Shekara biyun Tinubu ne mafiya muni a tarihin dimokradiyyar Najeriya - Dalung

Lokacin karatu: Minti 3

Tsohon ministan harkokin matasa da wasannin Najeriya, Barrister Solomon Dalung ya bayyana shekara biyu da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shafe a karagar mulki da cewa marasa amfani ga talakan ƙasar.

Cikin tattaunarawa da BBC albarkacin ranar Dimokraɗiyya da cikar Najeriya shekara 26 a mulkin farar hula ba tare da katsewa ba - tsohon ministan ya ce "abin da kawai talakan Najeriya ya amfana da shi tsawon shekara biyun Tinubu shi ne ya gode Allah yana da rai".

''An samu ƙaruwar tsadar rayuwa da talauci da yunwa da wahala ta taɓarɓarewar tsaro, duka waɗannan gawurta suka yi'', in ji shi.

Solomon Dalung ya yi zargin cewa talakawan ƙasar na mutuwa saboda yunwa, da wahalar da gwamnatin Tinubu ta jefa ƙasar a ciki.

Tun bayan zuwan gwamnatin Shugaba Tinubu dai ta ɓullo da sabbin matakan tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da sabbin manufofin ɓangaren kuɗi.

Sai dai Mista Dalung ya soki gwamnatin da cewa ta cire tallafin man fetur ba tare da samar da wani cikakken tsarin da zai sauƙaƙa wa talakan ƙasar ba.

''Kuma duk da faɗa wa wahala da matakin ya jefa talakawan Najeriya, da ƴanjarida suka tambayi Tinubu, cewa ya yi bai yi nadamar cire tallafin man ba'', in ji Dalung.

Gwamnatin Tinubu dai ta sha cewa ta cire tallafin man fetur ne saboda magance sace kuɗaɗen tallafin da wasu "tsiraru" a ƙasar ke yi.

Kuma matakin "na da alheri ga tattalin arzikin Najeriya", kuma za a ga tasirinsa a nan gaba.

'Gwamnatin Tinubu ba ta talaka take ba'

Barrister Solomon Dalung ya ce ya zuwa yanzu babu wani tasiri da talakan Najeriya ya gani kan matakin cire tallafin man fetur.

''In dai ba canja jirage da motoci da gina sabon gida ga mataimakinsa ba to babu wani tasiri da muka gani (daga gwamnatin Tinubu)'', in ji Solomon Dalung.

Tsohon ministan ya ce gwamnatin Tinubu ba ta talaka take yi ba, kanta kawai ta sani.

A baya-bayan ne dai Bankin Duniya ya bayar da rahoton samun bunƙasar alƙaluman tattalin arzikin ƙasar da ba a taɓa gani da cikin shekara 10.

Sai dai Barrister Dalung ya bayyana Bakin Duniyar da kasancewa ''bakin ganga''.

''Ta yaya jiya-jiya za ku je halin tattalin razikin yana cikin matsi, yau kuma ku ce ya bunƙasa''?

''Ai dole Bankin Duniya ya yi bakin ganga, saboda a wurinsa ake ciwo bashin da ake karɓowa'', in ji shi

'Dimokraɗiyya na cikin tsaka mai wuya a Najeriya'

Tsohon ministan ya ce a cikin shekara biyun mulkin Tinubu dimokradiyya ta fuskanci barazanar da ba taɓa ganin irinta a tarihin ƙasar.

Ya zargi gwamnatin da hannu a kama wasu ƴan'adawa da ƴangwagwarmaya a ƙasar.

''Kuma yawanci an kama su ne saboda faɗar ra'ayinsu kan abin da gwamnati ke yi da bai dace ba'', in ji shi.

Haka kuma Barrister Dalung ya zargi gwamnatin Tinubu da sayen ƴan hamayya don komawa jam'iyya mai mulki.

''Cikin shekara biyun nan mun ga yadda ake sayen hamayya, suna koma jam'iyyar APC'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa Dimokraɗiyya na cikin tsaka mai wuya a Najeriya, kuma ''muna fatan za s gane cewa hakan ba alkairi ne ga ci gaban ƙasa ba'', kamar yadda ya bayyana.