Abin da ya kamata ka yi idan ka kasa bacci

Asalin hoton, Getty Images
Wataƙila ka kasa bacci, ko kuma ka tashi a tsakiyar dare kuma ka kasa komawa bacci.
Rashin bacci wata matsala ce, da za ta iya shafar mu a wani lokaci a cikin rayuwarmu- amma ga wasu, matsalar ta wuce na ƙasa yin bacci na wani gajeren lokaci, yakan zama babbar matsala.
Akwai abubuwa da dama da za su iya zama dalilan samun matsalar bacci, da lokacin da kamata mu nemi taimako, da kuma yadda yawan shekaru, ko buƙatar yin fitsari da daddare, ko kaiwa shekarun ɗaukewar jini, ko kuma yanayin aiki da ke sauyawa su ke taka rawa wajen samun matsalar.
Tawagar Sashen binciken lafiya ta BBC ta tattaro ƙwararru, waɗanda su ka bayar da shawarwari masu ban mamaki.
Shawarwarin da ƙwararrun suka bayar
Dakta Faith Orchard, malama a fannin ilimin halayyar ɗan'adam a Jami'iar Sussex na ganin cewa karatun littafi zai taimaka wajen magance matsalar.
''A mafi yawan lokuta tunani ne ke hanani barci. A don haka nakan ɗauki littafi in fara karatu har sai na shirya ƙara hutawa.''
Ita kuwa Dakta Allie Hare, shugabar cibiyar binciken lamuran da suka shafi bacci ta Birtaniya, kuma likita a fannin waraka daga matsalar bacci a asibitin Royal Brompton da ke London, tana ganin cewa sauya makwanci ne mafita ga matsalar.
''Idan na ƙasa bacci, wasu lokuta saboda mijina na juye-juye a kan gado, ko kuma yana minshari, abin na nake yi sai na koma wani ɗakin, sai kuma na yi baccin''.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Colin Espie, Farfesa a fannin matsalolin da suka shafi bacci a Jami'ar Oxford na ganin tashi daga gadon a kuma sake komawa ne mafita.
''A lokacin da na kasa bacci, nakan tashi daga gadon, sannan in sake komawa kai domin farawa daga farko, domin hakan na faruwa ne saboda akwai abin da ke raina. kuma ina ganin wannan ne matsalar ga mafi yawan mutane.''
Farfesa Espie ya ce idan ka kasa bacci na dare ɗaya, daga nan ya koma kwanaki, zuwa makonni har suka koma watanni uku ko fiye, muna kiran wannan matsalar ''rashin bacci.''
Matsalar kasa bacci na da alamomi da dama, a cewar Dakta Orchard ''Mukan alaƙanta matsalar da rashin iya baccin tun da farko, amma a zahiri matsalar ita ce kasa yin baccin tun farko da kuma iya cigaba da bacci.
Ga wasu mutanen yakan zo musu a yanayi na farkawa cikin dare da kuma wahalar komawa bacci, ko kuma tashi da wuri sosai da kuma kasa komawa baccin.''
Dakta Hare ta ce aƙalla kashi 50 na mutane na fama da alamomin.
Idan ka yi fama da rashin bacci a dare uku ko fiye cikin mako guda har tsawon fiye da wata uku- kuma hakan ya shafi al'amuran rayuwarka a rana ta gaba- to lokaci ya yi da zaka nemi magani.
Me ke faruwa a ƙwaƙwalwa da ke kawo rashin bacci?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Orchard ya ce abubuwa biyu ne ke taimaka mana yin bacci da kuma tashi, su ne sinadarin hallitun ɗan'adam da ke saka bacci, da gajiyar da aka tattara daga ayyukan da aka yi a ranar.
Abubuwan biyu suna aiki tare, idan ba su haɗu yadda ya kamata ba, misali idan muka yi bacci da rana ko da yamma, tsarin ba zai tafi yadda ya kamata ba kuma yin baccin daren zai iya yin wahala.''
Farfesa Espie ta ce '' idan akwai wani abu da kake tunani a ranka, ƙwaƙwalwarka za ta gane cewa ba ka so ka yi bacci kana so ka tsaya ka yi tunanin abin da ke damunka saboda zai iya zama abu mai muhimmanci, zai iya zama mai barazana.''
Dakta Hare ta kuma ce wasu rashin lafiyar kan janyo ranshin bacci, '' Mun san cewa mutanen da ke da rashin lafiya masu tsanani, ko tsanannin ciwo, akwai yiwuwar za su fi fama da yin bacci, saboda rashin bacci na da alaƙa da ciwon damuwa, ko yawan fargaba ko wasu matsalolin kwakwalwa''.
