti 3

Yanzu haka shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara hutu, inda ya ɗebi wasu kwanaki daga cikin hutunsa na shekara, kuma tuni ya bar Najeriya zuwa ƙasashen Turai a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Bola Tinubu zai yi hutu na tsawon kwana 10 a ƙasashen Faransa da Birtaniya.

"Sanarwar ta ce "Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja ranar Alhamis 4 ga watan Satumba domin fara hutu a nahiyar Turai, tsakanin ƙasashen Faransa da Birtaniya, inda zai yi kwana 10."

Tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi

An shaida cewa shugaba Tinubu na yawan tafiye-tafiye, kuma ita ma wannan tafiyar na daga cikin irin waɗannan tafiye-tafiye da ya saba yi tun bayan hawa mulki a watan Oktoban 2024.

Bayanai sun nuna cewa a cikin watanni 17 da hawansu mulki, Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare sau 41 zuwa ƙasashe 26, kuma sun kwashe kwanaki 180 a ƙasashen ƙetare.

Tafiya ta baya-bayan nan da Tinubu ya yi ita ce zuwa Brazil a cikin watan Agustan da ya gabata, inda ya gana da shugaban ƙasar Luiz Inacio Lula da Silva.

Ya tafi Brazil ne daga ƙasar Japan inda ya halarci taron birnin Tokyo na shugabannin ƙasashe.

Kafin nan, shugaban ƙasar ya yi wasu tafiye-tafiyen zuwa Amurka da Faransa da Birtaniya da China da Afirka ta Kudu da Jamus da Tanzaniya da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A Janairun 2025, Tinubu ya halarci taron shugabannin ƙasashen Afirka kan makamashi wanda aka yi a birnin Dar es Salaam na ƙasar Tanzaniya.

Haka ma a watan na Janairun na 2025, ya halarci bikin rantsar da shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama a birnin Accra.

A Mayun 2025, ya yi tafiya zuwa birnin Roma na ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da Fafaroma Leo XIV.

A tsakanin Yuni da Julin 2025, ya kai ziyarar aiki a ƙasar Saint Lucia, domin ƙarfafa alaƙa tsakanin Najeriya da ƙasashen yankin Karebiya.

A tsakanin Yuni zuwa Yulin 2025, ya kuma je ƙasar Brazil domin yauƙaƙa alaƙar kasuwanci da noma.

A watan Agustan 2025, ya yada zango a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, sa'ilin da yake kan hanyar zuwa ƙasar Japan.

A watan Agustan 2025, ya halarci taron ƙasashen duniya na Tokyo kan bunƙasa ƙasashen Afirka wanda ya gudana a birnin Yokohama na ƙasar Japan.

A watan Agustan 2025, ya sake komawa Brazil a karo na biyu a ziyarar aiki domin ƙulla yarjeniyoyin haɓɓaka harkokin noma da sufurin jiragen sama.

'Kasuwanci da Diplomasiyya'

Fadar shugaban ƙasar dai tana bayyana dalilan diplomasiyya da hulɗar kasuwanci alokacin tafiye-tafiyen nasa.

A wasu lokutan fadar kan ce Tinubu ya yi tafiyar ne da nufin halartar wasu manyan taukan ƙasashen duniya, da za su taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci ta hanyar ƙulla yarjejeniyoyi.

Sai dai wasu ƴan ƙasar kan soki tafiye-tafiyen da cewa ba su da amfani, in ban da ɓarnatar da kuɗin ƙasar.

Tafiye-tafiye wasu tsofaffin shugabanni

Wasu ƴan Najeriya na ganin cewa nan gaba kaɗan Bola Tinubu zai zama shugaban Najeriya da ya fi kowanne yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen ƙetare.

Amma bari mu duba mu ga yawan tafiye-tafiyen tsofaffin shugabannin Najeriya kamar Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da kuma Olusegun Obasanjo.

Ya zuwa watan Mayun 2023 an tabbatar da cewa tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari ya yi tafiye-tafiye na aiki a hukumance sau 53 cikin shekara takwas na mulkinsa, sai dai ya fi shafe kwanaki da dama a ƙasashen waje wurin neman magani.

A lokacin mulkinsa, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tafiye-tafiye da dama, duk da cewa ya yi alƙwarin rage irin waɗannan tafiye-tafiye da shugabannin Najeriya ke yi.

Bayanai sun nuna cewa Jonathan ya yi tafiye-tafiye sau 20 cikin wata 11 a shekara ta 2012.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi tafiye-tafiye sau 97 sa'ilin mulkinsa na shekara takwas tsakanin 1999 zuwa 2007.

Obasanjo ya ce ya riƙa yin tafiye-tafiye ne domin gyara sunan Najeriya a idon duniya.