Hankalin kasashen duniya ya karkata kan harin Poland

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Poland ta yi kira ga al'ummarta da su kwantar da hankalinsu, bayan da mutum biyu suka rasa rayukansu sanadin fadawar wani makami mai linzami a wani kauye da ke kusa da kan iyakar kasar da Ukraine.
Shugaba Andrzej Duda ya ce makami ne da aka kera a Rasha amma babu cikakken bayani a kan wanda ya harba shi.
Shugaba Duda ya fada wa ‘yan jarida cewa : ”Ba mu da wata kwakkwarar shaida ya zuwa yanzu a kan wanda ya harbo makamin….akwai yuwar cewa makami ne da aka kera a Rasha amma wani abu ne da ake gudanar da bincike a kansa a halin yanzu.”
Firaministan Poland Mateusz Morawiecki ya ce gwamnati za ta tsaurara tsaro a sararin samaniyar kasar sakamakon al'amarin da ya faru.
“ Mun yanke shawarar ganin cewa wasu daga cikin zababbun rundunoninmu na dakarun kasar sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana musamman a fannin da ya shafi sa ido a kan sararin samaniya” a jawabin da ya yi wa ‘yan jarida.
Al'amarin wanda ya janyo damuwa tsakanin mambobin kungiyar tsaro ta Nato wanda Poland mamba ce a ciki ya janyo musayar kalamai tsakanin Kyiv da kuma Moscow.
Rasha ta bayyana ikirarin da ake yi a kan cewa ita ce ta ke da alhaki a matsayin takalar fada daga wurin Kyiv wadda manufarta ita ce ta ja sauran kasashen duniya a cikin rikici dan a yi mata taron-dangi
Sai dai a daya bangaren Ukraine ta yi watsi da zargin na Rasha, a kan cewa ita ce take da alhakin harin a matsayin ba komai ba ne illa kutungwila ce kawai daga Rasha.
Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba a shafinsa na Twitter ya ce: ''A yanzu Rasha ta gabatar da wani bayani da ya yi zargin cewa makamin tsaron sararin samaniyar Ukraine ne ya fada a yankin Poland. Wannan kuma ba dai dai ba ne.''
Harin ya ja hankalin shugabannin kasashen G20
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da ke gudana a Bali na kasar Indonesia hankalin kowa ya karkata zuwa Poland.
Shugabannin kasashen na G20 sun rika magana da ministocin tsaronsu da na harkokin kasashen wajensu ta wayar tarho da kuma jami'an gwamnatin Poland.
Shugaba Joe Biden na Amurka da Firaministan Birtaniya Rishi Sunak na cikin wadanda suka kira shugaban kasar ta Poland.
Haka kuma shugabannin Amurka da Birtaniya da na Tarayyar Turai da Sifaniya da Jamus da Kanada da Faransa da Japan da kuma Netherlands sun taru domin gudanar da abin da fadar White Hiouse ta kira taron gaggawa.
Sai dai Shugaba Biden ya ce da wuya a ce daga Rasha ne aka harba makamin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a Poland.
Ya ce, “ an samu bayanan farko da suka nuna shaku” kan ko al'amarin da ya faru a Poland yana da nasaba da makamin da aka harba daga Rasha,''
“ Ba na son na fadi haka sai mun kammala bincike amma abu ne mai wuya idan aka dubi yanayin inda aka harbo makamin, a ce daga Rasha ne amma za mu gani,'' in ji shi.
Sai dai ya ce shugabannin duniya za su tantance matakai na gaba da za su dauka bayan sun gano abin da ya faru bayan an kammala binciken da ake yi a Poland.











