Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya na shirin buɗe shagon sayar da giya na farko ga jami'an diflomasiyya
Saudiyya na shirin barin a fara sayar da giya ga jami'an diflomasiyyar da ba Musulmai ba karon farko a tarihin ƙasar.
Kafafen yaɗa labari irin su Reuters sun ruwaito cewa an sanar da hakan ne a ranar Laraba a wani mataki na sassauta tsauraran dokokin da ƙasar da aka santa da ra'ayin riƙau ke da su a baya.
Kwastomomi za su riƙa yin rijistar sayan barasar ta manhajar salula, sannan a ba su wasu lambobin sahalewa daga ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, sannan ba za su wuce abin da aka ƙayyade musu za su saya a wata ba, kamar yadda yake a wata sanarwa da Reuters ya ruwaito ya gani.
Za a riƙa sayar da barasar ga jami'an diflomasiyyar da ba Musulmai ba, wadanda a baya suke sayanta da sunan ofisoshin da suke aiki, ko kuma a kawo musu ita a hukumance.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa "shagon da za a riƙa sayarwa za a buɗe shi ne a Riyadh" wani yanki da ke kusa da ofisoshin jami'an kasashen ketare da wuraren zamansu.
Za a riƙa barin mutanen da suka saya a manhajar Diplo ne kawai su riƙa shiga domin karɓar abin da suka saya.
Tun a 1952 aka haramta tare da kafa dokar shan giya a faɗin ƙasar Saudiyya, jim kaɗan bayan da wani daga cikin 'ya'ya gidan Sarki Abdulaziz ya sawu ya harbe wani jami'in diflomasiyyar Burtaniya har lahira.
Cikin shekaru masu yawa, an ta yaɗa jita-jitar cewa za a riƙa sayar da barasa a masarautar ta yankin Gulf cikin, yayin da ake tsaka da kawo sauye-sauyen rayuwa wanda Yarima Mohammed bin Salman ke fatan gani a matsayin burinsa nan da 2030.
Ciki har da buɗe gidajen kallo na zamani da kuma bikin rawa na shekara-shekara da za a hadu maza da mata.
Wata sanarwa da gwamnatin Saudiyya ta fitar a ranar Laraba ta ce hukumomin ƙasar na fitar da "sabbin ƙa'idoji da za a riƙa aiki da su.. domin kawar da hada-hadar da ake yi ta kwayoyi da giya da ake yi da jami'an diflomasiyya ba bisa ka'ida ba".
Sanarwar ta ƙara da cewa: "sabuwar dokar za ta mayar da hankali ne kan adadin barasar da za ta shiga Saudiyya domin kawo ƙarshen shigar da ita ba bisa ka'ida ba."
Tsauraran dokoki
Kamfain dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an sanya tsauraran dokoki game da sayar da barasar, "babu wanda za a sayarwa inda Musulmi ne. Za a sayar da ita be ga waɗanda ba Musulmi ba kawai".
"Ba za a bar ɗan ƙasa da shekara 21ba ya shiga shagon sayar da barasar" kuma "dole mai sayan ya yi shigar mutunci" in ji sanarwar.
Ko da mutum ya yi rijista ta manhajar wayar, ba zai iya aika ɗan uwansa ko direbansa ba ya karba masa, sai dai ya je da kansa.
An haramta amfani da waya a cikin shagon sayar da giyar.
Goga kafaɗa da makwabtan yanki
Burin 20230 na son sauya ƙasar da ta fi kowacce fitar da ɗanyen mai ta zama fuskar kasuwanci, yawon buɗe idanu da kuma wasanni, a wani shiri na ƙarkata akalarta zuwa ƙasar da za ta riƙa samun kuɗin shiga ba ta dalilin mai ba.
Labarin na ranar Laraba na zuwa ne lokacin da Saudiyya ke ƙara yunƙurin goga kafaɗarta da makwabtanta musamman Dubai da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wajen jan hankalin masu zuwa jari daga ƙasashen ƙetare da masu buɗe ido.
Misali a wannan watan, hukumomin ƙasar sun aiwatar da wata doka da ta nemi kamfanonin ƙasashen ketare su buɗe hedikwatarsu ta yankin a Saudiyya ko kuma su rasa kwangilar da gwamnati ta basu.
Ana sayar da giya a otel-otel masu yawa da wuraren sayar da abinci a Dubai.
A Qatar da ke makwabtaka, ana sayar da giya a gidajen abinci da otel masu lasisi amma ga waɗanda ba Musulmai ba da kuma suka haura shekara 21.
A bara aka bai wa Saudiyya damar ɗaukar nauyin gasar Cin Kofin Duniya na 2034 da kuma wasanni Expo na 2030 da za a yi a Riyadh, wanda tun a nan aka fara yada jita-jitar cewa za a iya janye haramcin giya.
Sai dai kowa ya san cewa ta’ammali da giya haramtaccen abu ne a addinin Musulunci, shi ya sa wanan lamari ya zama mai wuyar tattaunawa a ƙasar, wadda ita ce mafi tsarki ga mabiya addinin Islama, saboda garuruwan Makka da Madina.
A ƙarƙashin dokokin Saudiyya, sha ko kuma ta’ammali da giya kan iya jan hukunci kamar zaman gidan yari na tsawon lokaci, ko bulala a cikin mutane ko mayar da mutum ƙasar da ya fito ga waɗanda ba ‘yan ƙasar ba.