Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne ne mutanen da Saudiyya ta yarje wa shan barasa a ƙasar?
- Marubuci, Sameer Hashmi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Worklife
- Lokacin karatu: Minti 5
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun fara ɗage haramcin sayar wa masu kuɗi ƴan ƙasashen waje basara a ƙasar, a wani mataki na sauya dokar haramcin da aka sanya shekara 73 da suka gabata.
Masu sharhi na ganin da yiwuwar a faɗaɗa dokar zuwa ga masu yawon buɗe idanu a ƙasar, a cewar wakilin BBC.
An kwashe gomman shekaru ana aiki da haramcin shan barasa a ofishoshin jakadanci da gidajen baƙi domin kare dokokin ƙasar.
Saudiyya - wadda ƙasar masallatai biyu masu alfarma ce - ta haramta sha da sayar da barasa a 1952.
To sai dai a yunƙurin ƙasar ya wanke kanta a idanun ƙasashen duniya, a baya-bayan nan Saudiyya ta ɓullo da wasu sauye-sauye domin nuna kanta a matsayin mai bin matsakaicin ra'ayin addini.
A ƙarƙashin shugabancin Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ƙasar ta bayar da umarnin buɗe sinima tare da ɗaukar baƙuncin manyan bukukuwan kaɗe-kaɗe na duniya, da ɗage haramcin tuƙin mata tare da rage ƙarfin ƴan hisba a ƙasar.
To amma ɗage haramcin sayar da barasa ya kasance babban abin da ya ɗauki hankali zuwa yanzu.
A watan Janairun 2024 aka buɗe katafaren kantin sayar da barasa a birnin Riyadh, to sai dai an taƙaice masu iya saye kan jami'an diplomasiyya da ba musulbai ba.
To amma a wata sabuwar doka da aka fara aiki da ita ba tare da sanarwa ba a karshen shekarar 2025 a yanzu masu kuɗi, ƴan ƙasashen waje da ba Musulmai ba za su iya zuwa kantin domin sayen barasa.
Dokar ta yi tanadin cewa dole sai wanda ya mallaki takardun izinin zama a ƙasar na aƙalla shekara guda 'Premium Residence Permit' wadda ake bayarwa a kan riyal 100,000, kwatankwacin dala 27,000, ko kuma su nuna hujjar da ke nuna cewa suna samun aƙalla riyal 50,000 a kowane wata.
Kwastomomi da dama da suka sayi barasar a wannan kanti sun yi magan da BBC bisa sharaɗin ɓoye sunayensu.
Dole sai an kashe waya an kuma ɓoye ta cikin jaka kafin a bar kwastoma ya shiga cikin kantin.
Wani Bature da BBC ta zanta da shu ya bayyana kantin da ''haɗaɗɗen kanti'', wanda farashin barasar na ninka sau biyu zuwa uku da yadda ake sayar da ita a Turai, amma kuma ya ce duk ha haka barasar ta fi sauki a kanti fiye da kasuwannin bayan fage na ƙasar.
"Kwalba ɗaya ta barasar Johnny Walker Black Label whisky ta kai dala 124. Amma duk da haka ban damu da tsadar ba'', in ji shugaban wani kamfanin Birtaniya.
Sha da fataucin basara haramun ne ƙarƙashin dokokin Musulunci, kuma koyarwar Addinin Musulunci ta kasance babbar aƙidar da mafi yawan ƴan ƙasar Saudiyya ke bi.
To amma duk da haramcin an kwashe gomman shekaru ana safarta ta ɓarauniyar hanya a ƙasar.
Akan yi safarar wadda aka sarrafa gida da wadda aka shigar da ita ƙasar a ɓiye ta ɓaraniyar hanya.
Sauya dokokin harƙallar basara a ƙasar ya zo daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙarin matsin tattalin arziki.
Yanzu haka akwai wasu rahotonnin kafofin yaɗa labarai da ke cewa hukumomin ƙasar na shirin sake buɗe wasu kantunan sayar da basarar biyu a ƙasar.
Ɗaya a gaɓar tekun Maliya da ke birnin Jedda, yayin da ɗayan zai kasance a birnin Dhahran da ke gabashin ƙasar, inda shalkwatar kamfanin man ƙasar Aramco take.
Yayin da kasuwannin makamashin ƙasar ke fama da matsaloli a ƴan shekarun baya-bayan nan, kasar na neman masu zuba jari daga ƙetare tare da buƙatar ƙwararru domin gina ɓangaren kasuwancinta da ba na man fetur ba, kamar fannin ƙirƙirarriyar basira da kam kamfanoni.
Ƙasar Saudiyya na cike da burin kammala manyan ayyukan da ta saka a gaba, ciki har da katafaren aikin gina Birnin Neom da zai laƙume tiriliyoyin daloli.
Wani abu da ya sa ƙasar ke neman ƙwararrun masu fasaha da masu zuba jari.
A daidai lokacin da ƙasar ke zuba jarin biliyoyin daloli a fannonin yawon bude idanu da shaƙatawa da wasannin motsa jiki na duniya, a wani ɓangare na dabarunta na kawar da mai.
Ƙasar ta kuma gina wani katafaren otal na alfarma a bakin tekun Maliya, musamman domin baƙin da suka fito daga yammcin duniya.
Yawon shaƙatawa shi ne babban ginshiƙi cikin shirye-shiyen Saudiyya na Vision 2030.
A 2024, ƙasar ta jawo hankalin baƙi kusan miliyan 30 na duniya, tare da tafiye-tafiyen da ba na addini ba yanzu ya kai fiye da rabin adadin masu zuwa ƙasar, a cewar Ministan yawon buɗe ido Ahmed Al Khateeb.
Saudiyya na da burin janyo hankalin masu yawon buɗe ido miliyan 70 na duniya nan da shekarar 2030.
"Muna son ninka abin da muke samu daga m asu yawan buɗe idanu nan da 2030,'' kamar yadda ya bayyana cikin wata hira da BBC a watan Nuwamban 2025.
Ƙasar wadda ke yankin Gulf na shirin ɗaukar baƙuncin manyan gasanni na duniya, ciki har da Gasar Kofin Duniya ta 2034 da Babban bikin baje kolin al'adu an duniya da za a yi a 2030.
An kuma ɗage wasannin bazarar na n ahiyar Asiya da aka yi a birnin Neom a 2029, duk da yake ba a bayyana dalilin ɗagewar ba wasu na ganin rashin kammala aikin gina birnin ne na daga cikin dalilan.
Ƙasar na ƙoƙarin inganta sauran fannonin tattalin arzikinta domin rage dogaro da man fetur, wanda a yanzu farashinsa ke tsakanin dala 60 zuwa 66 a kasuwannin duniya, saɓanin dala 100 da yake a 2022.
Raguwar farashin dai ya haifar da ragin kuɗin shiga ga ƙasar, sakamakon fannin man shi ne ginshiƙi cikin hanyoyin samun kuɗin shigar ƙasar.