Real Madrid za ta sayar da Vinicius don sayo Haaland, Man U na son Wharton

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na neman Adam Wharton, mai shekara 21. Ana sa ran farashin dan wasan na Ingilan zai kai fan miliyan 60 (Mirror)
A halin yanzu, United ba za ta dauki kocin Ingila Thomas Tuchel a matsayin wanda zai maye gurbin Ruben Amorim ba. (Sun)
Bayern Munich ta kuduri aniyar tsawaita kwantiragin dan wasan baya Dayot Upamecano, mai shekara 26, sakamakon zawarcinsa da Liverpool ke yi, duk da cewa kulob din na Jamus ba zai iya amincewa da kara inganta albashinsa ba a watan Yunin 2026. (Florian Plettenberg)
Real Madrid na shirin siyar da dan wasan gabanta Vinicius Junior, mai shekara 25, kan kudi mafi tsada a duniya a wani yunkuri da take yi na sayan dan wasan gaban Manchester City Erling Haaland, mai shekara 25. (CaughtOffside)
Nottingham Forest na matukar sha'awar Rafael Benitez a matsayin wanda zai maye gurbin Ange Postecoglou idan suka yanke shawarar rabuwa da kocin da Australia. (Footbal Insider)
Manchester United na fuskantar hamayya daga Tottenham Hotspur wajen neman dan wasan tsakiyar Sporting Morten Hjulmand mai shekaru 26. (Fichajes)
Crystal Palace ta bayyana dan wasan West Ham United Max Kilman, mai shekara 28, a matsayin wanda zai maye gurbin Marc Guehi idan dan wasan Ingilan ya bar kungiyar a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Football Insider)
Dan wasan bayan Ingila da Manchester United Harry Maguire, mai shekara 32, zai yi watsi da duk wani tayin makudan kudi daga Saudi Arabiya idan har kungiyar ta yi masa sabon kwantiragi. (Star)
Dan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez, mai shekara 24, yana jan hankalin Real Madrid amma Blues za ta bukaci akalla fan miliyan 120 kan dan wasan wanda ya lashe kofin duniya. (Fichajes)
Roma ta Italiya, na son dan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24 a watan Janairu. (Gazetta dello Sport)
Kulob din Galatasaray na Turkiyya ne ke kan gaba wajen neman dan wasan bayan United Tyrell Malacia mai shekaru 26. (Star)










