Yadda Najeriya ta zama sahun gaba wajen masu aikata laifi ta intanet da aka kama a faɗin Afirka

Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar 'yan sandan ƙasa da ƙasa Interpol ta ce ta kama mutum sama da 300 bisa zargin aikata laifuka ta intanet.

Interpol ta ce ta samu nasarar kama mutane ne a samame daba-daban da ta kai ƙasashen Afirka bakwai - inda jimillar mutanen suka kai 306.

A cewar Interpol, ta gano mutum sama da 1,500 da aka damfara, musamman waɗanda ke mu'amala da banki ta intanet da kuma manhajojin aika sakonni.

"Kama mutanen na cikin wani samame mai suna Red Card, wanda muka fara daga Nuwamban 2024 zuwa Fabrairun 2025, da zimmar daƙile masu aikata laifuka a kan iyaka da suka addabi mutane da kuma kasuwancinsu"

"Hukumomi a waɗannan ƙasashe bakwai sun kama waɗanda ake zargi su 306 da kuma ƙwace na'urori 1,842 a samamen na ƙasa da ƙasa da ya mayar da hankali kan masu aikata laifuka ta intanet."

Ƙasashen bakwai da aka kai samamen sun haɗa da Benin da Côte d'Ivoire da Najeriya da Rwanda da Afirka Ta Kudu da Togo da kuma Zambiya.

Ƙasashen sun haɗa gwiwa wajen bai wa ƴan sandan Interpol bayanan sirri da kuma yanda ɓata-garin ke aikata laifuka, abin da ya kai ga kama su.

Najeriya ce a sahun gaba wajen yawan waɗanda ake zargi da aikata laifuka da aka kama, inda Rwanda da Afirka ta Kudu da kuma Zambiya ke biye mata.

Ƙasashe da kuma alkaluman waɗanda ake zargi da laifi da Interpol ta kama

Najeriya

Ga Najeriya, Interpol ta tabbatar da kama mutum 130 da suka kunshi ƴan ƙasashen waje 113 - waɗanda ake zargi da aikata laifuka ta intanet da kuma zamba a ɓangaren zuba jari.

Idan za a iya tunawa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta fitar da bayanai na yanda ta kama wasu gungun masu aikata laifi da ke zamba ta intanet, inda turawa suka fi yawa - waɗanda aka fi sani da ƴan 'yahoo yahoo a ƙasar.

EFCC ta ce ta kama mutanen ne a watan Disamban 2024, inda ta kuma gano cewa ƴan ƙasashen wajen na horar da matasa ƴan Najeriya da kuma ɗaukarsu aiki da ba su kwamfutoci da wayoyi domin su shiga harkar ta zamba. Har ta kai suna buɗe musu shafuka a kafofin sada zumunta waɗanda za su yi amfani da shi wajen aikata duk wata harkar zambar intanet - kama daga soyayyar karya da yaudara don zuba-jari da kuma zambar kuɗaɗen intanet.

A cewar ƴan sandan na ƙasa da ƙasa, "Ƴan sandan Najeriya sun kama mutum 130, ciki har da ƴan ƙasashen waje 113, bisa zargin hannu a laifukan zamba ta intanet da ya danganci damfarar zuba-jari da sauransu.

Interpol ta ce waɗanda ake zargin na ɗaukar mutane aiki daga ƙasashe da dama - inda za su iya yin aikinsu na zamba.

"Hukumomin Najeriya sun gano cewa wasu daga cikin mutanen da ke yin zambar ta intanet, za su iya kasancewa waɗanda aka yi safararsu da kuma aka tilasta musu shiga harkar," in ji Interpol.

Sun ƙara da cewa bincikensu ya kai ga ƙwato ababen hawa 26 da gidaje 16 da filaye 39 da kuma na'urori 685 a Najeriya.

Rwanda

Hukumomin Rwanda sun kama mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifi su 45 waɗanda ke da hannu a zamba ta intanet da dama, abin da kuma ya kai ga ƙwato dubban daloli yayin samamen Interpol.

A cewar ƴan sandan, hukumomin na Rwanda sun kama mutanen ne bayan da suka damfari mutane sama da dala 305,000 a 2024 kaɗai.

Mutanen suna sajewa a matsayin ma'aikatan kamfanonin sadarwa, inda suke karɓan muhimman bayanai da zai ba su damar shiga wayar mutum da kuma asusun bankinsa," in ji Interpol.

"Wata hanya da suke bi ita ce yin shigar mara lafiya don neman taimako don biyan kuɗin asibiti," in ji ƴan sandan Interpol.

Sun bayyana cewa sun ƙwato kusan dala 103,043 da kuma na'urori 292.

Afirka ta Kudu

A Afirka ta Kudu, Interpol ta tabbatar da kama waɗanda ake zargi guda 40 - waɗanda suka kware wajen sauya kiran waya na ƙasa da ƙasa zuwa na cikin gida domin samun damar aikata laifi.

Ƴan sandan sun kuma ce sun ƙwace layukan waya 1,000 wanda mutanen ke amfani da shi wajen aikata ɓarna.

"Mun kuma samu nasarar ƙwace kwamfutoci 53 da kuma wasu na'urori da masu aikata laifin ke amfani da su don yin zamba," in ji Interpol.

Zambiya

A can Zambiya, ƴan sandan ƙasa da ƙasa sun kama mutum 14, waɗanda ake zargi da kutse cikin wayoyin mutane.

Waɗanda ake zargin suna kuma aika sakonnin karya wa mutane - idan suka buɗe sakonnin a wayoyinsu, to daga nan za a iya ɗebe bayanani da ke ciki.

"Idan suka damu damar kutsawa cikin wayoyin mutane, suna ɗebe musu kuɗaɗe a asusun banki," in ji Interpol.

Interpol ta ƙara da cewa masu aikata laifin na iya amfani da mahajar tura sakonni na wayar mutum wajen yaɗa sakonninsu zuwa sauran mutane.