Me ya sa wasu ƴan APC ke fargabar yiwuwar ajiye Kashim Shettima?

Lokacin karatu: Minti 3

Wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan raɗe-raɗin yiwuwar ajiye mataimakin shugaban ƙasar Kashin Shetimma a zaɓe mai zuwa da ake tunanin shugaba Tinubu zai yi takara.

Wannan na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka tashi baram-baram a wajen wani taron APC na arewa maso gabas, yayin da aka ayyana shugaba Tinubu a matsayin ɗan takarar jam'iyyar ba tare da mataimakin nasa ba.

A baya-baya nan ne aka jiyo shugaba Tinubu na yi wa jam'iyyun hamayyar ƙasar shaguɓe saboda rigingimun da suke fama da su, yana mai bayyana tasa jam'iyyar ta APC a matsayin shafaffiya da mai.

Da alama dai kalaman shugaba Tinubun na zungurar jam'iyyun hamayya game da rikicin cikin gidan da suke fama da shi ya zamo irin abun nan da Hausawa kan ce kaikayi koma kan mashekiya, kamar yadda wasu jam'iyyun hamayyar ke gani.

La'akari da yadda kasa da mako guda da yin wannan magana sai ga shi an tashi dutse a hannun riga a wajen taron jam'iyyarsa ta APC a jihar Gombe yayin da aka so bayyana shi shi kadai a a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben 2027 da ke tafe, kamar yadda sugabbannin jam'iyyar ke yi a taruka da dama.

Wani abu da ya sa wasu gaggan APCn, ke ganin da walakin goro a miya.

Dr Musa Inuwa Kubo, tsohon kakin majalisar dokokin jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa suna so su tabbatarwa wadanda suke nunawa shugaban kasa cewa akwai bukatar idan zai sake komawa kan mulki to kada ya koma tare da mataimakinsa Kashim Shettima.

Ya ce," Wallahi idan aka ce haka za a yi wannan tafiya to za a haifar da babbar matsala domin hausawa na cewa rigima a kwance ta ke tayar da ita kuma akwai babbar matsala."

" Abin da ake gani ya faru a Gombe to idan aka je wani wajen sai ya fi muni, kuma duk wani aiki da ake gani shugaban kasa ya yi na azo a gani ai bashi kadai ya yi ba dole sai an sa mataimakinsa a ciki."

To sai dai a cewar jam'iyyar APC ta shugaba Tinubun wasu ne kawai ke neman tada fitina a inda babu ita, daraktan watsa labaran jam'iyyar na kasa Malam Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa kowa ya sani cewa a dokance shugaba shi ke zabar mataimakinsa.

Ya ce," Su masu nema ko son su ga an yi rigima su suke suga ana samu matsala ko matsala a jam'iyya, kuma har kawo yanzu ba a ji daga bakin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce akwai wata matsala a tsakaninsa da shugaba Tinubu ba, haka shi ma daga nasa bangaren shugaba Tinubu bai ce akwai wata matsala a tsakaninsa da mataimakin nasa ba."

Sai dai duk da kokarin kore wannan rade radi da jam'iyyar APC ke yi, masana siyasa a Najeriya kamar Farfesa Kamilu Sani Fagge, na ganin cewa babu rami babu abun da zai kawo rami.

Farfesan ya shaida wa BBC cewa akwai kanshin gaskiyar za a ajiye shi mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Ya ce," A gaskiyar magana idan har ba a ci gaba da wannan tafiya da shi mataimakin shugaban Najeriyar ba, to ko shakka babu APC za ta iya rasa yankin arewa maso gabas, musamman da ake kishin-kishin din cewa shugaba Tinubun zai dauko wanda ba musulmi ba ya yi masa mataimaki a wa'adin mulkinsa na biyu."

Farfesan ya ce," Idan har ya yi abin da ake zargi to musulmai za su ga cewa ya ajiye nasu a nan kuma idan ba a yi aune ba sai jam'iyyar APC ta rasa yankuna da dama a Najeriya."

Wannan dambarwa ta APC da ta kunno kai na faruwa ne bayan cikar shugaba Tinubu shekara biyu a kan Mulki, watau rabin wa'adin mulkinsa na farko, abin da ya sa masu suka da dama ke zargin gwamnatin da dauke hankali daga harkokin jagoranci tare da mayar da hankali kan siyasa, ko da yake fadar shugaban Najeriyar na ganin cewa bikin Magaji baya hana na Magajiya.