Yadda kumbon Artemis ya isa duniyar wata lami lafiya

Asalin hoton, NASA
Jirgin sama jannatin Nasa na Artemis ya isa duniyar wata lami lafiya. Jirgin sama jannatin ya yi tafiyar kilomita 130 a saman duniyar wata, a yanzu kuma zai fara zagayen duniyar.
Ba a ji ɗuriyar kumbon ba har na tsawon minti 34 a yayin da yake wannan tafiya, wacce ya fara ta da misalin ƙarfe 12.44 agogon GMT, daga can gefen wata.
A lokacin da siginal ɗin jirgin ya koma aiki, sai ya aiko da wani hoto zuwa nan duniyarmu ta Earth.
Nasa ta ce zuwa yanzu dai shirin "ya wuce yadda aka tsammace shi" tun bayan ƙaddamar da shi a makon da ya gabata.

Asalin hoton, NASA
Daraktan da ke kula da jiragen sama jannati a Nasa Zebulon Scoville ya ce: "Wannan rana na ɗaya daga cikin waɗanda kuka daɗe kuna tunaninsu da fatan zuwansu.
"Da safiyar wannan rana mun ga duniyar wata na faɗuwa ta bayan wata a yayin da muka aika da kumbon da zai kai bil adama zagayen watan, a shirye-shiryenmu na ganin ɗan adam ya sake tafiya duniyar wata a cikin ƴan shekaru masu zuwa.
Wannan lamari ne a zai kawo matuƙar sauyi.
Jirgin sama jannatin ya wuce ta dab da wajen da kumbon Apollo na 11 da 12 ea 14 suka taɓa sauka.
A ranar Larabar da ta gabata ne aka ƙaddamar da kumbon Artemis sararin samaniya daga Cibiyar Kennedy a Florida, inda aka harba jirgin sama jannati mafi ƙrfi da Nasa ta taɓa ƙerawa.
An sanya ƙululun da ke jikin kumbon mai suna Orion a daidai saitin da wata yake. Tuni jirgin ya aiko da hotunan da ya ɗauka da kansa a yayin tafiyar.

Asalin hoton, NASA
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yake wannan jrigin an harba shi don gwaji, babu ɗan sama jannati ko ɗaya a cikinsa - a maimakon haka, sai a saka manyan ƴar tsanar tallan kaya har uku, aka lulluɓe su da na'urorin sarrafa su.
"Waɗannan na'urorin suke gano ko yanayin wajen zai iya zama marra cutarwa ga mutane," in ji jami'in Nasa, Zena Cardman.
"Don haka akwai abubuwa kamar na'urori masu gano tururi, da na'urori masu gano motsi da masu gano yanayi - abubuwa dai da ɗan adam zai damu da sanin yadda suke tafiya."
Kuma hakan na da muhimmanci saboda idan jirgin ya tafi lafiya lau to ƴan sama jannati za su iya bin sa a karo na gaba, da farko za su fara zuwa zagaye a sararin duniyar wata, kafin kumbon Artemis ya ɗauki mace ta farko da jinsin da ba Turawa ba na farko zuwa dandaryar duniyar watan.
Hukumar Sararin Samaniya ta Turai ESA, ma tana sa ido a nutse kan jirgin sama jannatin. Ita ta ƙera wani sashe na tolouwar nan ta Orion, wacce ke samar da wuta ga jirgin.
Esa ma tana da fasinja a cikin jirgin: wata butum-butumin tunkiya da ake nunawa a shirin yara na katun mai suna Shaun the Sheep.

Asalin hoton, NASA
Bayan zuwa kurkusa da wata da jirgin ya yi, a yanzu Orion zai ƙara yin gaba sosai don sake matsawa daf da watan.
A ranar 26 ga watan Nuwamba ne, ake sa ran jirgin zai isa fiye da inda kumbo Apollo na 13 ya taɓa zuwa wato nisan kilomita 400,171 daga duniya.
Kwana biyu bayan nan, da zai iya tafiyar kilomita 430,000 daga duniyarmu - tafiya mafi nisa da wani jirgin sama jannati ya taɓa yi.
Bayan wannan, sai jirgin ya karkato ya kamo hanyar gida ta hanyar Wata sannan zuwa Earth inda aka shirya zai sauka a Tekun Fasifik ranar 11 ga Disamba.










