Waiwaye: Kisan matafiya a jihar Edo da kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Isuhu Yellow

Gwamnan Edo Okphebolo

Asalin hoton, Edo State Government

Lokacin karatu: Minti 4

Kamar kowane mako, mun duba wasu daga cikin manyan labaran da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.

Kisan matafiya a jihar Edo

Wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga kudanci zuwa arewacin Najeriya.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce mutanen da aka kashe 'yan asalin jihar Kano ne kusan 16.

"Yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fito da su daga motarsu, suka yi musu duka, sannan suka cinna musu wuta," a cewar wani saƙo da Amnesty ta wallafa a shafukan sada zumunta.

Ta ƙara da cewa matafiyan na kan hanyar komawa garinsu na asali ne "domin yin bukukuwan sallah tare da iyalansu".

Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta Edo ta fitar ta tabbatar cewa maharan 'yan sa-kai ne.

"Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴanbanga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne," kamar yadda sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Fred Itua, ya bayyana.

Yunƙurin majalisa na cire wa gwamnoni da mataimakin shugaban ƙasa rigar kariya

Tajudeen Abbas

Asalin hoton, House of Reps

Yunƙurin da Majalisar Wakilan Najeriya ke yi na gyara kundin mulkin ƙasar domin janye rigar kariya ga gwamnoni da mataimakin shugaban ƙasa ya bar baya da ƙura, yayin da ta yi amai kuma ta lashe.

A ranar Laraba ne majalisar ta yi wa ƙudirori sama da 40 karatu na biyu, waɗanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska, cikinsu har da wanda ya nemi a tuɓe wa mataimakin shugaban ƙasa da gwamnonin jiha rigar kariya.

Sai dai kuma, kwana ɗaya da ɗaukar matakin ne majalisar ta ce ta janye karatu na biyun da ta yi wa ƙudirin rigar kariyar.

Yayin zamanta na ranar Alhamis, ɗanmajalisa kuma Shugaban Masu Rinjaye Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudirin neman janye matakin da kuma neman sake saka shi cikin waɗanda za a yi muhawara a kai.

Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya ce sun yanke shawarar yin hakan ne "saboda a sake yin cikakkiyar muhawara a kan sa ganin irin muhimmancinsa".

Haka nan, majalisar ta janye karatu na biyu da ta yi wa ƙudirin da ke neman a yi wa tanadin hukuncin kisa gyara.

Yadda aka kashe ƙasurgumin ɗanbindiga Ɗan-Isuhu a jihar Zamfara

Dan-Isuhu

Asalin hoton, Nigeria Police

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fitaccen ɗanbindigar nan da ya yi fice wajen garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, wanda ya addabi yankunan jihar Zamfara da wasu yankunan jihar Katsina, wato Kachalla Isuhu Yellow, wanda aka fi sani da Ɗan-Isuhu ya cimma sa'i.

Lamarin ya auku ne da yammacin Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴanbindiga a arewacin Najeriya da suke nemansa ruwa a jallo.

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar ɗanbindigar a wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar.

Haka nan ma ɗanjarida mai bincike kan harkokin ƴanbindiga, Munir Fura-Girke ya tabbatar da kashe ɗanbindigar.

Sanarwar ƴansanda ta ce jam'ian tsaro ne suka samu labarin cewa an ga ƴanbindiga da dama ɗauke da muggan makamai sun nufi garin Keta, inda ya ce jami'an tsaron haɗin gwiwa na ƴansanda da askarawan Zamfara da ƴan sa-kai da mafarauta suka kai ɗauki, inda suka fafata da gungun ƴanbindigar na tsawon lokaci.

  • Ga cikakken labarin a nan:

Kungiyoyi 93 na neman rajistar zama jam'iyyu

Yayin da babban zaɓenta a shekarar 2027 ke ci gaba da karatowa a Najeriya sama da ƙungiyoyi cassa'in da uku (93) ne suka miƙa buƙatar zama jam'iyyun siyasa gare ga hukumar zaben kasar INEC.

Sai dai mika wannan bukatar, ya sa wasu daga cikin manyan jam'iyyun hamayya a Najeriyar cewar, ƙara yawan jam'iyyun zai iya wargaza shirinsu na haɗewa wuri guda domin ganin sun karbe mulki daga hannun jam'iyya APC a zaɓen na 2027.

Mai magana da yawun hukumar zaben a Najeriya ta INEC, Zainab Aminu, ta ce 'kawo yanzu hukumar ta karbi kusan kungiyoyi 93 da suka mika bukatarsu na son a yi musu rajistar zama jam'iyya.

sannan ta ce har yanzu su na nan su na ci gaba da karba, tare da duba yiwuwar yi musu rajistar, idan har sun cika ka'idar.

Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun Sallah

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma'aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.

A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.

Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu'ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

Ba za mu yi haɗaka da kowa ba - SDP

Jam'iyyar SDP a Najeriya ta yi watsi da yunkurin haɗaka tsakaninta da sauran jam'iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027.

Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam'iyyar ta SDP ya karu sakamakon sauya shekar da wasu manya 'yansiyasa a kasar ke yi zuwa cikinta.

A makon da ya gabata ne wasu jagororin adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP suka sanar da cewa suna wani yunƙuri na ƙulla haɗaka domin kawar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai shugaban jam'iyyar na kasa Alhaji Shehu Musa Gabam a hirarsa da BBC ya ce SDP ba za ta haɗe da wata jam'iyya ba.

  • Karanta cikakken labarin a nan: