Mutanen da suka mutu a dogwayen layukan sayen fetur a Sri Lanka

Bayanan bidiyo, Mutanen da suka mutu a dogwayen layukan sayen fetur a Sri Lanka

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kafafen yada labaran Sri Lankan sun ce a alla mutum takwas ne suka mutu a yayin da suke jiran sayen mai a dogwayen layuka yayin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki.

Mummunan yanayin ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje da hauhawar farashi sun jawo ƙarancin fetur da magunguna da sauran abubuwan buƙatar rayuwa da ƙasar.

Enganona mai shekara 86 ta rasa ɗanta bayan da ya shafe awanni a dogon layin shan mai.

Shi ma wani mutum Chaminda Pushpa Kumara daga arewa maso yammacin Sri Lanka ya faɗi magashiyyan ya rasu a yayin da yake kan layin shan mai.

Mai magana da yawun ƴan sandan Sri Lanka Nihal Thalduwa ya shaida wa BBC cewa ƴan sanda ba sa ajiye bayanan yawan mutanen da suka mutu a layukan gidajen mai.

Ministan Kula da Tsaron Al'umma Tiran Alles ya ce ba za a iya tabbatar da cewa mutane sun mutu ne sakamakon shafe awanni a layin mai ba, don wataƙila akwai waɗanda dama suna fama da wata rashin lafiyar.