Rikicin Sri Lanka: Su waye Rajapaksas, iyalan firaministan da ya yi murabus saboda matsin lambar ƴan ƙasa?

Shugaban Sri Lankan na yanzu Gotabaya Rajapaksa (dama) tare da dan uwansa tsohon shugaban kasa Mahinda Rajapaksa, a shekarar 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan uwan juna cikin farin ciki lokacin komai na tafiya daidai (2018): Mahinda (hagu) da Gotabaya Rajapaksa dukkansu sun taba rike mukamin shugaban kasar Sri Lanka

"Wai sunan Rajapaksa shi ne kadai ya rage a kasar?"

Wannan shi ne barkwancin da 'yan Sri Lanka ke yi wa juna: wani wakilin kasar China da ya kai ziyara kasar, ya koma cike da tarin tambayoyi da alajabin yawancin mutanen da ya hadu da su sunansu guda.

Amma ba abu ne mai sauki tuna yadda barkwancin ya fito sarari ba: iyalan Rajapaksa su ke rike da madafun ikon Sri Lanka sama da shekaru 20 da suka gabata.

Irin wannan mamaya, sam ba ta fuskantar barazana: Sri Lanka na fuskantar mummunar karayar tattalin arziki tun bayan karbar 'yanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar 1948, yawancin mutane na alakanta mummunann halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da almubazzaranci da dukiyar kasa.

Tsohon shugaban Sri Lankan Mahinda Rajapaksa

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, Mahinda Rajapaksa ya mulki kasar wa'adi har biyu daga shekarar 2005 da 2015

Tuni aka fara samun sakamako maras kyawu: ranar Litinin 9 ga watan Mayu, Fira Minista kuma tsohon shugaban kasa Mahinda Rajapaksa ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, daidai lokacin da kasar ke tsaka da zanga-zanga da ta yadu zuwa sassan kasar tun watan Afirilu da ya wuce.

Mahinda yaya ne ga shugaban kasa, Gotabaya Rajapaksa.

Tafiyar hawainiyar siyasa

Kar ka sake ka yi kuskure, hakan zai janyo matsala.

"Murabus din Mahinda Rajapaksa daga mukaminsa, ya kawo karshen mulkin mutumin Sri Lanka mafi karfin fada aji a daukacin kasar," in ji editar shafukan sada zumuntar BBC na yankin Asiya, wato Ayeshea Perera.

Tsohon shugaban kasar, ya kasance babban mutum mai karfin fada aji cikin iyalan gidansu, wadanda kuma suka mamaye siyasar Sri Lanka.

Sun kasance mutanen kudancin gundumar Hambantota, an kuma fara zabar shi a matsayin matashin dan majalisa a shekarar 1970. A shekarar 1980 kuwa Mahinda da yayan sa Chamal aka zabesu 'yan majalisa.

Yadda iyalan Rajapaksa suka mamaye siyasar Sri Lanka

Mahinda ya yi fice kan kin amincewa da cin zarafin 'yan gurguzu tsakanin shekaraun 1987 zuwa 89, a wani lamari da ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani.

A shekarar 1994, sabon shugaban Sri Lanka na lokacin Chandrika Kumaratunga ya sanar da sunan shi a matsayin ministan kwadagoe. Shekaru goma bayan nan, ya zama fira minista, a kuma shekarar 2005 kuma ya yi nasarar zama shugaban kasa da gagarumin rinjaye.

Mahinda ya mulki Sri Lanka tsahon wa'adi biyu (2005-2015). A shekarar 2009, ya kawo karshen zubda jinin da yakin basasar kasar da 'yan awaren Tamil da aka dauki shekaru 30 ana fafatawa.

Sai dai nasararsa ta zama ko oho, bayan zargin cin zarafin farar hula musamman tsirarun kabilu da mabiya addinai skamar Sinhalese Budda da suka kasance kashi 75 cikin 100 na al'ummar kasar, da kuma cin hanci da rashawa.

Sai dai tsohon shugaban kasar ya musanta wadannan zarge-zarge.

Kasuwancin 'yan gida daya

Wannan danbarwa ba ta sanya iyalan Rajapaksas sun yi ko dar ba, musamman yadda suke juya siyasar kasar yadda suka ga dama: Gotabaya ya rike babban mukami a ma'aikatar tsaron Sri Lanka saboda rawar da ya taka wajen kawo karshen yakin basasar kasar.

