Lokuta biyar da aka yi takun-saƙa tsakanin Kannywood da gwamnatin Kano

Asalin hoton, FB/Multiple
Har yanzu ana cigaba da tafka muhawara game da matakin da Gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na dakatar da nuna wasu fina-finan Hausa masu dogon zango guda 22, waɗanda hukumar ta zarga da saɓa ƙa'idarta.
Lamarin wanda ya zo makonni kaɗan bayan gwamnatin jihar ta Kano ta dakatar da watsa shirye-shiryen siyasa na kai-tsaye ya jawo muhawara sosai, musamman a kafofin sadarwa, inda wasu suke nuna jin daɗinsu da matakin, wasu kuma ke kushewa.
An ƙirƙiri hukumar tace finafinai ta Kano ne domin tabbatar da an bi ƙa'idoji ɗab'i da harkokin fasaha a jihar Kano, wanda hakan ya sa aka fi ganin ayyukan hukumar a kan masana'antar Kannywod.
Ba wannan ne karon farko da aka samu mummunar takun-saƙa tsakanin ɓangarorin biyu ba, domin tun a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau ake ta samun saɓani da hukumar, har suke ganin idan aka samu ɗan cikinsu a shugabancinta za a samu sauƙi.
Baya ga samun saɓani da masana'antar, hukumar ta sha sawa ana kama wasu mashahuran mawaƙa ko ƴan wasan kwaikwayo, kamar Aminu Ala da Naziru Ahmed da Sanusi Oscar 442 da Sadiq Zazzaɓi da sauransu.
BBC ta yi waiwaye domin gano lokuta biyar da aka samu takun-saƙa tsakanin hukumar da masa'antar.
Haramta kallon fim ɗin 'Baƙar Ashana'

Asalin hoton, carmenmccain.com
Duk da cewa an kafa hukumar tace finafinai tun kafin lokacin, amma za a iya cewa haramta kallon fim ɗin 'Baƙar Ashana' na cikin abubuwan da suka ƙara fito da hukumar da ayyukanta.
A shekarar 2004 ce kamfanin Bright Star Entertainment ya shirya fim ɗin, wanda Aminu Bala ya bayar da umarni, inda a cikin fim ɗin aka nuna yadda mata masu zaman kansu ke gudanar da harkokinsu.
A wata maƙala da wata baturiyar marubuciya, Carmen McCain ta rubuta, ta ce an samu saɓani ne saboda Aminu Bala ya kai fim ɗin hukumar tace finafinai ta Najeriya, NFVCB, amma ya tsallake hukumar ta Kano.
Hakan ya sa hukumar ta haramta fim ɗin, sannan ta sa aka kama shi, aka ci shi tara, sannan aka ƙwace faye-fayen fim ɗin a kasuwa.
Zamanin mulkin Mallam Shekarau

Asalin hoton, FB/Ibrahim Shekarau
Wani al'amari da ya kusa durƙusar da Kannywood, har wasu suka yi tunanin masana'antar ta mutu shi ne fitar bidiyon tsiraici na jaruma Maryam Hiyana da wani mai suna Usman Bobo a shekarar 2007.
Wasu na ganin hakan ne ya sa gwamnan wancan lokacin, Malam Ibrahim Shekarau ya naɗa jami'in hukumar Hisbah, Abubakar Rabo a matsayin shugaban hukumar tace finafinai, wanda za a iya cewa ya buɗe ƙofar takun-saƙa tsakanin hukumar da masana'antar.

Asalin hoton, FB/Abubakar Rabo Abdulkarim
Rabo ya fitar da sababbin dokoki sannan ya yi wa tsofaffin garambawul, ciki har da kai wa hukumar labarin fim domin dubawa da samun amincewa kafin ɗaukar fim ɗin da fito da shi.
Zamanin Rabo ne ya jawo takun-saƙa mafi girma a harkar fim a Najeriya, inda dole wasu jaruman suka daina harkar a Kano, wasu suka koma Kano wasu suka koma Jos domin cigaba da harkarsu.
Kame-kamen Rabo

Asalin hoton, FB/Multiple
Daga cikin fitattun ƴan masana'antar da hukumar ta ɗaure a a zamanin Rabo akwai Hamisu Iyantama da Adam A. Zango da marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar 2007.
Bayan wannan lokacin ne Adam A. Zango ya koma Kaduna, ya cigaba da gudanar da harkokinsa na fim bayan zaman gidan kaso da ya yi.
A lokacin Ibro ya hau wasu waƙoƙi kamar ta 'Sanƙarau' da ake zargin ya yi wa gwamnatin lokacin gugar zana, shi ma Zango ya yi waƙar "In na ga damaa' da sauran waƙoƙi da finafinan da aka yi da aka yi zargin sun mayar da martani ne.
Haka kuma akwai waƙar "Rabo, rabo, rabon aiki, ba fa rabo, rabon wahala ba,"
Hana finafinan da ba a tace ba a YouTube

Asalin hoton, FB/Ismail Afakallu
Haka kuma a watan Janairun shekarar 2022 a zamanin shugabancin Isma'ila Na'Abba Afakallah, hukumar ta hana ɗora fim a YouTube ba tare da an tace ba.
Lamarin ya zo ne duk da cewa Afakallahu ne mutum na farko da ke da alaƙa ta ƙut da ƙut da masana'antar ta Kannywood da aka naɗa a matsayin shugaban hukumar tace finafinan.
Haka nan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da masu shirya finafinan na Hausa suka fara gano dabarar komawa sanya ayyukansu a kan YouTube a maimakon sayar wa ƴan kasuwa waɗanda ke bugawa a faya-fayen CD ko kuma kaset.
A wata zantawa da BBC, Afakallah ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon yadda ake sakin wasu finafinai da suka ci karo da al'adu da addinin mutunen jihar ta Kano.
Afakallah ya kara da cewa matakin da suka ɗauka ya haɗa da duk wani fim mai dogon zango da za a ɗauka a wasu wurare amma daga bisani a kai jihar ta Kano.
Sai dai za a iya cewa matakin bai yi tasiri ba sosai a lokacin.
Haramta finafinan Hausa 22 masu dogon zango

Asalin hoton, Abba El-Mustapha/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan matakin na ƙunshe a cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a daren Lahadi, inda ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne ya bayar da umarin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa'idojin hukumar waɗanda suka tanadi cewa dole ne hukumar ta tace su kafin a fitar da su.
Daga cikin finafinan da aka dakatar da haskawa akwai Labarina na Aminu Saira da Daɗin Kowa na gidan talabijin na Arewa24 da Gidan Sarauta na Bashir Maishadda da Garwashi da Daƙin Amarya da Kishiyata da Jamilun Jiddan da Mashahuri da Wasiyya da sauransu.
Waɗannan na daga cikin finafinan Hausa masu dogon zango da aka fi kallo.
Sai dai bayan tattaunawa da ƙungiyar MOPPAN, hukumar ta amince ta ƙara mako ɗaya kan wa'adin mako ɗaya da ta bayar tun farko, "domin kada masu fim ɗin su yi asara."
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da MOPPAN ta fitar bayan taron, sannan ta ce za a sake zama domin samar da maslaha.