Shi kuwa farfesa Espie ya ce shekaru ma na iya zama dalili, ''tsarin bacci yana tsufa, tsarin agogon jikin ɗan adam ma yana tsufa, tsarin bacci shi ne yawan baccin da kuma nauyin baccin, tsarin agogon kuma shi ne lokacin da ake baccin. Abin da ke faruwa shi ne a lokacin da shekarun ke ja, baccin na ɗan rarrabuwa.
''Sai dai agogon ma yana tsufa, yadda matashi na iya jinkirin bacci, ya kuma yi jinkirin tashi, amma wanda ya tsufa yakan yi bacci da wuri ya kuma tashi da sanyin safiya kuma ya yi fama wajen ƙoƙarin komawa baccin.''
Farfesa Espie ya kuma ƙara da cewa ƙwayoyin halittu na taka muhimmin rawa, yawan gajiya, saurin ɗaga hankali ko kuma zama cikin taka-tsantsan, na iya bin dangi kuma ana ganin hakan cikin iyalai.
Akwai wasu hujjoji da ke nuna tsarin lokacin bacci da tashin mutune ya bambanta, kamar mai son tashi da sassafe ko mai kaiwa dare sosai bai yi bacci ba, abu ne da za a iya gado a cikin dangi, sai dai matsalar rashin bacci na da dalilai masu yawa.
Abin da za ka yi idan ka kasa bacci

Asalin hoton, Getty Images
Shin me ya kamata ka yi idan ka kasa komawa bacci bayan ka tashi da tsakar dare?
Farfesa Espie ya ce akwai sarƙaƙiya a batun ƙoƙarin yin bacci.
''A lokacin da safiya ke gabatowa, buƙatar mu ta yin bacci na raguwa, sannan kuma wataƙila za ka fara tunani sosai, tunanin '' na kasa komawa bacci'' hakan kuma zai zama ɗaya daga cikin abubuwan da za su hana ka bacci, saboda a iya fahimta, babu wanda zai iya sa kansa bacci, sai dai baccin ya zo. Kuma a lokacin da ka ke ƙoƙarin sa kanka bacci, za ka kasa yin baccin, kuma ina tunanin hakan na daga cikin matsalolin da ake da su.''
''A don haka mafita a nan shi ne ka yanke shawarar ƙin yin baccin. Ka ƙi sa kanka bacci ka bari ya zo da kansa'', inji shi.
''Kana murmushi da yawa a yayin da kake ƙoƙarin hana kanka murmushi, kana ina ne a lokacin da kake ƙoƙarin ƙin yi... Hakan na nuna mana wani abu mai muhimmanci sosai, cewa tunanin da ke ƙwaƙwalwarmu kan kawo cikas, kuma akwai buƙatar mu bi tsarin yin baccin da ya kamata domin ya zame mana jiki. Hakan ne zai sa ka zama wanda ya iya bacci, idan ka so.''
Akwai abubuwa marasa wahala da za mu iya yi da zai taimaka mana horas da kanmu yin bacci yadda a kamata a kullun, inji dakta Orchard.
Ya kamata mutum ya samu tsari guda ɗaya da zai dage a kai ''yin bacci a dai dai lokaci ɗaya a kullum, sai kuma tashi a lokaci ɗaya kullum''.
''Sai kuma yin bacci a wuri ɗaya a kodayaushe, wato sanar da ƙwaƙwalwar ta san inda muke bacci da kuma ƙoƙarin kauce wa bacci a kan kujera da kuma kauce wa yin aiki a kan gado'', inji ta.
Dakta Hare ta kuma ce idan ka farka daga bacci kuma ba ka ji alamun za ka iya komawa bacci nan take ba, ya kamata ka tashi ka yi wani abin daban na mintuna 30 ko fiye kafin ka sake komawa kan gadon, ''idan ka tashi bacci kuma ka gane ta tashi, to ka sauka daga kan gadon.''
Muna buƙatar shan magani?
Dakta Hare da Farfesa Espie duk ba su goyi bayan hakan ba, inda suka ce shawarwarin sauya tunani su ne ɗaya daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa wajen magance matsalolin rashin iya bacci.
''maganin da ya fi aiki bisa hujja na magance matsalar rashin bacci shi ne shawarwarin sauya tunani, kuma hakan ya taimaka wa kashi 70 zuwa 80 na mutane, kuma kashi 50 cikin su alamominsu baki ɗaya sun warke, inji dakta Hare.
