Arsenal za ta ɗauki Martinez, City da Real za su yi rige-rige kan Hernandez

Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na son ɗaukar ɗan wasan Inter Milan, Lautaro Martinez, Manchester City na fatan sayen mai tsare baya, Chelsea za ta bai wa Andrey Santos dama a kakar baɗi.

Arsenal na shirin sayen ɗan wasan Inter Milan kan £100m Lautaro Martinez, (Fichajes)

Har yanzu ɗan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko, shi ne kan gaba da Arsenal ke fatan saya a karshen kakar nan. (Independent),

Arsenal ta tattaunawa da wakilan dan ƙwallon AC Milan, Alvaro Morata a makon jiya tun kan ya amince ya koma buga wasannin aro a Galatasaray. (Athletic)

Manchester City da Real Madrid za suyi rige-rigen sayen ɗan wasan AC Milan, Theo Hernandez, da zarar kowacce ta kasa ɗaukar ɗan wasan Juventus, Andrea Cambiaso. (Teamtalk)

Napoli ta hakura da zawarcin ɗan ƙwallon Manchester United, Alejandro Garnacho, saboda albashinsa yana da yawa. (Fabrizio Romano)

Za a rage kuɗin kunshin yarjejeniyar mai taka leda a Bayern Munich, Harry Kane, idan ƙungiya za ta saye shi yarjejeniyarsa ba ta kare ba daga £67m zuwa £54m a kakar baɗi. (BILD)

Kociyan Chelsea, Enzo Maresca na shirin amfani da matashin ɗan wasa mai shekara 20 a kaka mai zuwa, Andrey Santos - wanda ke wasannin aro a Strasbourg. (Fabrizio Romano)

Arsenal za ta yi kokarin sayen mai tsaron raga, Joan Garcia daga Espanyol a karshen kakar nan. (Athletic)

Kadan ya rage ɗan wasan Manchester United, Tyrell Malaciaya koma Wolves a ranar rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo, domin zuwa PSV Eindhoven. (Voetbal Verslaafd)

Ɗaya daga ƴan wasa huɗu da Manchester City ta ɗauka a Janairu ba zai buga mata Champions League a wasan cike gurbi da Real Madrid - dokar Uefa ta amince ka kara ƴan ƙwallo uku sabbi da ka saya daga waɗanda ke buga maka gasar a zagaye na biyu. (ESPN)