MDD ta yi Allah-wadai da gano ƴan cirani 92 tsirara a iyakar Girka da Turkiyya

An image of some of the 92 men was tweeted by Greece's migration minister

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Wani hoto da ke nuna mutanen tsirara wanda minsitan kula da ƴan cirani na Girka ya wallafa a Tuwita
    • Marubuci, By Alex Binley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Hukumar Kula da Ƴan cirani ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNHCR, ta ce ta damu matuƙa da gano kusan wasu maza 100 tsirara da aka yi a tsakanin iyakar Girka da Turkiyya.

Ƙasashen biyu sun zargi juna da ƙin mayar da hankali kan ƴan ciranin 92.

Girka ta ɗora alhakin hakan a kan Turkiyya, tana mai cewa "ɗabi'ar da ta nuna abin kunya ce ga zamani."

Turkiyya ta ce ikirarin maƙwabciyar tata labarin ƙanzon kurege ne ta kuma zargi Girkan da mugunta.

A yayin da ɓangarorin biyu ke zargin juna, hukumar kula da ƴan ciranin ta yi kira da a ƙaddamar da bincike tana mai cewa ta yi matuƙar jin ɓacin rai da rahotanni da hotuna masu ɗaga hankalin da ta gani.

Ƴan sandan Girka sun ce sun ceto mutum 92 da aka gani tsirara, wasun su sun ji raunuka, a kusa da iyakarta da Turkiyya daga arew,a a ranar Juma'a.

Sun ce binciken da suka yi tare da jami'an hukumar iyakoki ta Tarayyar Turai wato Frontex, ya gano cewa ƴan ciranin sun tsallaka kogin Evros ne zuwa iyakar Girka a cikin kwale-kwalen roba daga Turkiyya.

"Ƴan sandan kan iyaka... sun gano ƴan cirani 92 babu kaya a jikinsu, wasunsu ma da raunuka a jikinsu," a cewar sanarwar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumomin Girka sun ce nan da nan aka ba su kaya suka saka, sannan aka ba su abinci da magungunan da suke buƙata.

Ba a gano dalilin da ya sa aka gan su tsirara ba.

Frontex ta ce yawanci mutanen ƴan Afghanistan da Syria ne, kuma an sanar da babban jami'in kula da hakki na ƙungiyar cewa akwai yiwuwar take hakki.

Ministan kare hakkokin mutane na Girka, Takis Theodorikakos, ya zargi Turkiyya da "assasa cirani ba bisa ƙai'da ba" a wani rikici na baya-bayan nan kan batun cirani tsakanin ƙasashen biyu.

Da yake magana a gidan talabajin na Girka, ya yi ikirarin cewa da yawan ƴan ciranin sun shaida wa Frontex cewa "wasu motocin soji na Turkiyya uku ne suka kai su wajen kogin, inda nan ne iyakar ƙasashen biyu.

BBC ba ta iya tabbatar da wannan ikirari ba. Mr Theodorikakos ya ce "Dole a tsammacin bayani a hukumance daga ɓangaren gwamnatin Turkiyya."

Kwana ɗaya kafin nan, Ministan Cirani na Girka Notis Mitarachi a wani saƙon tuwita ya ce abin da Turkiyya ta yi wa ƴan ciranin "babban abin kunya ne a zamanance."

Ya ce Girka na sa ran Turkiyya za ta yi bincike kan lamarin ta kuma "kare... iyakarta da Tarayyar Turai".

Rikicin ya kai kunnen ƙololuwa a gwamnatin Turkiyya, inda aka wallafa saƙon tuwita da sunan shugaban ƙasar ana ƙaryata batun hannun ƙasar a kan abin da ya faru, aka kuma ɗora alhakin zalintar mutane a kan Girka.

"Tsarin Girka na yaƙi da labaran ƙarya ya dawo bakin aiki," kamar yadda babban mai taimaka wa Shugaba Erdogan shawara a harkar yaɗa labarai Fahrettin Altun, ya wallafa a shafin sada zumunta.

Ya bayyana zarge-zargen a matsayin "shirme kuma abin dariya", yana zargin Girka da rashin girmama ƴan ciranin ta hanyar wallafa hotunansu.

A martaninta, UNHCR ta ce ta shiga matuƙar damuwa bayan samun rahoton da hotunan masu ɗaga hankali, amma har yanzu ba ta kai ga yi wa ƙungiyar magana kai tsaye ba - sai dai tana fatan yin hakan nan da ƴan kwanaki.

"Mun yi Allah-wadai da duk wata mugunta da ƙasƙantarwar tare da yin kira ga aiwatar da cikakken bincike," kamar yadda UNHCR ta shaida wa BBC.

An gano mutanen ne kwanaki kaɗan bayan ɓullar wani rahoto da hukumar ta EU da ke zargin wasu manyan jami'an Frontex da mayar da kakkausan martani kan yadda Girka da Turkiyya suke yi wa ƴan cirani, sai dai Girkan ta musanta hakan.

A watan da ya gabata, shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zargi Girka a wajen taron MDD kan mayar da kogin Aegea maƙabarta, ta kuma ce Girkan na da tsauraran tsare-tsare kan batun cirani.

Girka na gaba-gaba a cikin ƙsashen da suka fi fama da matsalar ƴan cirani a 2015 da 2016, lokacin da kusan ƴan cirani miliyan ɗaya da suka tsere wa yaƙi da talauci a Syria da Iraki da Afghanistan suka isa ƙasar, yawanci ta Turkiyya.

Tun daga lokacin yawan ƴan ciranin ya ragu, amma hukumomin Girka sun ce a baya-bayan nan ma an samu ƙaruwar masu ƙoƙarin shiga ƙasar ta iyakar Turkiyya da tsibiran Girka.

Girka ta nemi Turkiyya da ta girmama yarjejeniyar 2016 da aka cimma da Tarayyar Turai a inda Ankara ta amince ta shawo kan tururuwar ƴan cirani cikin Turai bayan ba ta biliyoyin yuro a mtsayin na tallafi.

Girka za ta faɗaɗa katangarta daga arewacin iyakarta da Turkiyya don kare kwararar ƴan ciranin ƙasar, in ji Mr Theodorikakos