Wasa biyu kacal Barca ta ci a La Liga tun bayan ragargazar Real 4-0

Asalin hoton, Getty Images
Nasarar da Atletico Madrid ta yi a kan Barcelona ranar Asabar ta rikito da ƙungiyar ta Camp Nou daga mataki na ɗaya a teburin gasar ta La Liga.
Alexander Sorloth na Atletico ne ya taso daga benci kuma ya ci mata ƙwallon nasara bayan minti shida da cikar lokaci.
Tun da farko, Barca ce ta fara cin ƙwallo ta ƙafar Pedri minti 30 da fara wasa, amma Rodrigo De Paul ya farke ta daidai minti na 60.
Da wannan sakamako, wasa biyu kacal kenan Barca ta ci cikin takwas da ta buga a a La Liga jere - tun bayan ragargazar da ta yi wa Real 4-0 a wasan Clasico na hamayya a watan Oktoba.
A ranar Lahadi kuma, Kylian Mbappe na cikin 'yanwasan da suka taimaka wa Real Madrid doke Sevilla domin neman ɗarewa saman teburin gasar ta La Liga.
Ƙwallon da Mbappe ya ci minti 10 da fara wasa, da wadda Federico Valverde ya ci minti 10 bayan haka, da wadda Rodrygo ya ci minti 13 bayan haka, su ne suka fara bai wa Madrid tun kafin hutun rabin lokaci.
Minti 13 da dawowa ne kuma Brahim Diaz ya ci ta huɗu a filin wasa na Santiago Bernabéu.
Sai dai tun a minti 34 Isaac Romero ya farke wa Sevilla ƙwallo ɗaya, amma sai saura minti biyar a tashi daga wasan D. Lukébakio ya ƙara zare ɗaya.
A wasan ne kuma tairaron ɗanwasan Sevilla, Jesus Navas mai shekara 39 ya taso daga benci domin buga wasansa na ƙarshe, inda zai yi ritaya bayan shafe shekara 20 a kulbo ɗin. Zai jingine takalmansa a tsakiyar kaka ne saboda raunin da yake fama da shi a ƙugunsa.
Ɗanwasan Sifaniyan shi kaɗai ne ɗan ƙwallo a tarihi da ya taɓa lashe Kofin Duniya da European Championship da Uefa Nations League a tarihi. Ya buga wa Sevilla wasa 705.
Nasarar da ta samu kan Sevila ta 19 cikin wasa 20 da ta buga a gida tare da Sevilla, ta bai wa Real ɗin damar hayewa saman Barcelona zuwa mataki na biyu a teburi, da kwantan wasa ɗaya a hannu.
Yanzu Atletico Madrid ce ta ɗaya da maki 41 (da kwantan wasa ɗaya), maki ɗaya kenan tsakaninta da Real ɗin, sai Barca ta uku da maki 38.











