Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa ya fi yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje tsakanin Tinubu da Buhari?
Tun lokacin da William Ruto na Kenya da Bola Tinubu na Najeriya suka zama shugabanni a ƙasashensu ne suke fuskantar suka kan tafiye-tafiyen da suke yi zuwa ƙasashen waje.
Masu suka sun faɗi munanan kalamai kan shugabannin, inda suke kwantanta kuɗin da suke kashewa wajen tafiye-tafiyen da kuma hali na matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasashen su a matsayin almubazzaranci.
A Kenya, wata jaridar ƙasar mai suna 'The Standard' ta yi wa Ruto laƙabi da "shugaban ƙasa mai tashi sama" saboda yawan son tafiye-tafiye da zirga-zirga da jiragen sama. Duk da matsalolin cikin gida kamar tsadar rayuwa, Ruto da alama ba ya barin duk wata dama ta tafiya ta wuce shi.
Haka nan, tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi ciki har da ziyarar da ya kai Turai a baya-bayan nan, sun tayar da ƙura, inda madugun ƴan'adawar ƙasar Atiku Abubakar ya soki yawan tafiye-tafiyen da shugaban ke yi "yayin da Najeriya ke fama da matsalar rashin tsaro da na tattalin arziƙi."
Yayin da halartar tarukan ƙasashen duniya da inganta hulɗa da ƙasashen waje ke da matuƙar muhimmanci ga shugabanni, masu sukar lamirin sun ce tafiye-tafiyen da suka wuce kima na iya karkatar da hankali daga matsalolin cikin gida.
Wannan yana da mahimmanci ba kawai domin dalilai na diflomasiyya ba, har ma da na tattalin arziƙi, saboda ana iya yin shawarwarin sanya hannun jari mai riba.
Masu sukar sun yi nuni da marigayi shugaban ƙasar Tanzaniya John Magufuli, wanda musamman ya ƙaurace wa tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Afirka a lokacin mulkinsa.
'Jin daɗi na ƙashin kai'
Farfesa Macharia Mune mai sharhi ne kan manufofin ketare na Kenya ya ce ya fahimci cewa yayin da wasu tafiye-tafiyen ke da mahimmanci, wasu kuwa babu shakka asara ce. A cewarsa, wasu shugabannin ƙasar na yin tafiye-tafiyen da ba dole ba ne domin jin daɗin kansu maimakon amfanin ƙasar.
Ruto da Tinubu, tare da masu magana da yawunsu, sun kare tafiye-tafiyen nasu, inda suka bayyana cewa suna da matukar muhimmanci wajen tunkarar matsalolin da ake zargin su da sakaci.
A cikin watanni takwas da hawan sa mulki, Tinubu ya yi tafiye-tafiye 14, wanda ya kai kimanin sau biyu a wata ɗaya. Wannan karamin abu ne idan aka kwatanta da tafiye-tafiyen Ruto, wanda ya yi tafiye-tafiye kusan 50 zuwa ƙasashen waje tun bayan da ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar a shekarar 2022, inda ya kai kimanin fiye da uku a wata ɗaya.
Shugaba Uhuru Kenyatta wanda ya gaji Ruto, yakan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje ne kimanin sau ɗaya a duk wata a tsawon shekaru goma, kwatankwacin na tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Duk da haka, dangane da jimillar kwanakin da suka kwashe a ƙasashen waje, bambancin ba shi da yawa.
Sauran shugabannin duniya ma suna yawan tafiye-tafiye ta jirgin sama zuwa sauran ƙasashe, amma Ruto da Tinubu na ci gaba da fuskantar bincike kan wajibcin kowace tafiyar tasu.
Shugabannin Najeriya da na Kenya duka sun yi tafiya zuwa Turai a karshen watan da ya gabata inda Ruto ya halarci taron ƙasashen Afirka da Italiya yayin da shi kuma Tinubu ya ci gaba da “ziyara ta ƙashin-kai” da ba a bayyana ba a Faransa, ziyararsa ta uku ke nan a ƙasar tun watan Mayun da ya gabata.
Tun daga wannan lokacin kuma Ruto ya kasance ya ƙara yin wasu tafiye-tafiye.
A watan Yunin 2023, makonni uku kacal da hawansa mulki, Mista Tinubu ya tafi birnin Paris domin wani taro na sauyin yanayi na kwanaki biyu.
Dama Tinubun ya je ƙasar a watannin baya "don hutawa" da kuma tsara yadda zai karɓi mulki bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Daga birnin Paris, Tinubu ya tafi Birtaniya domin tattaunawa ta sirri da magabacinsa kafin ya halarci taron ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas a Guinea-Bissau, sannan kuma ya tafi Nairobi.
A watan Agusta, ya ziyarci Benin, kuma a watan Satumba ya tafi Indiya da Haɗadɗiyar Daular Larabawa, da Amurka don taron Majalisar Ɗinkin Duniya kafin ya koma Paris.
