Mene ne gaskiyar iƙrarin Fasto Chris kan yawaita shan gishiri?

Fasto Chris

Asalin hoton, Pastor Chris/X

Lokacin karatu: Minti 5

A baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗi game da shan gishiri fiye da kima bayan wani malamin addinin Kirista ya soki yadda ake hana mutane shan gishiri saboda wasu magunguna su samu karɓuwa a kasuwa.

An ga Fasto Chris Oyakhilome cikin wani bidiyo yana bayanin cewa da gangan ake hana mutane shan gishiri mai yawa domin magunguna masu sinadarin sodium su yi kasuwa sosai a tsakanin al'umma.

Da take mayar da martani, Ma'aikatar Lafiya ta Najeriya ta nemi ;yan ƙasa su ci gaba da bin shawarwarin da take bayarwa da sauran likitoci, ciki har da na Hukumar Lafiya ta Duniya wato World Health Organization (WHO).

Gishiri na da muhimmanci a jikin ɗan'adam, babba daga ciki shi ne yadda sinadarin Sodium da ke cikinsa yake daidaita ruwan jikin mutum.

Kazalika, yana gishiri na daɗa wa abincimu ɗanɗano.

Wannan maƙala ta yi duba kan muhimmanci da kuma yawan gishirin da ya kamata ɗan'adam ya kamata ya sha a rana bisa bincike da kuma shawarar likitoci.

...

Asalin hoton, Getty Images

...

Asalin hoton, Getty Images

Mene ne muhimmanci da illar gishiri a jikin ɗan'adam?

Gwajin jini

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Shan gishiri fiye da kima na haddasa hawan jini, da kuma cutukan zuciya da na ƙoda, in ji likitoci

"Gishiri na taimaka wa duk wata gaɓa a jikin mutum," kamar yadda Dr. Salihu Ibrahim Kwaifa - babban likita a Abuja babban birnin Najeriya - ya faɗa wa BBC.

Likitan ya ce idan babu gishiri a jikin ɗan'adam ko motsawa ma ba zai iya yi ba sakamakon sinadaran sodium da chloride da yake ɗauke da su.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Shi ya sa ake kiran gishiri sodium chloride a [Turance]. Shi sodium yana cikin jinin mutum ne ba a ƙwayar halitta ba - wato cell. Shi kuma sinadarin Potassium chloride yana waje a cikin ƙwayar halitta. Waɗannan biyun, su ne ke tsare ɓangarorin aiki na gaɓoɓin ɗan'adam," in ji likitan.

"Idan mutum ba shi da waɗannan sinadarai a jikinsa zai fuskanci cutar da ake kira ƙarancin sodium a jiki, wadda za ta hana gaɓɓai aiki. Idan ya tsananta ma yana saka mutum ya dinga kakkafewa, idan ya wuce haka yakan sa mutum ya fita daga hayyacinsa."

Haka nan, idan babu isasshen gishiri a jikin mutum, akwai wasu magunguna da ba za su yi aiki ya dace ba. "Kamar maganin ciwon zuciya, ko kuma na ciwon ƙoda, waɗanda ke amfani da sinadarin nan na sodium," a cewar Dr. Kwaifa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ɗaya daga cikin illoli na farko da shan gishiri mai yawa ke haifarwa ita ce hawan jini, wanda ke ƙara yiwuwar kamuwa da cutukan da suka shafi zuciya, da kansar hanji, da yin teɓa fiye da kima, da ma ciwon ƙoda.

WHO ta yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 1.89 ne ke mutuwa duk shekara sakamakon ta'ammali da sinadarin sodium fiye da kima.

Ta ƙara da cewa yaƙin da ake yi da shan gishiri mai yawa, shi ne mafi samar da amfani wajen rage yaɗuwar cutukan da ba ɗauka daga mutum zuwa mutum. Sannan duk dala ɗaya da aka zuba wajen yaƙi da hakan tana jawo amfanin da ya kai darajar dala 12.

Mene ne yawan gishirin da ya kamata mutum ya sha a kullum?

Sakwara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sakwara

Wata sanarwa da Ma'aikatar Lafiya ta Najeriya a matsayin martani ga Fasto Chris Oyakhilome ta ce yawaita shan gishiri ne jawo wa mutane matsala ba gishirin kansa ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce jimillar adadin sinadarin sodium da babban mutum ya kamata ya sha a duk rana shi ne 2000 mg, wanda ya yi daidai gishiri giram biyar (5g) - ma'ana kamar daidai cikin cokalin shan shayi ɗaya na gishiri.

Sai dai WHO ta ce akasarin mutane a kowace al'umma a duniya na shan sinadarin sodium fiye da kima da ya kai 4310 mg (ko kuma gishiri 10.78 g) - wato fiye da ninki biyu na abin da ya kamata su sha.

Ma'aikatar Lafiya ta Najeriya ta ce bincike ya nuna 'yan ƙasar ma na shan gishirin sama da ninki biyu na abin da ya kamata, "abin da ke jawo...cutukan da ke kashe dubban mutane duk shekara".

Saboda haka ne ma'iakatar ta ce ta ƙaddamar da wasu shirye-shirye domin rage yawan adadin sodium da 'yan Najeriya ke sha.

"Daga ciki akwai ƙaddamar da jerin shawarwari domin rage yawan sodium a na'ukan abincin da ake ci a gida ko kuma wuraren sayarwa," in ji ma'aikatar.

Mene ne bambancin gishiri da sanadarin ɗanɗano?

Abinci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masana sun ce sinadarin sodium a cikin magi ya fi na gishiri yawa

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke rikita mutane game da shan gishiri shi ne bambanci ko kuma alaƙa tsakanin gishiri da sanadarin ɗanɗano.

Masana sun ce shi ma sanadarin ɗanɗano gishiri ne, har ma adadin sinadarin sodium da ke cikinsa ya ɗara na gishirin, abin da ke nufin zai fi yi wa mutum illa idan ba a kiyaye ba.

"Wajen kashi 60 zuwa 70 na sanadarin ɗanɗano na zamani sanadarin sodium ne - wato gishiri ne shi ma," a cewar Dr. Kwaifa.

"Idan mutum ya ce ba zai ci gishiri ba sai sanadarin ɗanɗano kawai, akwai yiwuwar illar da zai samu sai ta wuce ta cin gishirin idan ya zuba da yawa. Saboda haka, da mutum ya ci sanadarin ɗanɗano kaɗai gara ya yi amfani da gishiri kaɗan."