Solomon Dalung: Gwamnatin jam'iyyar APC ta gaza

Tsohon ministan wasanni kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce jam'iyyar tasu ba ta damu da ta ga an magance matsalar tsaro a ƙasar ba, kamar yadda ta damu da batun sake lashe zabe a shekarar 2023.

Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC.

Barrister Solomon Dalung ya ce kamata ya yi a ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta mayar da hankalinta kan yadda za a shawo kan taɓarɓarewar tsaro, ba ta biye wa jam'iyyar APC ba da babu abin da ta sa a gaba sai batun shugabanci, a irin halin da talakawan Najeriya ke ciki.

"Dole ne mu yarda cewa akwai bukatar canza salon gudanar da abubuwa tun da ba su ɗauki saiti ba, kuma wahalhalu sai karuwa suke yi ko wace rana," in ji tsohon ministan.

Ya kuma kara da cewa "abin da gwamnatin APC ta fi damuwa da shi yanzu shi ne yadda za ta gudanar da zaɓen 2023 da yadda kuma mutane za su samu muƙamai.

''Wannan bai dace a ce shi ne abin da gwamnati ta fi mayar da hankali a kai ba," a cewar Solomon Dalung.

Ya kuma nuna damuwa irin yadda "gwamnoni da ƴan majalisa suke faɗi-tashin yadda za a gudanar da zaben cikin gida na jam'iyyar suke yi" a maimakon harkar tsaro.

Mr Dalung ya ce duk da irin kishin jam'iyyarsa da yake da shi da kuma goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da yake yi, ya zama dole su yadda cewa jam'iyyarsu ta gaza musamman a bangaren tsaron al'umma.