Fernandez na son ci gaba da zama a Man United, Silva da Man City za su raba gari

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Kyaftin ɗin Manchester United Bruno Fernandes, mai shekara 31, ba shi da niyyar barin ƙungiyar a watan Janairu, duk da sha'awar da ƙungiyoyin Saudiyya ke nunawa kan ɗan wasan tsakiyar na Portugal. (Talksport)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva, mai shekara 31, na shirin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta bana, inda wasu ƙungiyoyin Saudiyya da Benfica ke zawarcin ɗan wasan na Portugal. (GiveMeSport)

Ɗan wasan bayan United da Ingila Harry Maguire, mai shekara 32, na fatan rattaba hannu kan sabon kwantiragi inda yarjejeniyarsa ta yanzu a Old Trafford za ta ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Sun)

Chelsea za ta saurari tayi kan ɗan wasan gaban Ingila Tyrique George mai shekara 19 a watan Janairu (Football Insider)

West Ham da Real Sociedad da Valencia duk suna fafatawa don ɗaukar ɗan wasan gaban Real Madrid da Brazil, Endrick, mai shekara 19, aro a watan Janairu. (Estadio Deportivo)

Ƙungiyar gasar MLS Orlando City na son sayen ɗan wasan Tottenham Richarlison, mai shekara 28, a bazarar 2026 kuma har an fara tattaunawa da tawagar ɗan wasan na Brazil. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 25, yana son komawa gasar Premier a shekarar 2026kuma ɗan wasan na Serbia ya bayar da fifiko kan komawa Chelsea ko Tottenham. (TBR Football)

Manchester United ta shige gaban Liverpool a fafatukar sayen ɗan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25. (Caught Offside)