Falalar azumin ranar Arfa

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Alhamis 9 ga watan Dhul Hajji, 1446 ne al'ummar Musulmi kimanin miliyan biyu za su yi hawan Arfa - ɗaya daga cikin ayyukan wajibi na aikin Hajji a Musulunci.
Ga waɗanda suke gida ba su samu damar halartar aikin Hajji ba, akwai wasu abubuwa da za su iya yi domin samun alfarmar wannan rana kuma ɗaya daga ciki shi ne azumin ranar ta Arfa.
Azumin ranar Arfa na ɗaya daga cikin muhimman abubuwa da malamai ke ci gaba da kwaɗaitar da al'ummar Musulmi dangane da falalar kwanaki goman farko na watan Dhul Hijjah.
Malamai na cewa babu wata rana mai falalar ranar Arfa kamar yadda babu wani wata mai falalar watan Ramadan.
'Azumin ranar Arfa na kankare zunubai'
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a wata tattaunawa da BBC ya ce azumin ranar Arfa bisa hadisin annabi na janyo a yi wa mutum gafara.
"Hadisi ya zo cewa azumin ranar Arfa yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da kuma wacce za ta zo." In ji Sheikh Aminu Daurawa.
Shi ma Sheikh Ibrahim Mansur Kaduna, malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna ya ƙara da cewa azumi ranar Arfa na da matuƙar muhimmanci saboda haka rana ce da ake son ibada irin ta azumi.
"Waɗanda suke Arafat ba sa azumi amma mu na gida ana kwaɗaitar da mu da mu yi azumi a ranar."
Farfesa Ibrahim Maƙari, limamin babban masallcin Abuja, ya ce babu wata ibada da aka keɓe ga wanda bai je aikin Hajji ba illa azumi.
"A wani hadisi na annabi ya ce ba a taɓa ganin ranar da Shaiɗan ya wulaƙanta ba irin ranar Arfa. Sannan annabi a ingantaccen hadisi ya ce ana yafe wa duk mutumin da ya azuminci ranar Arfa zunubansa da ya yi."
Dangane da mata masu haila a ranar Arfa, farfesa Maƙari ya ce "macen da ke da niyyar yin azumin Arfa amma kuma sai al'ada ta same ta to Allah zai ba ta lada kwatankwacin na mai azumi domin Allah ya sa niyyarta."










