Abin da ya sa Sri Lanka ke cikin matsin tattalin arziki

masu zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Firaministan Sri Lanka, Ranil Wickremesinghe, ya fada wa sojojin kasar cewa su yi ''dukkan mai yiwuwa domin dawo da doka da oda'', bayan da masu zanga-zanga suka mamaye ofishinsa.

An ayyana dokar ta-baci a fadin kasar bayan tserewa daga kasar da Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya yi.

Barin sa kasar ya biyo bayan gagarumar zanga-zanga ta watanni kan karuwar matsin tattalin arziki da tsibirin ke fuskanta.

Me ke faruwa a Sri Lanka?

Zanga-zangar dai ta fara ne a farkon watan Afrilu daga Colombo babban birnin kasar, inda daga baya ta rikide ta koma gagaruma, ta kuma watsu a fadin kasar.

A tsawon watanni, mutane sun shiga matsin rayuwa saboda rashin wutar lantarki da sauran ababen more rayuwa kamar man fetur da abinci da kuma magani.

Farashin kayayyaki ma ya tashi zuwa sama da kashi 50 cikin dari.

A yanzu, kasar ba ta da isasshen man fetur da zai wadace ta tafiyar da ababen hawa kamar motocin bas da jiragen kasa da kuma motocin daukar marasa lafiya.

Jami'ai sun ce kasar ba ta da isassun kudaden waje domin shigo da kayayyaki.

An samu karuwar kudin man fetur da dizel tun soma wannan shekara.

A karshen watan Yuni, gwamnatin kasar ta haramta sayar da man fetur da dizel ga wadanda ba ayyuka na musamman suke yi ba na tsawon makonni biyu.

An hakikance cewa ita ce kasa ta farko da ta taba yin haka tun shekarun 1970. An takaita sayar da man fetur a fadin kasar.

An rufe makarantu sannan an bukaci ma'aikata su yi aiki daga gida domin taimakawa wajen adana ragowar man fetur din da kasar ke da shi.

A watan Mayu, kasar Sri Lanka ta kasa biyan kudin ruwa a kan bashin da ake bin ta a waje a karon farko a tarihi.

An bai wa kasar kwanaki 30 don nemo $78m don biyan kudin ruwa, amma gwamnan babban bankin kasar P Nandalal Weerasinghe ya ce ba za ta iya biya ba.

Abin da kasar ke yi domin shawo kan matsin tattalin arziki?

Shugaba Rajapaksa ya yi alkawarin sauka daga kan madafun iko bayan da masu zanga-zanga suka mamaye gidansa, amma sai da ya ja kafa kafin ya mika takardar yin murabus dinsa.

Shugaban ya nada Firaminista Ranil Wickremesinghe a matsayin shugaban riko.

Mr Wickremesinghe ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar da kuma sanya dokar takaita zirga-zirga a lardin yammacin kasar a kokari da yake yi domin daidaita al'amura.

Sai dai a ranar Laraba, daruruwan masu zanga-zanga suka mamaye ofishin Firaministan, da kuma kiraye-kirayen ya sauka.

masu zanga-zanga

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tserewar shugaban na kuma barazana ga rikicin mulki a Sri Lanka, da ke bukatar gwamnati mai aiki tukuru domin shawo kan rikicin tattalin arziki.

Kasashen waje na bin Sri Lanka bashin sama da dala biliyan 51, hade da dala biliyan 6.5 daga China, inda tuni ma Chinan ta fara tattaunawa domin gyara yanayin bashi da take bayarwa.

Kungiyar kasashen G7 da ta hada Canada da Faransa da Jamus da Italy da Japan da Birtaniya da kuma Amurka ta ce za ta taimaka wa Sri Lanka domin biyan bashin da ake bin ta.

Bankin Duniya ya amince ya bai wa kasar bashin dala miliyan 600, yayin da kasar India kuma ta yi alkawarin bayar da taimakon dala biliyan 1.9 ga kasar.

Asusun ba da lamuni na duniya IMF, na tattaunawa kan yiwuwar bai wa Sri Lanka bashin dala biliyan uku.

Sai dai ya ce har sai an sami gwamnati da ta tsaya da kafafunta da kuma za ta iya samun riba da kudaden shiga kafin ya bai wa kasar bashi.

Mr Wickremesinghe ya ce gwamnati za ta buga kudi domin biyan ma'aikata albashi, sai dai ya yi gargadin cewa hakan zai iya kara hauhawarar farashin kayayyaki da kuma tsadar man fetur.

Ya kuma ce za a cefanar da kamfanin jiragen saman kasar. Sri Lanka ta bukaci Rasha da Qatar da ta taimaka wajen samar mata da mai a farashi mai sauki domin rage tsadar man fetur.

Me ya jawo matsin tattalin arzikin?

protesters

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin ta dora laifin matsin tattalin arziki da kasar ta fada ciki kan annobar korona wadda ta yi wa bangaren yawon bude na kasar mummunar illa - wani wuri da take samun yawan kudin shiga daga masu zuwa yawon bude ido.

Ta ce masu yawon bude ido sun shiga fargaba kan jerin bama-bamai da suka tashi a 2019.

Sai dai masana sun dora laifi kan Shugaba Rajapaksa kan rashin tafiyar da tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

A karshe yakin basasar kasar a 2009, Sri Lanka ta zabi samar wa kasuwannin tana cikin gida da kayayyaki, maimakon kokarin farfado da kasuwannin kasashen waje.

Wannan na nufin kudin shigarta daga wasu kasashe kankani ne, inda kudin shigo da kaya cikin kasar kuma ya ci gaba da karuwa.

A yanzu, Sri Lanka na biyan dala biliyan uku wajen shigo da kayayyaki sama da kudin da take samu wajen fitar da kayayyaki, wanda hakan yasa kudaden kasashen waje suka kare a Sri Lankan.

A karshen 2019, Sri Lanka na da kudaden kasar waje dala biliyan 7.6 a ajiye, wanda ya sauka zuwa dala miliyan 250. An kuma caccaki Shugaba Rajapaksa kan kara kudin haraji a 2019, wanda ya sanya gwamnatin ta rasa kudin shigarta na shekara da ya kai sama da dala biliyan 1.4

mai dakon taki

Asalin hoton, Getty Images

Sri Lanka ta shiga matsananciyar wahala a farkon shekarar 2021 kan karancin kudaden kasar waje, inda gwamnati ta yi kokarin takaita mu'amalar kudin ta hanyar haramta shigo da taki.

Gwamnati ta fada wa manoma su yi amfani da taki da ake samu daga dabbobi a cikin gida domin ya maye gurbin wanda ake shigo da shi, wanda hakan ya jawo rashin samun amfanin gona a fadin kasar.

Sri Lanka dai na shigo da kayan abincin ta daga waje, wanda ya jawo wa kasar karancin kudaden waje.