Newcastle ta yi waje da Arsenal daga Carabao Cup

Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle ta kai zagayen karshe a Carabao Cup na bana, bayan da ta doke Arsenal 2-0 a St James' Park a wasa na biyu da suka kara ranar Laraba.

Kenan Newcastle ta yi waje da Gunners a kofin bana da cin 4-0 gida da waje a karawa biyun da suka yi.

A wasan farko zagayen daf da karshe da aka yi a Emirates cikin Janairu, Newcastle ce ta ci 2-0, inda Alexander Isak da kuma Anthony Gordon suka ci mata ƙwallaye.

Minti na 19 da fara wasa ne Neewcastle ta jefa ƙwallo a ragar Gunners ta hannun Jacob Murphy, haka suka je hutu ana cin Arsenal 1-0.

Kenan Murphy ya ci ƙwallo biyar a dukkan fafatawa a kakar nan - yana da hannu a zura 14 a raga a kakar nan bayan biyar da ya ci ya kuma bayar da tara aka zura a raga.

Kakar da ya ci ƙwallaye da yawa ita ce 2016/17 lokacin da yake Norwich, wanda ya ci 10 ya bayar da shida aka zura a raga.

Wannan shi ne wasa na uku da suka kece raini a tsakaninsu a kakar nan, bayan da aka ci Gunners 1-0 cikin Nuwambar 2024 a St James's Park a Premier League.

Arsenal ta yi ban kwana da FA Cup a kakar nan, wanda Manchester United ta fitar da ita da kuma Carabao Cup.

Kofin da ke gaban Arsenal ya rage na Premier League, wanda take ta biyu a teburi, kuma kaka 21 rabonda ta lashe kofin.

Haka kuma Gunners ta kai zagaye na biyu kai tsaye a Champions League, kofin da ba ta taɓa ɗauka ba.

Wannan koma baya ne ga kociyan Arsenal, Mikel Arteta, wanda FA Cup kaɗai ya ɗauka a Gunners a 2020 lokacin korona tun bayan da ya karbi aikin.

Ranar Lahadi 18 ga watan Mayu Arsenal za ta karɓi bakuncin Newcastle a Emirates a Premier League, wasa na huɗu da za su kara a tsakaninsu a bana.

Da wannan sakamakon Arsenal za ta je Leicester City, domin buga Premier League ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu a wasan gaba.

Daga nan Gunners za ta karɓi bakuncin West Ham a karawar hamayya ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu a Emirates.

Ita kuwa Newcastle za ta je Birmingham ranar Asabar 8 ga watan Fabrairu a FA Cup daga nan ta je Manchester City a Premier League ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu.