Ten Hag na shirin komawa gasar Premier, Madrid za ta sayar da Vinicius

Erik Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta yanke shawarar sayar da ɗanwasan gaban Brazil mai shekara 25, Vinicius Jr a ƙarshen kakar wasan bana bayan fushin da ya nuna saboda an cire shi daga karawar ƙungiyar da Barcelona. (Bild - in German)

Ɗanwasan gaban Brazil, Rodrygo na son barin Real Madrid a watan Janairu, kuma Arsenal da Tottenham na zawarcin ɗanwasan mai shekara 24. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United za ta raba gari da ɗanwasan gefen Ingila mai shekara 25, Jadon Sancho, wwanda ke zaman aro a Aston Villa, kuma a kyauta ɗanwasan zai sauya sheƙa. (Talksport)

Roma na shirin shiga cinikin ɗanwasan gaban Manchester United da Netherland mai shekara 24, Joshua Zirkzee a watan Janairu. (Calcio Mercato - in Italian)

Ɗanwasan bayan Inter Milan da Jamus mai shekara 24, Yann Bisseck, na shirin komawa taka leda a Ingila, inda West Ham da Tottenham ke bibiyar shi. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Crystal Palace da Inter Milan da kuma Juventus za su fafata wajen neman sayen ɗanwasan bayan Manchester City da Netherlands mai shekara 30, Nathan Ake a watan Janairu.

Manchester United willza ta ƙara ƙaimi wajen neman ɗanwasan tsakiyar Ingila da Nottingham Forest, Elliot Anderson a watan Janairu, kuma Red Devils ta gamsu ɗanwasan mai shekara 22 na sha'awar komawa Old Trafford. (Teamtalk)

Arsenal ba ta da aniyar sayar da ɗanwasan tsakiyar ta mai shekara 26, Martin Odegaard, duk da zawarcin shi da Barcelona ke yi. (Fichajes - in Spanish)

Ɗanwasan bayan Netherlands, Virgil van Dijk ya yi tunanin komawa Real Madrid a farkon kakar wasan bana, amma daga baya mai shekara 34 ya sanya hannu kan sabuwar kwangila da Liverpool (AS - in Spanish)

Everton ba za ta sayar da ɗanwasan bayan Ingila da aka yankewa farashin £70m, Jarrad Branthwaite a watan Janairu ba, duk da sha'awar da Manchester United ke yi wa ɗanwasan mai shekara 23. (Teamtalk)

Tsohon kocin Manchester United, Erik ten Hag na cikin waɗanda ake sa ran su zamo kocin Wolves. (ESPN)