Farfesa Espie ya ce wasu marasa lafiyar ba sa yarda cewa shawarwarin sauya tunani na aiki fiye da magani '' amma idan mukayi la'akari da wani dabara cikin shawarwarin sauya tunani da muke yi, muna ƙarfafa musu gwiwa su yi bacci na ƙanƙanin lokaci har sai baccin ya haɗu, kar su yi bacci da wuri, su kuma tashi da wuri.''
Wasu mutanen sun yadda sosai cewa shan sinadarin magnesium kafin lokacin bacci na taimakawa sosai wajen bacci da kyau. Sai dai Dakta Orchard ya ce babu bincike mai zurfi a kan hakan.
Sinadarin Melatonin fa? wanda ake iya samu a kananan shagunan maganin sha ka tafi a ƙasashe dayawa, yayin da wasu kuma sai likitoci sun rubuta musu?
Dakta Hare ta ce :'' hakan na da alaƙa da tambayar da aka yi kan Magnesium da kuma tasirin da ya yi wa wasu wanda ke nuna cewa bacci abu ne da ke da sarƙaƙiya.
Saboda haka akwai yiwuwar magungunan da mutane suke so suga sunyi musu aiki, za suyi aikin, ko da a zahiri ba sa aiki.''
Wasu abubuwan da suke shafar bacci

Asalin hoton, Getty Images
Ya ya batun kaiwa shekarun ɗaukewar jini, ko shaye-shaye, ko tsarin yin aiki na dare? ta ya ya su ke shafar bacci?
Dakta Hare ta ce shekarun ɗaukewar jini na kasancewa lokaci mai wahala ga mata kuma ya kan shafi baccinsu- tsawon lokacin da suke bacci, da tsawo lokacin da basa bacci da daddare da kuma rarrabuwar baccinsu, inji ta.
''Wani ɓangaren hakan na da alaƙa da ɗaukar zafin jiki lokaci guda wanda hakan ke katse bacci, saboda sauyin ƙwayoyin halittu, ko kuma canjin yanayi, wanda ke da alaƙa da shekarun ɗaukewar jinin, hakazalika yadda rayuwarsu ke cike da gajiya a shekarun, lokuta da dama suna fama da yara da iyaye- akwai ɗawainiya da yawa.''
Idan aka zo batun shaye-shaye kuwa, Dakta Orchard ya ce hakan na iya sauya yadda tsarin baccinmu yake, wato tsawon lokutan da muke bacci.
''Sai dai shan barasa kan shafi abubuwa da dama kuma, kamar misali buƙatar zuwa banɗaki, yana sa jiki ya sake, ya sa minshari, ya kuma shafi sinadaren halittunmu, waɗanda duk ɓangarori ne masu muhimmmanci a ƙoƙarin samun yin bacci da kuma yin cikakken bacci,'' inji ta.
Kan tambayar masu yin aikin dare da kuma yadda ya dace ka yi bacci in kana aiki da daddare, Dakta hare ta bayar da shawarar ƙoƙarin yin amfani da lokacin da baka aikin dare ka yi isashen bacci.''
Misali idan ba ka aiki da daddare kuma za ka iya bacci da daddare, ka yi ƙoƙarin amfani da wannan lokacin daidai gwargwado, sai kuma kishingiɗa idan ka samu lokaci, wannan ne lokacin da kawai muke ba da shawarar ɗan kishigiɗa a yi bacci.''
Kan batun yadda za a shawo kan matsalar katsewar bacci saboda yara sun tashi mutum da tsakar dare, dakta Orchard ya ce iyayen ƙananan yara na buƙatar lokacin kansu da kuma isashen lokacin bacci, wannan batu ne na samun yin bacci a duk lokacin da ka samu dama:
''Wasu lokutan dole ne ka ɗan yi baccin rana domin ka tabbatar ka samu isasshen baccin da zaka kula da kanka da kuma na yaronka. Ina ganin ya ɗan bambanta ga kowa''- kuma ka tuna wa kanka cewa wannan lokacin zai zo ya wuce!
Kan tambayar kallon fuskar wayoyinmu da zai iya hana mu bacci, Dakta Orchard ya ce:
''Abin da muke fahimta a hankali shi ne matsalar na zuwa ne daga abin da muke yi a kan wayoyin ba daga hasken da ke fitowa daga cikinsu ba.
A don haka idan muna amfani da wayoyinmu muna abinda zai sa mu natsu jikinmu ya sake, hakan ba zai yi tasiri sosai wajen hana mu bacci ba, ba kamar idan muna yin abin da zai ɗauke mana hankali ba.''











