Mace ko namiji: Me ya sa ake taƙaddama kan jinsin matar shugaban Faransa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Anoushka Mutanda-Dougherty
- Marubuci, Melanie Stewart-Smith
- Marubuci, Victoria Farncombe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Fame Under Fire podcast
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da matarsa Brigitte na shirin gabatar da hotuna da gwaji na kimiyya a wata kotu da ke Amurka a matsayin shaida kan cewa matar ta Macron mace ce.
Lauyan mutanen biyu ya ce shugaban na Faransa da matarsa za su gabatar da shaidar ce gaban alƙali a wata ƙara da suka shigar bisa zargin cin fuska, inda suka maka wata sananniyar ba'amurkiya mai ra'ayin riƙau Candace Owen, wadda ta riƙa yada cewa asali an haifi Brigitte ne a matsayin namiji.
Tuni lauyoyin Ms Owen suka buƙaci kotu ta yi watsi da ƙarar.
Lokacin da ya tattauna da wani shirin BBC, lauyan shugaban Macron, Tom Clare ya ce ikirarin da Candace ta yi ya yi "matuƙar tayar mata da hankali", kuma wani yunƙuri ne na kawar da hankalin shugaba Macron daga muhimman ayyuka.
"Kamar duk wani mutum wanda ke ƙoƙarin gudanar da aikinsa da kuma kula da rayuwarsa, idan wani ya ci zarafin iyalinka, ba za ka ji daɗi ba. Ba zai ƙi jin haka ba kawai saboda shi ne shugaban ƙasa," in ji lauyan.
Mista Clare ya ce akwai "ƙwararre da zai bayar da shaida" kuma duk da cewa ba zai bayar da bayanin dalla-dalla ba a yanzu, amma iyalin a shirye suke su gabatar da shaidun da za su tabbatar cewa zargin da ake yi ba gaskiya ba ne.
"Abin tashin hanakali ne a ce dole sai ka je kana ƙoƙarin gabatar da shaidu," in ji shi.
"Amma haka nan za ta je a gaban al'umma ta bayar da shaida. Ta ci alwashin yin duk abin da ya dace wajen ganin an tabbatar da gaskiya."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da aka tambaye shi kan ko Macron da matarsa za su gabatar wa kotu hotunan Brigitte a lokacin da take da juna-biyu da kuma lokacin da take renon yaranta, Mista Clare ya ce akwai hotunan kuma za a gabatar da su.
Candace Owen, wadda tsohuwar mai sharhi ce a gidan jaridar Daily Wire ta Amurka, tana da miliyoyin mabiya a shafukan sada zumunta, kuma ta sha yaɗa ikirarinta na cewa Brigitte Macron namiji ne.
A watan Maris ɗin 2024 ta ce babu wani abu da zai hana ta janye ikirarinta na cewa Matar Macron ɗin namiji ne.
Irin waɗannan zarge-zarge sun fara yaɗuwa ne tun wajen shekarar 2021 a wasu shafukan intanet, inda aka fi nuna yatsa kan bidiyon da wasu masu shafukan intanet a Faransa Amandine Roy da Natacha Rey suka wallafa a YouTube.
Macron da matarsa sun yi nasara a wata ƙarar da suka shigar bisa zargin ɓata kan Roy da Rey a shekarar 2024, sai dai wata kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncin a shekarar 2025 bisa dogaro da ƴancin faɗin albarkacin baki, ba wai domin sahihancin batun ba. Daga nan sai Macron da matar tasa suka ɗaukaka ƙara.
A watan Yuli Macron da matarsa suka maka Candace Owen ƙara a wata kotu da ke Amurka. Ƙarar ta zargi Ms Owen da yin watsi da duk wasu "ƙwararan shaidu da suka ci karo da ikirarinta, kawai domin ci gaba da yaɗa shaci-faɗi da ikirarin masu neman ɓata suna".
A Amurka, duk wata ƙara ta zargin ɓata sunan sanannun mutane, ana buƙatar mai shigar da ƙara ta tabbatar da "mummunan nufin da ake da shi" - tare da cewa wanda ake zargi ya ci gaba da yaɗa bayanan ƙarya duk da bayyanar gaskiya ƙarara.

Asalin hoton, Candace Owens
A watan Agusta, Emmanuel Macron ya yi wa wata mujallar ƙasar Faransa, Paris Match, bayani kan dalilan da suka sa suka ɗauki matakin zuwa kotu.
"Wannan mataki ne na kare mutuncina! Domin wannan zancen wofi ne. Mutum ce wadda tana da masaniya cewa bayanan ƙarya ne amma ta ci gaba da yaɗawa domin cutarwa."
Lauyoyin Ms Owen sun mayar da martani ta hanyar buƙatar kotu ta yi watsi da ƙarar iyalin Macron, inda suka ce tu farko bai kamata a shigar da ƙarar a Delaware ba, domin a cewarta batun bai shafi sana'arta ba, wadda take da rajista a jihar.
Sun yi ikirarin cewa tilasta mata kare kanta a kotu a Delaware zai yi "illa gare ta ta fannin kudi da tafiyar da lamurra".
BBC ta nemi jin ta-bakin lauyoyin Candace Owen. Tuntuni, ta bayyana cewa ta san abin da take faɗa gaskiya ne kuma a Amurka akwai ƴancin faɗar albarkacin baki kuma mutum na da damar yin suka.











