Me ya sa harba kumbo zuwa duniyar wata da Nasa ke son yi ke ba ta wahala?

Picture of nose cone of Artemis-i SLS rocket and Orion capsule on launch gantry with moon above

Asalin hoton, Getty Images

Nasa ta samu nasarar ƙddamar da jirgin sama jannati mafi ƙarfi da ba a taɓa yi ba a wani shirinta na ganin ɗan adam ya sake komawa duniyar wata.

An harba jirgin sama jannatin mai suna SLS ne daga tashar da ke Florida da misalin karfe 6.47 agogon GMT - a wani lamari mai cike da tarohi ga Nasa, a yayin da shirin na - Artemis-1 - ya zama irinsa na farko na son komawa duniyar wata a cikin shekara 50.

Amma Nasa ta yi ta samun tsaiko wajen harba rokar saboda matsalolin na'ura da aka dinga samu da kuma rashin kyawun yanayi.

Mene ne shirin Artemis?

Shirin Artemis shi ne na farko na ƙoƙarin ganin an sake zuwa duniyar wata tun bayan shirin Kumbo Apollo shekara 50 da suka wuce.

Artemis-I shiri ne na gwada harba kumbon SLS da ba ya ɗauke da mutane mai wani ƙululu ta samansa.

Za a sanya manyan ƴar tsana irin ta tallar kaya har uku a cikin kumbon wanda zai shafe kwana 25 yana tafiya, ta yadda ƙululun da ke jikin kumbon mai suna Orion zai zagaya wata kafin daga bisani ya faɗo Tekun Fasifik.

An shirya tafiyar ne don gwada irin wahalar da kumbon zai sha da kuma gane yadda turirin da ke sararin samaniya zai iya shafar ɗan adam.

Shirin Artemis-II, wanda aka tsara yin sa a shekarar 2024, zai ɗauki tsawon mako shida inda ƴan sama jannati za su yi zagaye a gefen duniyar wata sannan su dawo duniyarmu ta Earth.

Tawagar za ta kasance ta mutum hudu ce da suka hada da mace ɗaya da kuma wanda ba Bature ba ɗaya, in ji Nasa.

Shi kuwa shirin Artemis-III, da aka tsara yin sa a shekarar 2025, shiri ne da ƴan sama jannati da suka haɗa da mace ɗaya, za su sauka a kan duniyar wata don kafa wata tasha da za ta daɗe - gabanin shirin tafiyar mutum zuwa duniyar Mars.

Sai dai, saboda lokacin da aka ɗauka don ƙaddamar da kumbon SLS a bana, ga alama shirin Artemis-III zai wuce 2025 kafin aiwatar da shi.

Me ya sa Nasa ke samun matsala wajen ƙaddamar da kumbon Artemis?

Kumbon SLS da ake amfani da shi a shirin Artemis shi ne mafi girma kuma mafi ƙarfi da Nasa ta taɓa amfani da shi.

Kamfanin Boeing ne ya ƙera shi, yana da tsayin mita 98 kuma injinsa kan shanye man haidurojin da oksijin har lita miliyan 2.8 a cikin minti takwas kacal.

Dole aka yi haƙuri a karon farko na ƙoƙarin ƙaddamar da SLS a ranar 29 ga watan Agusta, saboda zargin tsiyayar mai da kuma lalacewar na'urar auna yanayi.

Lokaci na biyu kuma da aka so sake harba shi ranar 3 ga Satumba, shi ma haka aka haƙura saboda tsiyayar man.

Base of rocket

Asalin hoton, NASA

Dr Lucinda King, shugaban shirye-shiryen zuwa sararin samaniya a Jami'ar Portsmouth da ke Birtaniya ya ce: "Wannan kumbon cike yake da sarƙaƙiya fiye da na Saturn V wanda Nasa ke amfani da shi a baya wajen zuwa duniyar wata.

"Yana amfani da mayuka daban-daban kuma yana da ƙrfi, saboda ba don zuwa Wata kawai aka ƙera shi ba, har Mars zai iya zuwa."

An sake ɗaga harba shi da aka yi niyya ranar 27 ga Satumba, saboda alamun da ya nuna na cewa mahaukaciyar guguwa na iya lalata shi.

A wannan karon ma an jinkirta harba shi har tsawon kwana biyu saboda ƙaƙƙarfar iska da ruwan sama.

Me ya sa shirin Artemis ka da muhimmanci?

Nasa ta ɗauki tsawon shekara 10 tana tsara Shirin Artemis.

Shi ne karo na farko da Nasa ta so aika kumbo duniyar Wata tun bayan na Kumbo Apollo.

Daga tsakanin shekarar 1969 zuwa 1972, kumbunan shirin Apollo shida ne suka sauka a duniyar Wata da jumullar mutum 12 a cikinsu.

Astronaut Dave Scott in Moon buggy on the moon's surface

Asalin hoton, NASA

Tun daga wancan lokacin Nasa ta mayar da hankali kan shirin sararin samaniya da zagaya duniyar Earth kawai, inda take gudanar da al'amuranta daga tashar ƙasa da ƙsa da ke sararin samaniya.

Babban dalilin da ya sa Nasa ke son komawa duniyar Wata shi ne don ta gwada yadda rayuwa ka iya kasancewa idan za a rayu a duniyar Mars, a cewar Farfesa Sa'id Mosteshar, darakta a Cibiyar Tsari da Dokokin zuwa sararin samaniya da Landan da ke Jami'ar London.

"Wata shi ne ya fi kusa da duniyar Mars," a cewarsa. "Kana iya gwada abubuwa a wani wajen da za su bai wa ƴan sama jannati damar gane yadda rayuwa za ta kasance a Mars."