'Yadda tsohon mijina ya sake ni bayan ƙwace min kwangilar biliyoyin naira'

Asalin hoton, Mansurah Isah/Facebook
Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywood, Masurah Isah ta tabbatar da mutuwar aurenta na biyu, wanda ta bayyana cewa ya zo mata a wani yanayi na ba-zata, kamar almara.
Mansurah ta ce ita aure ta yi na soyayya, domin a cewarta, "so makaho nr", amma ashe mijin da wata manufar daban ya zo, ba aure na gaskiya ba.
Mansurah ta bayyana haka ne a shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, inda BBC ta tattauna da ita tare da tsohuwar jaruma a masana'antar, Fati Mohammad kan zargin matan Kannywood da rashin zaman aure.
Da take shimfiɗa, Fati Mohammad ta ce mutane ne suke musu gurguwar fahimta, domin "shi aure ai yana da rai, kuma idan Allah ya kawo ƙarshensa, dole sai ya ƙare. Mutane da yawa aurensu yana mutuwa, amma saboda ba a sansu ba, sai ba za a ji ba," in ji ta.
Ta ce yawanci ana auren matan Kannywood ne don sha'awa, "kuma kin san tunanin mata daban da na maza. Wani da an yi auren, da ya biya buƙatarsa sai ya sake ki. Ba za a yi tunanin shi ya sake ki ba, sai a ce kin ƙi zama saboda 'ta saba da kuɗi'. Ai idan mai kuɗi ne, idan jin daɗi ne akwai kudin da jin daɗin, to me zai sa ta fito?" in ji Fati.
An daɗe ana jifar matan Kannywood da zargin ƙin zaman aure, lamarin da suke ƙaryatawa tare da cewa suma mutane ne kamar kowa, kuma wasunsu na can suna zamansu a gidajen aurensu, duk da cewa akwai waɗanda auren nasu ya mutu.
'Don kwangila ya aure ni'
A watan Yunin shekarar 2024 ne aka ruwaito Mansurah Isa ta sake wani auren bayan rabuwarta da tsohon mijinta Sani Danja.
Mansurah Isah da Sani Danja sun rabu suna da ƴaƴa huɗu: Iman da Khalifa da Sultan da Sudais, lamarin da ya ja hankali matuƙa saboda yadda aka kasance ana kwatance da aurensu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An yi ta yaɗa wani faifan bidiyo na auren na biyu na Mansurah, wada a ciki ake cewa ta yi aure, mijin ya biya sadakin naira miliyan ɗaya, auren da Mansurah ta ce shi ma yanzu sun rabu.
"Gaskiya matan Kannywood da yawa muna faɗawa cikin soyayya da sauri, ba ma gane masoyanmu na gaskiya ko maƙiyanmu, kamar yadda ƴan siyasa suke," in ji ta a lokacin da take ƙarin bayani kan batun Fati Mohammad cewa suna amincewa da namiji ne idan ya nuna musu da gaske aure yake so.
Ta ce, sun haɗu da tsohon mijin nata ne a sanadiyar wani kawunta, "na samu wata kwangila a Legas, da na ga ba ni da wani a can sai na sai na neme shi ya riƙa kula min da aikin, amma ni ce a tsakiya duk abin da ake buƙata ni zan yi magana," in ji ta, inda ta ƙara da cewa ashe shi yana da wata manufa ta zama uwa da makarɓiya a kwangilar.
Ta ce saboda haka ne "ya bijiro mani da soyayya. Lokaci ɗaya kawai ya ce a zo a yi aure, ni kuma na amince. Na ga duk abin da nake so na samu, ya ce in cigaba da fim ɗina da duk sauran harkokin da nake yi. Aka ɗaura aure da daddare, kawai da safe ya ce min zai tafi Legas."
Ta ce da ya zo auren ya zo da takardar yarjejeniya, "cewa in saka hannu ni Mansurah na amince ya cigaba da jagorancin kwangilar nan ta biliyan huɗu saboda ya zama mijina, kuma tunda maza ne shi zai riƙa magana da su kai-tsaye."
Manurah ta ce tun da ya fara magana da su, shi ke nan ya daina ɗaga wayarta, suma suka daina ɗaga wayarta.
"A taƙaice dai tun daga lokacin nan har ya sake ni, ban sake saka shi a idona ba," in ji Mansurah.
A game da halin da ta shiga, ta ce, "da ya daina ɗaga waya, sai aka je Legas aka same shi, sai ya ce wallahi shi ya manta ya yi aure. Daga baya aka buƙace shi ya sake ni, da farko ya ƙi, amma da ya ga za a yaɗa shi, sai ya amince ya yi sakin," in ji ta, inda ta ce ta amince da ƙaddara.
Zargin ƴan matan Kannyawood da 'bariki'

Asalin hoton, Fati Muhammad/Instagram
A game da zargin ƴan matan Kannywood da ake yi da zaman banza, Mansurah ta ce ba haka ne, inda ta ce wasu waɗanda a cewarta yawanci ba ƴan masana'antar ba ne suka ɓata musu suna.
"Yawanci ƴan mata masu tasowa suna mana kallon abin koyi, kuma suna kallon rayuwar ƙaryar da ake yi a kafofin sadarwa suna tunanin tamkar gaskiya ce. Akwai ƴan fim da idan kika ga gidan da iyayensu suke zama sai kin musu kuka. Akwai waɗanda a gidan ƙawaye suka zaune, amma idan suka ko kafofin sadarwa sai su riƙa nuna rayuwa mai kyau."
Ta ce yawancin masu kuɗin suna da sana'ar da suke yi, "kamar ni tun ina ƴar shekara 13 nake da shaguna guda biyu na kasuwanci a Kano."
Sai dai ta ce fitowar TikTok ta sa an rage zagin ƴan fim, domin a cewarta, "a da gani ake yi a duniya babu wanda ya kai ƴan Kannywood iskanci. Yanzu waɗada suke TikTok ɗin nan ai ba ƴan fim ba ne, yara ne da suke gaban iyayensu. Yanzu da mutane suka gane iskancin da suke yi, yanzu wa ke zagin ƴan fim? kalilan ne suke zaginmu, shi ma yawanci saboda abin da wasu ke yi ne idan sun saya mota ko sun buɗe shago sai an saka a kafofin sadarwa."
A nata ɓangaren, Fati Mohammad ta ƙara da cewa maganar da ake jifarsu da ita ta iskanci da shaye-shaye yana ci musu tuwo a ƙwarya, inda ta ce ba za a kawo wata jarumar Kannywood babba a masana'atar da take shaye-shaye ba.
"Akwai waɗanda suke shaye-shaye, da an kama su sai su ce su ƴan Kannywood ne, alhali ba haka ba ne."
Zaman aure
A game da zargin ƙin zaman aure, Fati Mohammad ta ce akwai da yawansu da suka yi aure, kuma suke zaune a gidajensu.
"Wasu da dama suna gidan mazansu, kuma wasu ma za ki ga suna rayuwa cikin rashi ne, amma duk da haka suna zaune," in ji Fati.
A nata ɓangaren, Mansurah Isah ta ce a Najeriya kaɗai da ke da miliyoyin mutane, "amma sai a riƙa maganar mutuwar auren ƴan Kannywood waɗanda ba su wuce dubu 10 ba, amma sai a riƙa cewa aurensu yana mutuwa."










