Inter Miami na zawarcin Neymar, Real Madrid na bibiyar Guehi

Neymar Jr

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Inter Miami na nazari kan ɗaukar tsohon ɗan wasan Barcelona da Brazil Neymar, mai shekara 33, inda ta ke fatan sake haɗa shi da tsoffin abokan wasansa Lionel Messi na Argentina da Luis Suarez na Uruguay. (Mail)

Ɗan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, ya shige gaban ɗan wasan bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, a jerin ƴan wasan da Real Madrid ke neman ɗauka a bazara mai zuwa. (Fichajes)

Tottenham na daga cikin ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗan wasan gaban Brentford ɗan ƙasar Jamus Kevin Schade, mai shekara 23. (Sky Germany)

Liverpool na zawarcin ɗan wasan baya na Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, tare kuma da Marc Guehi na Crystal Palace. (Florian Plettenberg).

Juventus za ta nemi golan AC Milan Mike Maignan, mai shekara 30 wanda kwantaraginsa zai ƙare a bazara mai zuwa, amma za ta fuskanci hamayya daga Chelsea da Bayern Munich(Gazzetta dello Sport).

Ɗan wasan Levante da Kamaru Etta Eyong, mai shekara 21, ya fi son ya koma Barcelona a kan Manchester United. (Sport).

Bayern Munich na sha'awar sayen Murillo na Nottingham Forest, mai shekara 23, amma za ta buƙaci fara sayar da ƴan wasa domin samun kuɗin ɗaukar ɗan wasan na Brazil. (Bild)

Liverpool da Chelsea da Manchester United na daga cikin jerin ƙungiyoyin da ke sha'awar daukar ɗan wasan bayan RB Leipzig da Faransa Castello Lukeba, mai shekara 22, kan kuɗi Yuro miliyan 60 (Caught Offside)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tottenham na zawarcin ɗan wasan Najeriya, Sani Suleiman, mai shekara 19, bayan ta aike da wakilanta domin kallonsa a wasan da ya bugawa ƙungiyar AS Trencin ta Slovakia. (Teamtalk)

Ɗan wasan Crystal Palace Adam Wharton, mai shekara 21, ya bayyana farin cikin ci gaba da zama a filin wasan Selhurst Park kuma ɗan ƙasar Ingilan ba ya da niyyar barin ƙungiyar a watan Janairu duk da cewa Liverpool da Manchester City da Real Madrid na zawarcinsa. (Football Insider)

Newcastle na daf da ɗaukar babban jami'in kula da ƙwallon ƙafa na Nottingham Forest Ross Wilson a matsayin sabon daraktan wasanni. (Telegraph)

Newcastle na jiran a naɗa Wilson kafin ta fara tattaunawa kan sabunta kwantiragi da ɗan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali, mai shekara 25, da ɗan wasan baya na Ingila Tino Livramento, mai shekara 22, da kuma ɗan wasan baya na Holland Sven Botman mai shekara 25.

Everton ba ta kallon ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 29, a matsayin wanda take zawarci, duk da cewa David Moyes ya ɗauke shi a matsayin aro lokacin da yake jagorantar tsohuwar ƙungiyarsa ta West Ham. (Talk)