Rikicin Ukraine: Shugabannin Turai za su ci gaba da aika wa ƙasar makamai don daƙile Rasha

Rikicin Ukraine

Asalin hoton, Reuters

Shugabannin kasashen yammacin duniya sun yi alkawarin kara yawan makaman da suke kai wa Ukraine, yayin da take kokarin tinkarar sabon farmakin da Rasha ke kaiwa a gabashin kasar.

Biyo bayan wata ganawa ta bidiyo shugaba Biden ya ce Amurka za ta ba da karin tallafi, gami da manyan bindigogi.

Jamus ta yi alƙawarin ba wa Ukraine kuɗi don siyan tankunan yaƙi, yayin da Burtaniya ke aikewa da makami mai linzami.

Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce da ace kasarsa ta samu makamai kwatankwacin na Rasha, da tuni an kawo karshen yakin.

Ita dai Moscow ta zargi kasashen Turai da kokarin tsawaita yakin.

''Dakarun Ukraine na daƙile hare-haren

Dakarun Ukraine

Asalin hoton, AFP

Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta ce sojojin Ukraine na ci gaba da dakile hare-haren da Rasha ke kai wa a yankin Donbas.

Cikin wani sabon rahoton tsaro, Burtaniya ta ce Moscow na ci gaba da kara kai hare-hare a yankin.

Shima shugaba Zelensky na Ukrane din ya ce hare-haren makaman atilare sun tsananta.

Ya zargi sojojin Rasha da dakile yunkurin kwashe mutane daga tashar ruwan Mariupol da aka lalata.

Rashar ta bai wa tsirarun sojojin Ukraine din da labe a wata ma'aikatar karafa da ke Mariupol wa'adi a karo na biyu, su ajiye makamansu ko ta auka musu.