Rishi Sunak ya zama sabon firaministan Birtaniya

Rishi Sunak ya zama sabon firaminista Birtaniya bayan da Sarki Charles ya ba shi izinin kafa gwamnati.

Hakan ya tabbata ne a ranar Talata bayan ganawarsa da Sarki Charles din a Fadar Buckingham.

Rishi Sunak wanda dan asalin asar Indiya ne ya zama shi ne firaministan Birtaniya na 57 a tarihin asar.

Kuma shi ne firaminista na uku da ya shiga Fadar Downing Street a wannan shekarar, sannan mafi kuruciya a cikin firaministocin da suka mulki kasar a shekara 20 da suka gabata.

Ganawar sabon firaministan Rishi Sunak da Sarki Charles ta tabbatar da miƙa mulki da wani ƙwarya-ƙwaryan biki na siyasa. Al’adace ta ci gaba da tabbatar da mulki a wani yanayi na gagarumin koma bayan siyasa da ke damun ƙasar.

Wannan lamari na ɗaya daga cikin manyan ayyukan Sarki a hukumance – kuma wani abu ne da marigayi mahaifiyarsa ta ɗauka da matuƙar muhimmanci, ta yadda duk da halin rashin lafiyar da take ciki sai da ta riƙe shi kan’in da na’in wajen tabbatar da Liz Trus a matsayin firaminista dab da rasuwarta.

Kalaman Sunak

Sunak ya ce a lokacin da yake Ministan Kudi ya yi bakin ƙoƙarinsa don kare mutane da kasuwanci ta hanyar gabatar da tsare-tsare masu yawa.

“Zan haɗa kan ƙasar nan ba ta zance ba kawai, ta yin aiki a zahiri,” in ji Sunak.

“Zan yi aiki dare da rana don yi muku hidima.”

Sunak ya ce gwamnatinsa za ta yi martaba da nuna ƙwarewa da aiki tuƙuru a kowane mataki.