Dan uwansa Chamal ya yi aiki a ma'aikatar aikin noma, da ta kifaye, da noman rani, ya yin da dayan dan uwan shiBasil, ya rike mukamin ministan kudi da bunkasar tattakin arziki.

Gotabaya Rajapaksa

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, Gotabaya Rajapaksa, da dan uwansa ya gaji kujerarsa ta shugaban kasa, ya na da karfin fada aji a kawo karshen yakin basasar Sri Lanka

Yawancin zuriyar gidansu 'yan uwan hudu sun rike madafun iko da manyan mukamai a Sri Lanka, misali dan Mahinda mai suna Namal ya rike mukamin ministan wasanni, ya yin da shi kuma Yoshitha wanda har lokacin da babansa ya sauka daga mukamin fira minista ya ke rike da ikon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Sai dai, iyalan sun fuskanci koma baya a fannin siyasa a shekarar 2015, ba zato ba tsammani Mahinda ya sha kaye a zaben shugaban kasa.

Amma ya sake komawa kan karagar mulki shekaru 4 bayan nan, a wannan lokacin da Gotabaya ne kan sitiyarin motar, tsarin mulki bai wa tsohon shugaban kasar damar sake tsayawa takara ba.

Takara karkashin jam'iyyar masu ra'ayin sauyi, sabon shugaban kasar ya maida hankali akan dawo da doka da oda: bayan harin da 'yan ta'adda na kungiyar IS suka kai da ya hallaka mutane 250.

Ikirarin cin hanci da rashawa

Babu inda zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa iyalan Rajapaksa ya je, sun sake bulla a zanga-zangar baya-bayan nan kan yadda kasar ta tafiyar da barkewar cutar korona da tattalin arziki.

Basil

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, Basil Rajapaksa ya mamaye muhimman ma'aikatun gwamnati, na baya-bayan nan shi ne ministan kudi

"Yawancin mutane sun yi amanna Mahinda Rajapaksa ya sharewa 'yan uwansu hanyar yin arziki ta amfani da son kai," Ayeshea Perera ta kara.

Manyan alluna, da kalaman batancin da masu zanga-zangar ke amfani da su ya munana, inda allunan da aka "barayin kudi" sun cika titunan Sri Lanka.

'Gota ka koma gida'

Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, sun kai 'yan kasar bango, musamman wadanda suka zabi Gotabaya shi ya sa suke ihu da sunan da suke kiran shi idan ana cikin nishadi "Gota ka koma gida" an kuma rubuta hakan a alluna da dama da aka kafa a titunan kasar.

Chamal Rajapaksa

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, Mukami na karshe da Chamal Rajapaksa ya rike shi ne na ministan noma

An yi ta zanga-zangar kin jinin gwamnati, wadda ta kai har an far wa ofishin Fira Minista, da gidan shi, bayan an tarwatsa masu zanga-zangar lumana a kusa da wani wuri da aka kai musu hari.

Ba a dade ba, sai zanga-zangar lumanar ta rikide tashin hankali, inda farar hula cikin fusata suka fara kona yawancin kadarorin gwamnati da iyalan Rajapaksa ke amfani da su, ciki har da gidansu na gado da ke Hambantota.

Masu zanga-zangar sun kuma lalata makabartar zuriyar Rajapaksa inda aka binne iyaye da kakannin su. Su na zargin shugaba, Gotabaya da almubazzaranci da dukiyar kasa wajen gina katafariyar makabartar.

Duk da haka shugaban kasar, ya ce ba shi da niyyar sauka daga mukaminsa, duk da murabus din da yawancin ministocin gwamnatinsa suka yi, da daina goyon bayan gwamnati da 'yan majalisar Sri Lanka suka yi.

A ranar Juma'a 6 ga watan Mayu, Gotabaya ya ayyana dokar ta baci karo na biyu cikin wata guda, bayan yajin aikin da daukacin kasar suka tafi, ciki har da masu kantinann saida kayan masarufi.

Har yanzu, iyalan ba su sha kaye a rikon Sri Lanka ba,to amma fa alamu sun nuna iyalin Rajapaksa na rasa wani bangare na abin da suka gina shekara da shekaru musamman a siyasar kasar.