Jirgin da Nasa ta aika duniyar wata ya komo duniyarmu ta Earth lafiya

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda jirgin da Nasa ta aika duniyar wata ya komo duniyarmu ta Earth lafiya

Hukumar sararin samaniyar ta Amurka NASA, ta dawo da kan rokar ta na farko da aka harba duniyar wata.

Kan rokar mai suna Orion capsule, ya fado kasa cikin Tekun Pacific, bayan ya yi wa duniyar wata shigar burtu, tare da dawowa doron kasa.

Daman dai wannan wani gwaji ne, kuma babu kowa a cikin rokar lokacin da ta fado, amma nan gaba idan za a sake harba wata lamarin zai sauya.

Nasa na gagarumin shirin zuwa duniyar watar da rokar Orion.

Watakila a yi wannan aiki a shekarar 2024 zuwa 2025 ko ma 2026, sannan za a yi yunkurin sanya dan adam cikin rokar da za a harba.

Shekaru 50 kenan cif da aka cimma irin nasarar, lokacin da aka harba kumbon Apollo mai lamba 17.

Hukumar NASA ta ce sabon shirin da akai wa lakabi da Artemis, wanda kalmar lissafi ce ta Girkawa, kuma Artemis kamar danjuma ne da danjummai tsakaninsa da Apollo.

"[A lokacin kumbon Apollo] mun yi abin da ake ganin ba mai yiwuwa ba ne," in ji jami'in Hukumar ta Nasa Bill Nelson.

Wasu labaran da za ku so

"A yanzu haka, muna sake yin wannan kokarin, amma da manufa ta daban, saboda wannan karo za mu sake komawa duniyar wata domin mu koyi rayuwa a can, da yin aiki, da kirkira, da kafa abubuwa a can, domin mu nuna za a iya rayuwa a can.

Abin da muke shirin yi, shi ne daukar bil'adama domin rayuwa a can, kuma za mu fara wannan shirin ne a kasrhen shekarar 2030, daga nan za mu fadada wannan damar'', a hirarsa da manema labarai.

Mike Sarafin, manajan shirin, wanda ya dde ya na yi wa manema labarai bayani kan shirin cikin makwanni uku da suka gabata, ya kasa boye farin ciki da zakwadin zuwan lokacin: "Abokaina, wannan shi ne yadda nasara ke samuwa."

apollo

Asalin hoton, NASA/JSC/ASU/@ANDYSAUNDERS_1

Nasa ta bayyana dawowar kan rokar Orion doron kasa da cewa "matakin farko" cikin abin da ake son cimma.