Ana samun karuwar cutar tamowa a jihar Bauchi - MSF

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar agaji na likitoci ta Medecins Sans Frontieres - MSF ta bayyana cewa matsalar cutar tamowa na ƙara tsanani a jihohin arewacin Najeriya, musamman a jihar Bauchi da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Wannan lamari ne da ƙungiyar ta bayyana a matsayin mai ban mamaki ganin cewa galibin wuraren da aka yi hasashen za su yi fama da wannan matsalar, jihohi ne da ke fuskantar matsalolin tsaro wanda ke haifar da samun ƴan gudun hijira, kuma ita jihar Bauchi ba ta da wadannan ƙalubalen.
A wani rahoton da ƙungiyar ta fitar a watan mayun wannan shekarar, ta yi hasashen cewa matsalar na iya ta'azzara a wasu jihohin arewa a cikin wannan shekarar amma lamarin na jihar Bauchi ya wuce yadda ta yi tsammani.
Adam Ousmane N'Gari wani babban jami'i na ƙungiyar ta MSF a Najeriya ya shaidawa BBC, ''A Bauchi matsalar na da girma sosai, yau shekara biyu ke nan da mu ke buɗe cibiya ta Bauchi kuma mun fara ne da gado 72, mu ka ƙara zuwa 250 bayan wani lokaci, amma a yanzu da mu ke magana muna da kusan gado 300 a wannan cibiyar.''
N'Gari ya ƙara da cewa matsalar na nema ya fi karfinsu inda ya yi kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki cikin lamarin da su yi yunƙurin tallafa wajen magance matsalar.
Ya ce: ''Yanzu a Bauchi MSF ce kaɗai ƙungiyar ƙasashen waje da ke yaƙi da wannan matsalar ta tamowa, don haka mu ke kira ga mutane da su agaza mana domin mu yi aiki tare saboda wannan matsalar ta na neman tafi ƙarfin mu. Matsalar na da girma sosai, idan ba mu tashi tsaye ba abin zai gagari kowa da kowa.''
Babban jami'in na MSF ya kuma ƙara yin kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta hanyar ma'aikatar lafiya da ta taimaka musamman ta fannin wayar da kan al'umma kan girman matsalar domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin magance ta.
MSF ta alaƙanta matsalar da rashin samun isashen abinci mai gina jiki wanda hakan ke da nasaba da matsin rayuwa, sakamakon barazanar tattalin arziki da kuma sauyin yanayi wanda ke kawo cikas a al'amuran noma.
Ƙungiyar ta ce tun shekaru biyu da suka gabata take gargaɗi game da yiwuwar fuskantar ƙaruwar matsalar tamowa tsakanin yaran arewacin Najeriya, amma ta ce na wannan shekarar ya zarce yadda ake tunani,
A watan Mayun wannan shekarar 2024 ne majalisar ɗinkin duniya da gwamnatin Najeriya suka ce ana buƙatar fiye dala miliyan 300 domin magance matsalar tamowa a jihohin arewa maso gabashin ƙasar.
To sai dai da alama wannan kuɗi ya gaza duba da yadda matsalar ta bazu a wasu sassan jihohin yankin arewacin ƙasar, kamar yadda ƙungiyar MSF ta yi bayani.
Medicine San Frontiers ta ce akwai buƙatar ƙara wayar da kan jama'a domin su bayar da ta su gudumawar domin kawar da wannan matsala a jihar Bauchi da ma yankin arewacin Najeriya baki ɗaya.










