Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan wasan PSG sun kai ƙarar Mbappe, Man Utd ta yi yarjejeniya da Hojlund
Ƴan wasan PSG shida ciki har da guda biyu da suka saya a bazara sun yi korafi ga shugaban kungiyar a kan kalaman da Kylian Mbappe, ya yi. (Sky Sports)
Manchester United ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Rasmus Hojlund kuma a shirye dan wasan na Denmark yake ya nemi kungiyarsa, Atalanta ta Italiya da ke son fam miliyan 60 a kansa, ta ba shi dama ya tafi idan har ba ta cimma matsaya da United ba a cinikin matashin mai shekara 20 (Football Transfers)
Ana sa ran Bayern Munich ta kara tayin da ta yi wa Harry Kane ya kai fam miliyan 70, to amma da wuya hakan ya gamsar da Tottenham, duk da cewa saura shekara daya a kwantiragin kyaftin din na Ingila a kungiyar. (Mail on Sunday)
Chelsea na son fam miliyan 40 a kan Romelu Lukaku, wanda Al-Hilal da Juventus, ke son, kuma daman ta yi watsi da tayin da Inter Milan ta yi masa. (Guardian)
Tottenham na sa ido a kan dan wasan Chelsea na Sifaniya, Marc Cucurella, wanda ke iya wasa a baya da kuma gaba, a kokarin da kungiyar ta Landan ke yi na neman wanda zai maye gurbin dan gabanta na gefe Ivan Perisic, dan Croatia. (Football Transfers)
Haka kuma Tottenham din da Napoli na son sayen dan bayan Borussia Monchengladbach da Japan Ko Itakura, mai shekara 26. (Sky Sports, da Get German Football News)
Chelsea ta fara tattaunawa da Arsenal a kan cinikin Folarin Balogun, Ba'amurke asalin Najeriya mai shekara 22. (Mail Sunday)
Dan wasan gaba na gefe na Ivory Coast, Wilfried Zaha, wanda kwantiraginsa da Crystal Palace, ya kare, na nazari a kan sabuwar yarjejeniyar da kungiyar ta gabatar masa, yayin da kuma ya tattauna da PSG da Napoli da Galatasaray. (Guardian)
Ƙungiyar FC Twente ta Holland na dubu yuwuwar karbar aron matashin dan wasan gaba na Manchester United da Uruguay Facundo Pellistri, mai shekara 21. (Voetbal International)
Bayern Munich za ta sayi dan bayan Napoli, Kim Min-jae, dan Koriya ta Kudu mai farashin yuro miliyan 50 a kansa, tsawon shekara biyar. (Sky Sports)
Inter Milan ta gaya wa Bayern Munich cewa tana son sayen golanta Yann Sommer, dan Switzerland mai shekara 34. (Sky Sports)
Burnley ta cimma yarjejeniyar dauko aron matashin dan bayan Borussia Dortmund Soumaila Coulibaly, mai shekara 19, da kuma zabin sayensa a kan yuro miliyan 15. (L'Equipe)
Fulham za ta yarda da wata sabuwar yarjejeniya da Willian, bayan da dan Brazil din mai shekara 34 ya ki yarda da tayin da suka yi masa na farko a makon da ya gabata. (Football Insider)