Abu huɗu da suka fito fili sakamakon kisan matafiya a jihar Edo

Edo

Asalin hoton, Canva collage BBC Pidgin

Lokacin karatu: Minti 5

Har yanzu ana cigaba da tafka muhawara kan kashe matafiya mafarauta ƴan arewacin Najeriya da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo a kudancin ƙasar, lamarin da ya ja hankalin ƙasar baki ɗaya.

Mutane da dama daga yankin arewa sun yi Allah wadai da kisan, tare da kira da a ɗauki matakin gaggawa domin kiyaye aukuwar lamarin a gaba.

Tuni masana harkar tsaro a ƙasar suka fara yin fashin baƙi dangane da darussan da ya kamata a koya daga al'amarin.

Malam Kabiru Adamu wanda masanin harkokin tsaro ne a Najeriya kuma shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya shaida wa BBC waɗansu abubuwa guda huɗu da ya ce su ne suka bayyana daga kisan farautan.

1) Gazawar jami'an tsaro

Wani abun da ake ta tafka muhawara tun bayan da batun kisan matafiyan ya bayyana shi ne rasihn ganin jami'an tsaro sun kawo ɗauki, lamarin da Dokta Kabiru Adamu ya ce ya ƙara nuna gazawa a fili.

Ya ce, "akwai gazawar jami'an tsaro. Daga farkon lokacin da abin ya faru zuwa ƙarshen kisan wulkancin baki ɗaya ya kai aƙalla tsakanin minti 30 zuwa 40. Kuma a tsari na tsaro, duk abin da ya kama daga minti 7 zuwa 10, ya kamata a ga jami'an tsaro a wajen," in ji shi.

Masanin tsaron ya ce yadda aka yi, aka ci aka goge baki ba tare da jami'an tsaro sun kawo ɗauki ba matsala ce, wadda ke nuna, "akwai giɓi da gazawa daga ɓangaren jami'an tsaron."

Sai dai ya ce suna jiran ganin an gabatar da waɗanda aka ce an kama domin su fuskanci hukunci.

"Wataƙila za su ce saboda hutu ne, amma a ƙasashen da aka cigaba ana hanzarin gabatar da irin waɗannan abubuwa ne domin a yi hukunci cikin gaggawa domin zama izina," in ji shi.

2) Rashin yarda da jami'an tsaro

Malam Kabiru Adamu ya ce babban matsalar da ake samu ita ce mutane da dama ba su da yarda da haƙiƙancewa kan cewa idan sun kai ƙarar wanda suke zargi da laifi za a ɗauki matakan da suka dace wajen bincike da hukunci, wanda a cewarsa hakan ke sawa mutane ke ɗaukar doka a hannu.

"Yadda doka ta tanadar shi ne idan kana zargin mutum da aikata laifi, doka cewa ta yi ka miƙa shi ga jami'an tsaro, su ne suke da hurumi. Suma ɗin dai iyaka su gabatar da shi a gaban kotu. Amma yanzu an waya gari mutane da dama ba su da wannan yardar cewa jami'na tsaron za su yi musu adalci," in ji shi.

Ya ce irin wannan ne ya sa aka samu matsalar da har mutane suke ɗaukar doka a hannu wajen kashe wanda suke zargi da laifi.

3) Yawaitar ƙungiyoyin sa-kai

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Malam Kabiru ya kuma ce akwai matsalar ƙaruwar ƙirƙirar jami'an tsaro na sa-kai da ake yi a jihohi da yankuna, sakamakon gazawar jami'an tsaro waɗanda a cewarsa ba bisa ƙa'ida ake yi ba.

A cewarsa, "har yanzu kundin tsarin mulkin Najeriya ya bar tsaro ne a matakin tarayya. Abin da doka ta amince da shi kenan kuma ba a canja ba. Amma yanzu an wayi gari kusan kowace jiha tana da tanade-tanaden tsaronta. Haka ma wasu al'umomin sun yi nasu."

Sai dai ya ce wasu daga cikin jihohin sun je majalisunsu na jiha sun yi doka, "amma a fahimtarmu wannan ya saɓa da kundin tsarin mulkin ƙasar kuma majalisar tarayya ta yi shiru a kai. Gaba dai dole a je kotun ƙoli domin ta fayyace komai."

