Nijar za ta iza ƙeyar gomman ‘yan Najeriyar da suka so tsallaka Sahara

'yan ci-rani

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce sun kama wasu ‘yan Najeriya kimanin 55 da ke shirin tsallaka Sahara a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na yankin Mata-Maye, Annuri Hamidu Bohamni ya shaida wa manema labarai cewa sun kama ‘yan Najeriyar ne a cikin dajin Isharnawa.

Ya ce jami'ansu sun samu 'yan ci-ranin ne waɗanda masu fasa-ƙwaurin mutane suka jibge a wani wuri, kafin lokacin da za a tsallaka da su.

Mutanen kamar yadda babban jami'in 'yan sanda ya bayyana, galibinsu mata ne da ƙananan yara.

"Abin takaici galibinsu mata ne da ƙananan yara da suka baro Najeriya da niyyar ƙetara Sahara, sannan su ƙetara ta cikin tekun Bahar Rum zuwa ƙasashen Turai, inda suke tsammanin za su samu ingantacciyar rayuwa," in ji shi.

Ya ce mutanen su 55 sun yi niyyar tafiya Turai ne, inda za su bi ta jihar Agadez daga nan su ratsa cikin ƙasar Libya kafin su isa bakin tekun.

Wannan tafiya ce mai cike da hatsarin gaske, in ji babban ɗan sandan.

Suspected victim of human trafficking

Asalin hoton, NAPTIP/WEBSITE

Bayanan hoto, Ɗumbin 'yan Najeriya ne musamman mata da matasa, ake yaudara tare da kwaɗaita musu zuwa Turai don samun ingantacciyar rayuwa

Shi ma sakataren shugaban ma'aikatar gunduma ta Mata-Maye, Mal Bubakar Mahmud Ya’u ya ce kama 'yan ci-ranin wata nasara ce ga jami'an tsaro saboda hana su ci gaba da wannan tafiya mai cike da hatsari.

Ya kuma ce galibi irin waɗannan 'yan ci-rani, idan suka tsallaka suka bar Nijar sukan fuskanci tsangwama da cin zarafin da mafi yawa ba su taɓa ganin irinsa ba.

‘’Irin waɗannan mutane sukan fuskanci ƙyama dalilin launin fatarsu, amma ba sa ganin haka, mutanen da ke musu romon baka su tafi (Turai), ba sa faɗa musu gaskiyar abin da ke faruwa," a cewar Bubakar Ya'u.

Hukumomin 'yan sandan Mata-Maye dai sun ce za su iza ƙeyar waɗannan mutane zuwa inda suka fito cikin kwanciyar hankali.

Sai dai kuma, mataimakin kwamishinan 'yan sandan Mata-Maye ya lashi takobin kamo duk masu hannu a safarar 'yan ci-rani ta yankin da nufin gurfanar da su gaban shari'a.

Ya ce doka za ta hukunta su, ko a wacce ƙasa suke tsakanin Nijar da Najeriya, ko ma 'yan wata ƙasar ne daban.

"A duk lokacin da irin wannan abu da ya shafi ƙasashe guda biyu ko fiye, mukan kwashi mutanen mu mayar da su ƙasashen da suka fito, idan akwai hukuncin da za a yi musu, sai a yi musu a can'', in ji shi.

''Amma mutanen da suka yi safarar su, mukan tabbatar da ganin an hukunta su ko daga wacce ƙasa suka fito," a cewarsa.

Jamhuriyar Nijar dai ta zama wata hanya ga dubban 'yan ci-rani da ke shiga Sahara a yunƙurinsu na tsallaka wa zuwa ƙasar Libya don shiga ƙasashen Turai ta cikin tekun Bahar Rum.

Irin wannan tafiya mai matuƙar hatsari na ci gaba da laƙume rayukan 'yan ci-rani, waɗanda ƙasashen duniya ke ta faɗi-tashi don ganin sun daƙile ayyukan masu safarar mutanen.