Bayan wata ɗaya a gida, a watan Oktoba, ya sake tafiya zuwa Saudiyya, sai Guinea-Bissau da Jamus a ƙarshen watan Nuwamba, kuma bayan mako guda, ya tafi Dubai.
Fadar shugaban Najeriya dai ta kare waɗannan tafiye-tafiye, inda ta bayyana cewa suna da matukar muhimmanci wajen janyo masu hannun jarin ƙasashen waje.
“A duk wata ziyarar da na fara zuwa ƙasashen waje, saƙona ga masu zuba jari da sauran ‘yan kasuwa iri daya ne: Najeriya a shirye take kuma a bude take don kasuwanci,” in ji Shugaba Tinubu a sakonsa na sabuwar shekara ta 2024.
Jadawalin tafiye-tafiyen shugaban Keya, Ruto tun bayan rantsar da shi a shekarar 2022 ya fi tsanani.
A tsakanin watan Satumba na waccan shekarar zuwa Disambar da ya gabata, ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje aƙalla sau biyu a kowane wata.
A cikin watan Mayun 2023 kaɗai, ya yi tafiye-tafiye biyar, inda ya ziyarci ƙasashen Afirka daban-daban da suka haɗa da Turai da Amurka don al'amuran duniya da tarukan ƙasashen biyu.
A cikin watan Janairu, Mista Ruto ya ziyarci ƙasashen Uganda, da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, da Italiya.
Bugu da ƙari, ya riga ya yi tafiya zuwa Japan da UAE a wannan watan.
Yawaitar waɗannan tafiye-tafiye na haifar da tambayoyi, haka ma a kan kuɗaɗen da suke kashewa a tafiye-tafiyen.
Rahotanni sun bayyana cewa, Tinubu ya kashe aƙalla Naira biliyan 3.4, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 2.2 wajen tafiye-tafiyen gida da waje a cikin watanni shida na farkon mulkinsa, wanda ya zarce adadin kasafin kuɗin tafiya da aka cire na shekarar 2023 da kaso 36.
Hakazalika, a ƙasar Kenya, an samu ƙaruwar kuɗaɗen tafiye-tafiye a ofishin shugaban ƙasar, wanda ya kai sama da shilin ƙasar Kenya biliyan 1.3 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 9.2 a shekarar da ta gabata, wanda ya zarce kasafin tafiye-tafiye na shekarar da ta gabata da fiye da kashi 30 cikin ɗari.
Duk da irin tambayoyin da aka yi, kakakin gwamnatin Kenya bai yi magana kai-tsaye ba game da tafiye-tafiyensa. Sai dai Mista Ruto ya kare tafiye-tafiyen nasa, inda ya bayyana cewa, ba tafiye-tafiyen shakatawa ba ne, amma ya zama dole domin jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma samar da ayyukan yi ga 'yan Kenya a ƙasashen ketare.
Ya yi iƙirarin samun sama da ayyuka 300,000 ta hanyar tattaunawa yayin tafiye-tafiyensa, gami da yarjejeniyoyin sama da dala biliyan 2.3 bayan ziyarar da ya kai Japan kwanan nan.
Ƙasashen Najeriya da Kenya dai sun ɗauki matakin magance sukar da ake yi wa ma'aikatan gwamnati da ke yawan fita ƙasashen waje, tare da jaddada alfanun tafiye-tafiyen shugaban ƙasa.
Kenya ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kasafin tafiye tafiye na ma'aikatanta, biyo bayan tuhumar da ake yi mata na "ɓarna da ƙudin ƙasa" ko da yake shugaban ƙasar da kansa ya ce zai ci gaba da tafiye-tafiyen da ake ganin akwai amfani.
Hakazalika, a baya-bayan nan ne shugaban Najeriya ya sanar da rage tafiye-tafiye zuwa kashi 60 cikin 100.
Umarnin da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya sanar ya haɗa da mukarrabansa, amma har yanzu babu tabbas ko hakan zai haifar da ƙarancin tafiye-tafiye.
Amma kuma, damuwa game da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tafiye-tafiye bai shafi waɗannan ƙasashen biyu kaɗai ba.
A Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kwango, Shugaba Félix Tshisekedi ya fuskanci suka kan tafiye-tafiyen da ya yi ba tare da wani sakamako mai ma'ana ba, musamman a lokacin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓe.
Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya dakatar da tafiye-tafiyensa zuwa ƙasashen waje ga kansa da ministocinsa a watan Nuwamban da ya gabata saboda kalubalen tattalin arzikin ƙasar.
Sauran ƙasashen da suka haɗa da Uganda da Gambia da Namibia da Saliyo, su ma sun yi maganin kashe kuɗaɗen da jami'an gwamnati ke kashewa wajen tafiye-tafiye.
Jaridun ƙasar sun yi wa shugabanni a Namibiya da Saliyo lakabi da "shugaban ƙasa mai tashi", inda suka yi ta sukar Ruto na Kenya.