Ya ƙara da cewa bayan ɗaukar ƴan sa-kan ba bisa ƙa'ida ba, yawanci ba a ba su horo da ya dace, "wasunsu horon bai wuce wata uku, waɗanda suka daɗe ne suke wata shida, kuma a cikin horon ba a koya musu abin da ya dace wajen fuskantar laifuka wato 'rules of engagement' da kuma tattalin aiki da makaman da aka ba su."

Sannan ya ce ko da ma an je ɗaukar ma'aikatan, "ba a cika bin tsari ba. Yawanci ana sa ɓangaranci, sannan babu tsarin bibiya domin gudun kada a ɗauki wani tsohon mai laifi."

4) Ƙiyayya a tsakanin juna

Wani abu da masanin harkokin tsaron ya ambata da ke kawo matsala shi ne yadda kalmomin ƙiyayya da tsanar juna ke yawaita a tsakanin al'ummomi daban-daban.

Ya ce yawanci mutanen kudu da suke fama da matsalolin tsaro suna zargin akwai sa hannun Fulani ne.

"Amfani da kalmar Fulani. Ɗan kudu idan ya ji kalmar Fulani bai iya bambancewa saboda akwai wata tsanar da yake yi wa Fulanin. Wani lokacin masu aikata irin waɗannan aika-aikar suna aikatawa ne da wannan tsanar ta Fulani da ke zuciyarsu ba tare da la'aikari da cewa waɗanda wataƙila mutanen ba ma Fulanin ba ne," in ji shi, inda ya ƙara da cewa, "misali waɗanda aka kashe a Edo ai mafarauta ne, ba Fulani ba."

Shawara

A game da hanyoyin da ya kamata a bi domin kaucewa ko rage aukuwar irin waɗannan matsalolin, Malam Kabiru Adamu ya bayar da wasu shawarwari kamar haka:

  • Mafarauta

Ya ce bai kamata ba a ce a wannan yanayi da ake ciki ɗan arewa ya tashi ya tafi kudu farauta kuma da makami a hannunsa.

"Duk wanda ya gan shi, tunani na farko da zai yi shi ne mai garkuwa da mutane. Kuma saboda yawaitar matsalar yana da wahala ka fahimtar da shi cewa ba ɓarawon ba ne."

  • Gwamnoni

Ya ce akwai buƙatar gwamnonin arewa su ɗauki matakan tuntuɓa tare da tataunawa da takwarorinsu na kudu domin su yi tsari ta yarda idan ma za a je farautar ko wani abu zuwa yankin, dole za a bi wannan daftarin ne.

  • Faɗakarwa

Shugabanni da malamai da jagororin al'umma su riƙa faɗakar da mutane.

  • Bayanan masu zuwa kudu

Ya ce zai yi kyau gwamnoni su ɗauki bayanan ƴan arewa masu kudu saboda idan haka ya faru a gano waɗanda lamarin ya rutsa da su.

"Irin wannan ba don an naɗa a bidiyoba, da ba dole ba ne a gane waɗanda abin ya rutsa da su. Tattara bayanan zai taimaka wajen bin kadi da diyya," in ji shi.

Halin da ake ciki a yanzu

Yanzu haka dai gwamnan jihar ta Edo, Monday Okpebholo na yin rangadi a jihohin arewacin ƙasar, inda yake ganawa da gwamnoni da masu ruwa da tsaki na yankin domin jajantawa kan kisan mafarautan guda 16.

A ganawarsa da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Okpebholo ya sanar da kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a aika-aikar, sannan ana neman sauran ruwa a jallo, kamar yadda rundunar ƴansanda jihar ta bayyana.

A nata ɓangaren, rundunar ƴansanda ta Najeriya ta sanar da karɓe binciken lamarin daga rundunar ta jihar Edo, inda ta ce an mayar da lamarin sashen binciken manyan laifuka na rundunar da ke Abuja.

Harwa yau gwamnatin jihar Edo ta dakatar da ayyukan ƴan sa-kai baki ɗaya a jihar.

Sai dai duk da haka, ana ganin an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa musamman kan ɗaukar doka a hannu da ke kaiwa ga kashe mutanen da ba su ba, ba su gani ba, lamarin da Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited ya ce akwai ɗanyen aiki a gaba.

Masanin harkokin tsaron a Najeriya da yankin Sahel ya ce idan ana so abubuwa su inganta, to lallai dole a koyi wasu darussa daga wannan kisan.